Sashe 24
Shin So Daya Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mun cimma mutane ba laifi acikin saloon din,Mahmood ya narka musu uban kudi don kawai asamu ayi min da sauri,su kuwa sae washe haqora suke don ganin sun yaqi naira da safiyar nan,nan da nan suka wanke min kan sannan aka shigar dani dryer,retouching kawai nayi.Ana gama min ban wani b'ata lokaci ba na fito na sameshi zaune awaje yana jirana.Murmushi ya sakar min tare da mik'ewa daga inda yake,ya tako ya sameni ah inda nake tsaye.
Yace"Zahmood har an gama? "
"Yo! ba dole agama ba tunda ka narka musu uban kudi kamar baka san zafin nemansu ba? retouching kawai da zanyi shine ka tashi ka zabga musu uban kudi..... "
"Can do more than that for you my Zahmood,wallahi kinfi karfin komai awurina,kudi kuwa yanxun mah na fara bararwa indai akanki ne... "
Sosae kalamansa sukai min dadi,ya kamo hannuna yana fadin"Zahmood tunanin meh kike haka?taho mu tafi.... "
Na soma k'ok'arin kwatar hannuna"Haba my dear meye haka? Sakar min hannu kaga fa mutane na kallonmu..... "
"Yo! toni ina ruwana da mutanen? Inace ko halali ta na rik'e? Idan kuma basu yadda ba toh suzo su duba foreheads dinmu zasu ga an rubuta *'MAHMOOD WEDS FADIMA'*"
Sosae abin yaban dariya,har muka iso gidan Baba Mu'azzam fira muke tayi da kuma wasanni.Acan suma rasa inda zasu sakani sukai don murna,ji suke tamkar su hadiyeni don so,mahmood ya tafi yace anjima zai dawo ya daukeni.
Afreen ta yaryara min kananun kitso meh k'yau,tace"Anty Zahra jan lallinki mah harta soma gogewa bari na aiki Rafi'ah ta dauko mana meh lalli anan bayan layinmu.... "
Nace"Afreen wlh dama kin basshi kada ya dawo ya zauna zaman jirana don kinsan lalli bata saurin bushewa... "
"A'ah wallahi anty sae fa an miki don yayana ya gani ya kusan zaucewa,in banda abinki mah ai lalli itama adoce ga 'ya mace,nifa wlh mijin da xan aura idan har baya son lalli da k'amshi tofa bazan aureshi ba.... "
Da mamaki nace"Akan lallin?"
"Anty naki wasane wlh....... "
Ta kwalawa Rafi'ah k'ira tazo,ta aiketa gidan meh lallin,ba'a wani jima ba sae gashi sun dawo da meh lallin,zuwansu yayi daidai da gama kitsonmu.Aka zana min jan lalli meh k'yau,abinka da farar mace sae ya zauna das ajikina,abinci mah abaki Afreen tayi ta bani.Bayan an gama ta biya kudin lallin,inata cewa ta basshi zan biya amma taki.Kai agaskia nide ranar naga gata awurin wa'ennan bayin Allahn.Sae bayan sallar hudu Mahmood ya dawo daukata,yana ganina ya soma cewa"wowww! Afreen wlh nasan aikinki ne wannan,ngd sosae kin fitar min da amarya,yanxu ni wacce irin k'yautace zan maki daze nuna lallai naji dadin wannan gyaran.....?"
"Yanzu brother shikenan donna gyara anty Zahra shine sae an bani wata k'yauta?nasan da'ace Khairat ce ko Labeeba bazaka yi musu wannan maganar ba,don Allah ka bari bannaso,idan kana hakan sae nayi ta ganin kamar baka daukemu daya ba kamar yadda mu muka daukeku.... "
Ahankali yace"okay am sorry kanwas bazan kuma ba.... "
Sun cikani da sha tara ta arziki,sukace insha Allah suna nan xuwa Zaria ganin gida,Kaka rigima sae tsiya take ta min waina kuke sae gyaran jiki nake,adole wai ina son na fita matsayi agun megidan namu,dariya ni take taban ba.Maminsu Afreen ita tata k'yautar ta tsimi ce,tace kada na kuskura nayi wasa da amfani da ita don mace sae da gyara.Akunyace na k'arba ina mata godia.
Amota kuwa Mahmood kamar ze hadiyeni don sha'awar lallina,yana tuki amma rabin hankalinsa na kaina ne,ya jawoni yana meh cusa kansa ajikina yana shak'ar kamshin jikina,hadda lallin kafata dana hannayena ya hau shafawa,ah rud'e nace"Haba dearnah tuki fa kake,pls concentrate on it.... "
"Ai ke dince Zahra kike nemar zautani da wannan adon taki,agaskia yau sai kwalliya ta biya kudin sabulu.... " ya kashe min ido daya,ni kuwa na gane nufinsa don haka sae nayi rau-rau da idanu kamar xan saki kuka,ganin hakan ya sakashi sakin dariya yace"Wallahi ayau babu zancen daga kafa,na fayi haquri kwana kusan uku kenan na zuba miki idanuwa ina kallonki amma yau babu daga kafa...... "
Tuni na sakar masa kukan shagwab'a,ya shiga lallashina har muka karaso Family house.Bansan meyasa nake jin faduwar gaba ba idan har akan komai daya shafi su hajiyar Mahmood ne,lfy lau muka baro gidan Baba Mu'azzam,banji wani faduwar gaba ba sanda mukaje amma gidansu Momi saina tsinci kaina da jin tsananin faduwar gaba.Kila kuma don wannan zuwan shine karona na biyu shiyasa.
Mahmood ya lura da yadda yanayina ya sauya,yace"Zahmood pls cool down,Momi has totally changed wlh believe me babu abinda Zata miki kinji matar Mahmood? " kai kawai na daga masa.
Ah main falon gidan muka tarar da Hanan da Usee suna hira.Muna hada idanuwa da ita sae naji gabana ya tsananta bugawa,ji nayi kamar Mubarak dinne nayi ido hudu dashi.
"Oyoyo matar Yaya.... " Usee ya fada tare da mik'ewa,awasance Mahmood yace"Dakata malam ince dai ba shirin rungumar min mata kake ba? "
Dariya muka sakar,kafin Usee yayi magana na karba"Toh idan mah yayi haramun ne?shima din mijina ne fa... "
"Yauwa gaya masa matar Yaya.... "
Tuni muka ga Mahmood ya hade rai sosae kamar be taba dariya ba wanda hakan ya bani tsoro har naji ina meh nadamar abinda na fada.
Yace"pls ki dena min irin wannan wasar bana so... " kan nayi magana ya shige dakin Momi.
Usee yace"Matar Yaya haquri zakiyi ki kuma dunga kula sosae don Yayah akwai zazzafar kishi akan duk wani abinda yake so..... "
Nide jinsa kawai nake amma hankalina atashe yake na ganin na b'ata ran mijina.Tunawa nayi bamu gaisa da Hanan ba,juyowar da zanyi kawai naga inda take zaune wayam! bata awurin kuma.
Usee yace"Haquri zakiyi don dole daga ke har Yayah ku fuskanci hakan daga gareta,ita wai adole taya mijinta kishinki take..... " Murmushi kawai nayi nace"Ina Jasmin dita?"
"Ina tsammanin bacci take.... "
"Don Allah yi maza ka tadata baccin yamma Sam babu k'yau kada kanta yazo yana mata ciwo..... "
Murmushi yayi yace"An gama matar Yayah... " ya nufi wani daki can daban.
Saukar da ajiyar xuciyata yayi daidai da fitowar Momi da Mahmood.
Da fara'arta tace"A'ah 'yata kune tafe da yamman nan? Sannu da xuwa... "
Har kasa na russuna ina gaidata cike da kunya.Mahmood fuskarsa babu yabo ba fallasa yace"Hajiyata zan dawo na dauketa anjima kadan.... " kan tayi magana yayi gaba abinsa ba tare da ya sake kallon inda nake ba.
Axuciyata nace"Ashe haka Engr. yake da saurin daukar zafi akan abu?lallai kuwa ashe ina da aiki sosae agabana..... "
Acan daki kuwa rigima ce ta kaure tsakanin Usee da kuma Hanan,ta jiyo zancensu da Fadima afalo don lab'e tayi musu.Ta hanashi tada mata 'ya.
Yace"Hauwa wai na tambayeki man? Yaushe kika fitsare kika koma haka ne?taurin kai agidan nan? Toh Wallahi baki Isa ba don Sam wannan dabi'ar ba tarbiyyar gidanmu bace,an baki haquri akan ki yadda da kaddara amma dayake ke din sokuwace marasa kishin mijinta dole kiki sauraran kowa.....
Da karfi tace"Usman ka fita daga cikin idona,Ai dama dole ka fadi hakan tunda kun hade kai wuri guda,kun nuna sam abinda Yah Mahmo yayi ba kuskure bane tunda ai shi cikinku daya dashi,ni kuwa nawa mijin tunda ba cikinku daya dashi ba ai dole ku nuna halin ko in kula akansa........ "
Dariya yayi yace"Jibi inda wawiyar ta bullo kuma?"
Ya tamke fuska yace"Kuma yau ya zamo rana ta k'arshe agareki da har zaki sake daga min murya,don kina auran yayana bashi ze saka ki sakani agaba kina min fada kamar wani danki ba,ni dinma ba tsaranki bane,daga Khairat har Labeeba babu tsaranki acikinsu balle ni,don haka take note,idan kunni yaji toh gangar jiki ya tsira,idan kuma kikace zaki cigaba da min rashin kunya,toh kuwa watarana rufe ido zanyi,xan manta Cewar ke din matar yayana ce na baki kashi sosae,idan yaso zumuncinmu dashi ya tarwatse akanki..... Yarki kuma don Allah kada ki bari atasheta idan har don kada su gaisa da Fadimar ne,don Allah na rokeki ki dunga hada mata da sleeping pills aduk sanda kika ga ko kika ji Anty Zahra zato zo,wawiyar banza kawai..... "
Axuciye ya juya ze fita sae kuma yaci k'aro da Momi wacce hayaniyarsu ce ta janyo hankalinta,rab'awa ta gefenta yayi ya fice.
Yazo ze fice daga falon gabaki daya don har yama manta da wata Fadimar don tsananin b'acin rai.
"Kanin miji haquri zamuyi duka kamar yadda ka fada dole ne duk mu fuskanci hakan daga garesu har mijin nata.... "
Allah sarki Usee sam be iya mah fushi ba arayuwarsa,duk cikinsu bayan maryam,shine na biyunsu ah haquri,komai ake mishi shanyewa yake,sam be iya maidawa babba magana ba,shiyasa abin na Hanan ya bashi haushi sosae.
Murmushi ya sakar mata"Babu damuwa matar Yayah... "
"Toh ina kuma zaka bayan Muna hira meh dadi? "
"Tsiren bakin titi zan siyowa amaryar tawa... " kafin nayi magana ya fice.Usee kenan sam bashi da matsala na ayyana hakan araina.
(U guys shld help ooo,am alrdy crushing on *'Dan rakiyar maza😁'*
Acan daki kuwa,Momi tas-tas tayiwa Hanan sannan ta fito don abin nata yakai mata wuya matuka,tayi lallashin,ta kuma nuna mata cewar tun fi'azal haka Allah ya rubuta cewar Fadimar matar Mahmood ce ba Mubarak ba,amma duk nasihun sun tashi abanza,shiyasa ta mata wankin babban riga.Babu abinda take illa kuka.Ita ba auran Fadima da Mahmood ne take jin haushi ba,A'ah ita damuwarta anan shine farin cikin mijinta da ake neman ruguzawa,bata burin ace yau mijinta ya shiga cikin wani mayuwacin hali akan Fadima,Zata cigaba da yi masa addu'ar Allah yasa ya haqura ya rungumi destiny dinsa,Allah ya sanyaya masa xuciya yaji kawai Fadimar ta fice aransa,wannan shine addu'arta akullum tun ranar data sami labarin auransu.
Kukanta shine ya tashi Jasmin,sae mutsissike idanuwa take don tabbatar da lallai kuka taga momin tata keyi.Ahankali ta saukar da kafafu daga saman gado,ta isa ga Mominta tace"Momina meya sameki kike kuka?kode kewar daddy kike ji ne? "
Uwar bata tankata ba sae aikin rera kukanta take ahankali,ganin hakan ya saka ta fice daga dakin xuwa falo,ta hango Usee da Fadima na cin tsirensu ah plate daya.Momi kuwa ta koma daki abinta bayan ta baiwa Fadima haquri akan cin fuskar da Hanan ta mata.