← Book details Shin So Daya Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 26

Sashe 8

Shin So Daya Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

     **
Awannan daren mun gurji amarcinmu,Mahmood ya fanshi kudin sadakinsa ba kadan ba,ni kuwa nasha kuka har na baiwa uku lada,lallashi da sanya albarqa kuwa har Mahmood ya gaji da yinsu,sae cewa yake "Matata ubangiji Allah yayi miki albarqa,nagode kwarai da gaske da kika tsare min mutuncin kanki har kika kawoshi gidana.....*'Zahmood'* ina sonki matuk'a fiye da tsammaninki,Allah ya k'ara mana qaunar junanmu,Sannan kuma Allah ya azurtamu da 'ya'ya nagari....."

    Cike da farin ciki na amsa da "Ameen ngd my *'Jannah'*.

    Da safiyar ranar kuwa,sae ga Usee da kayan breakfast wai Momi ce tace akawo mana.Sosae abin ya bamu mamaki matuk'a tare da jinjina al'amarin,Mahmood ya k'arbi basket din yace"Usee kace mata muna godiya sosae sae mun shigo.... "

   Da sauri Usee yace"A'ah tama ce suna nan tafe gobe duka dasu anty Meema.... "

Gabana naji ya yanke ya fadi jin abinda ya fada,amma sae na kada baki nace"Allah ya kaimu kanin miji,sae mun gansu..... "

   Murmushi ya sakar min yace"Toh!  matar Yayah,sae anjimanku.... "

Muka had'a baki wajen cewa"Toh mu jima da yawa.... " ya fice.

    Wani uban tsalle naga Mahmood ya daka yana fadin"Yessss! My family have accepted my Zahra da hannu bibbiyu........ Sauran mana kaninmu.... "

Murmushi kawai nayi abina.Daga haka muka soma cin breakfast wanda ferfesun kan rago ce,sae kuma kayan tea.

    Washeqari kuwa sun cika alqawari,sunzo din hadda 'yan gidan Baba Mu'azzam su Hafeezah da mominsu.Gida ya cika ya kacame da hayaniya,sae fira muke cikin raha da annashuwa.Dama tun safe nida Mahmood muka hada musu lafiyayyar girki kan suzo.

Nace"Anty Meema waini ina Anty Hanan ne? " (Dayake mijina ya fada min cewar yanxu ta koma gidansu Momi da zama tunda mijinta ya tafi,shine nayi tunanin kila tare zasu zo amma kuma sae naga akasin hakan,babu ita aciki).

   Momi ce ta kada baki tace"Hanan tana gida kinsan ciki yayi nauyi yanxu,don haka mah bata cika fita,amma tace tana gaidaki.... "

   (Gaskiyar lamari kuwa shine,babu yadda Momi batayi da Hanan ba akan tazo suje amma taki,tace babu inda zata,akan dole Momi ta rabu da ita,Jasmin mah ta hanata binsu,ita kuwa yarinyar sae kuka taketa yi amma babu damar zuwa tunda uwarta ta hana).

Nace"Allah sarki! Allah de ya raba lafiya... "

   Ni nasan tabbas Momi tade k'are Hanan ne,amma ni xuciyata ta bani cewar haushina takeji sosae don na auri wan mijinta.Oho! Wallahi kome ze faru ya dade be faru ba donni dai yanxu harga Allah ina son mijina kuma bana danasanin aurensa,kuma babu wanda ya isa ya raba wannan auran sae Allah wanda shine ya hada abinsa.Su Momi da Khairat seda suka sake nemar gafarata akan cin mutuncin da suka min da kuma sharrin asirin da suka lik'a min.Nace"Laah! wallahi babu komai,ni wlhy ban rik'eku axuciya ba,Allah ya yafe mana duka... "

Awa daya kacal su Momi sukayi,Sannan suka wuce,su Hafeezah kuwa sae da marece direban gidansu yazo ya daukesu wanda dama can shi dinne ya kawosu.'yan kudade na basu wanda Mahmood ne ya bani akan cewar idan sun tashi tafiya saina basu.

   Nace"Afreen gashi ba yawa kwa siyi kayan kwalliya,naso baku acikin nawa ne amma kayan lefena nacan Zaria..... "

   "Laaaaah! kuji anty sae kace wasu baki?mufa kannenki ne basai kin bamu wani abin ba,sada xumunci mukazo yi ba maula ba.... "

Ah wasance nakai mata bugu ta goce,nace"kai Afreen yanxu yaya bazata iya baiwa kannenta kyauta ba? Shikenan idan ta basu ya zama maula ce suka yi? "

      "Mude kome zaki fada bazamu k'arba ba,ki rik'e abarki bama so.... " tayi gaba su Rafi'ah suka take mata baya,har wajen Mota na bisu amma sam sunki k'arba,Afreen ce ta umarci direba daya tada motar,ya kuwa bi umarninta suka fice.Su Anty Meema mah haka suka min dana ce gashi sa baiwa 'ya'yana susha alawa,suka k'i k'arba.

Asanyaye na koma ciki,gab da sallar magrib ogan nawa ya dawo.Ware min hannaye yayi wai nazo na rungumeshi,babu b'ata lokaci na isa gareshi ina dan bubbuga kafata akasa nace"Anki ah rungumekan,daga cewa zakaje kayiwa abokanka ban gajiya shine kayi zamarka acan ko? Kode sunyi maka wata matarce ban sani ba? "

  "Lalalalaaaah! Sunma isa?kuma nima na isa na so wata bayan my Zahmood?wallahi babu ta biyunki acikin xuciyata my Zahra,ke kadai kin isheni rayuwa...... "

"K'arya kake har yanxu kana son Zaynab,kuma itama din ai hakan ka fada mata,kace babu wata da zaka rab'a ko bayan ranta,sae gashi ayau ka k'arya alqawari...... " babu xato ba tsammani kawai naji hawaye ya soma ziraro min saman kunci,hawayen da ban san ko na menene ba? Kota kishin Zaynab dinne ko kuwa tausayin kaina na ganin na kamu da sonsa bayan nasan har yanxu yana qaunar Zeeynsa,kuma ko kusa nasan bazan taba samin irin matsayinta axuciyarsa ba,yafi sonta akaina nesa ba kusa ba.

   Shima din idan yace ya manta Zeeynsa toh kuwa yayi k'arya,yasan yana mugun son Fadima,amma Zeeynsa ta dabance acikin xuciyarsa,yasan tabbas watarana Fadimar tana iya maye gurbin Zaynab din acikin xuciyarsa idan har ta iya bi dashi yadda ya kamata amatsayinta na wayayyiya.

Rungumota yayi ya soma lallashinta,cike da kissarsa da kuma salonsa ya mantar da ita batun Zeey.Atake anan suka shiga farantawa juna rai,suna meh jin sabuwar qaunar junansu na ratsa dukkan wani gab'ar jikinsu.Ya tambayeta yadda sukayi da bak'in nata,anan ta bashi labarin yadda sukai dasu Afreen,sosae yayi dariya hadda k'yak'yatawa.

    Yace"Ai nasan halin Afreen sarai bata son ana mata irin wannan k'yautar,sae tayi ta ganin kamar malauce tazo yi,yanxu mah idan ba sa'a kikaci ba,toh kuwa tana iya jera miki kwanaki kafin ki sake ganinta agidan nan.... "

Waro idanuwa waje nayi nace"Akan nayi mata k'yautar kudin?"

   "Naki wasane yarinyata,toh bari kiji akwai wani saurayinta Arham dake masifar sonta,toh wlh ko kwandala ya bata,toh shikenan daga ranar ta dena kulasa kenan har sae iyaye sun shiga cikin maganar,yanxu maganar da nake miki,babu wata k'yautar kudi da take k'arba daga gareshi,ita fa ta gwammace ayi mata k'yautar wani abin can daban amma bawai kudi ba,aurenta mah nan da wata uku masu xuwa insha Allah.... "

   Ahankali nace"Allah ya nuna mana.... Agaskiya nide ta birgeni,sam abin duniya basu rufe mata idanuwa ba kamar wasu matan..... "

     "Ai Aysha Afreen tayi ne,wallahi da'ace ni meh sha'awar auren dangi ne,toh kuwa wallahi da ita xan aura sabida halinta yayi ne... " ya fada tare da kashe min one eyes.

Wani irin kishinta ne naji ya tokare min qahon xuciya,lokaci daya na sakar masa kukan shagwab'a,nace"Nasan kila auran mah dakai za'ayi,b'oye min kawai kake kamar yadda ka b'oye min aurena dakai...... "

    Rik'e cikinsa yayi yana dariya yace"Babyna ji yadda kika koma lokaci guda,don't tell me kema kina da kishi sosae juz lyk Zee...... "

B'ata fuskar da yaga nayi ne ya sakashi yin shiru,ya sosa k'eya tare da fadin"Am sorry my Zahmood bazan k'ara k'iran sunanta agabanki ba.... " sae kuma naji duk ya bani tausayi.Haka muka cigaba da wasanninmu na ma'aurata kafin daga bisani muka mik'e don gabatar da sallar magrib,bayan ya dawo daga masallaci kuma muka zauna cin abinci.

      ****
Kwanakin amarcin daya biyo baya kuwa ba'a magana don sosae nake samun kulawa da kuma daddadar soyayyar mijina agareni,nima ba laifi ina gwada masa tawa kulawar da soyayyar akoda yaushe.'Ya mace kenan,ko kuma nace xuciya ita de babu ruwanta,da zarar ta sami Wanda yake bata kulawa da kuma damuwa akanta,shike nan saita mace akan son wannan din,gashi ayau son da nake yiwa Mubarak ya zama tsuntsu ya koma kan Mahmood.Ayanxu Kam ina masifar son Mijina Wanda har nake jin bazan iya cigaba da rayuwa babu shi ba,tofa kullum muna mak'ale da juna baya fita,koda ace ya fitan ne,toh kuwa baya jimawa yake dawowa,dalilin daya sanya muka k'ara shaquwa dashi kenan.

      Hakan yake gasu Suhaileedar,sun wani k'ara shaquwa da wani irin mugun son junansu daya qaru,sosae leedar ke tattalin Suhaima kamar wata sarauniya,haka mah iyayensa da kannensa ke masifar ji da ita.Rayuwa tayi mata fari kal,ga soyayyar miji ga kuma na family dinsa,agaskia Suhaima ko kadan bata da damuwa.

     Ana gobe zamu koma Zaria,Mahmood ya kaini gidajen 'yan'uwansa,gidan goggo Ladidi muka soma zuwa,sae gidan Anty Meema,Anty Labeeba,anty Khairat,duk kuma sun rasa inda zasu sakani don murnar ganina,kuma bamu tashiwa sae mun dire musu abubuwan alheri.Akan hanya Mahmood ya tsaya daidai wani saloon.

    Yace"Zahmood oya fito muje awanke miki kai,idan yaso Afreen ta miki kitso don ta iya sosae.... "

Banyi wata gaddama ba na fito don ni Kaina Ina buqatar awanke min kan don jinsa nake kamar yana wari mah sabida ruwan da yake sha kullum😁(Kun gane Ai).

    Mun cimma mutane ba laifi acikin saloon din,Mahmood ya narka musu uban kudi don kawai asamu ayi min da sauri,su kuwa sae washe haqora suke don ganin sun yaqi naira da safiyar nan,nan da nan suka wanke min kan sannan aka shigar dani dryer,retouching kawai nayi.Ana gama min ban wani b'ata lokaci ba na fito na sameshi zaune awaje yana jirana.Murmushi ya sakar min tare da mik'ewa daga inda yake,ya tako ya sameni ah inda nake tsaye.

   Yace"Zahmood har an gama? "

"Yo! ba dole agama ba tunda ka narka musu uban kudi kamar baka san zafin nemansu ba? retouching kawai da zanyi shine ka tashi ka zabga musu uban kudi..... "

    "Can do more than that for you my Zahmood,wallahi kinfi karfin komai awurina,kudi kuwa yanxun mah na fara bararwa indai akanki ne... "

Sosae kalamansa sukai min dadi,ya kamo hannuna yana fadin"Zahmood tunanin meh kike haka?taho mu tafi.... "

      Na soma k'ok'arin kwatar hannuna"Haba my dear meye haka? Sakar min hannu kaga fa mutane na kallonmu..... "

"Yo! toni ina ruwana da mutanen? Inace ko halali ta na rik'e? Idan kuma basu yadda ba toh suzo su duba foreheads dinmu zasu ga an rubuta *'MAHMOOD WEDS FADIMA'*"

   Sosae abin yaban dariya,har muka iso gidan Baba Mu'azzam fira muke tayi da kuma wasanni.Acan suma rasa inda zasu sakani sukai don murna,ji suke tamkar su hadiyeni don so,mahmood ya tafi yace anjima zai dawo ya daukeni.

     Afreen ta yaryara min kananun kitso meh k'yau,tace"Anty Zahra jan lallinki mah harta soma gogewa bari na aiki Rafi'ah ta dauko mana meh lalli anan bayan layinmu.... "

Nace"Afreen wlh dama kin basshi kada ya dawo ya zauna zaman jirana don kinsan lalli bata saurin bushewa... "
Chapter 8 · 0% Book details