← Book details Shin So Daya Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 26

Sashe 21

Shin So Daya Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

     "Pls have a sit,sannan ki natsu ki bani hankalinki anan..... " Alokaci daya kowannenmu ya sami wuri ya zauna.

Ahankali ya soma da"Zaynab Abdulmaleek 'ya ce ga wani tsohon comissioner of land & housing tanan Kanon,ni da ita mun had'e ne ah *'Federal University of Nigeria,Nsukka,Enugu state'*,, ah inda nake karantar 'computer engineering' ita kuma take karantar 'pharmacy'.Mun dau tsawon lokaci muna soyayya nida ita wanda ashe mah gari daya muke da ita,soyayyarmu abar kwatance ne da sha'awa acikin campus,bamu dau tsawon lokaci ba mukai aure bayan mun k'are karatunmu da bautar kasa duka,nima kuma alokacin na samu aiki awata shahararriyar 'Electronic company' anan Kanon.shekarunmu daya cif-cif Zaynab ta koma ga mahallicinta bayan tayi wata 'yar gajeriyar jinya ta typhoid...... "

    Kuka yaci k'arfinsa wanda har hakan ya jawo na dan ji birbishin tausayinsa araina,amma dana tuna laifinsa agareni,sae kuma nan da nan nasha mur!! nace"Ba labarin soyayyarka da tsohuwar matarka nake son ji ba,labarin yadda akai ka samu aurena nake son ji,we are talking about the presence,so pls stop taking us back Mr.young man................... 📝"

   A/N
Pls kuyi manage nayi busy ne,buh next episode will be ready tmrrw Insha Allah.

     *HAFNAN*💞
*💘SHIN SO DAYA NE?💝

      *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION📖✍*

       *{Onward together}*
*{ we give the reader's of ours the best out of the best's,, our inks are melodious And dropping a kinda light's to reader's}*
'''THE PEN OF LOVE😘 HEART  TOUCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 😊 GIGGLES 😁 AND MARRIAGE THINK 💑'''
*JUST GIVE US FOLLOW.....*✔

        *MALLAKAR:HAFSAT ALMUSTAPHA*

         *WATPADD:HAFNANCY💞*

          *IG:Hafsy____mustee*

                        ✨✨✨

_*wannan page din taki ce ke daya my Janaf💞,don haka kiyi yadda kike so da ita,Allah yabar qauna da zumunci*_

                          💥💥

*KASHI NA BIYU:RIKICIN K'ARSHE*

         🌼BABI NA TARA🌼

*page 23-26*

    Wuraren 7:10 Fadima ta farka daga nannauyar baccinta,k'arar ruwan wankan Mahmood dake zuba ak'asa ne ya tasheta.Ahankali nake bin dakin da kallo,dakin namiji kenan babu ruwansa da tara kayan k'warmasai,komai tsaf-tsaf dashi,dakin dan gayu kenan,sae wani daddad'ar kamshin turaren daki ne ke tashiwa,gaskia Mahmood akwai tsafta da kuma son gayu.lalubo wayata nayi dake ajje gefen filon da nayi matashi dashi,niyyata na latso Suhaima don ranar da Abba ya maida min da wayata,toh ita kuma aranar ya damk'a mata sabuwar dalleliyar waya.

    Ban kai ga latso layin nata ba kawai naji Mahmood na kiciniyar bud'e kofar bathroom.Da sauri na maida wayar na ajje don bana son yaji duk wani abinda zamuyi discussing da ita.idanuwana fes akansa sanda ya fito,daga shi sae 'yar gajeriyar wando wato 'boxers',hannunsa rik'e da wani k'aramin towel yana tsane kansa dashi.Da sauri na runtse idanuwana tare da dauke kallona daga gareshi don tunda nayi wayau ni de ban tab'a ganin namiji balagi ahakan ba.

shi kuwa ya lura da yanayin data shiga,wato dai bata ji dadin ganinsa ahakan ba kenan.Murmushi ya saki tare da jefar da jikakken towel din agefe,Sannu ahankali ya taka sadaf-sadaf cikin sanda xuwa gareta ba tare da ta sani ba don har yanxu idanuwan nata arufe suke.Cak! ya dauketa kamar wata 'yar baby.

     Ni kuwa saurin bud'e idanuwa nayi jin wani bak'on al'amari ajikina wato ayau jikina yayi gogayya dana baligin namiji,don sosae ya rungumeni ak'irjinsa kamar wanda baya son ak'wace masa ni.

"Please dear nah meye haka? don Allah ni ka saukeni.... " na fadi hakan kamar xan saki kuka.

    Murmushi meh sauti naji ya sake kawai ba tare da yace min uffan ba.Be direni ako'ina ba sae acikin bath tub.

Yace"oya Maza ga ruwan wanka nan na hada miki kiyi,idan kuma so kike ni na miki toh shikenan.... "

    Zaro idanuwa waje nayi"sae kace wata 'yar baby? No ka fita pls xanyi da kaina.... "

Ahankali yace"Ai ke din babyn tawa ce.... " ya kashe min ido daya,kana ya juya ya lakuto min maclean akan brush sannan ya miko min,ya janyo min wani dan babban towel dake rataye akan kofar bathroom din tare da azawa saman wata igiya,yace"Ga towel nan idan kin gama sae ki dauro.... "

     Kafin nayi wata magana ya fice tare da rufo min kofar,ni kuma mamakinsa nake,taya za'ai nama fita da wannan dan towel din ya ganni ahakan?gaskia nifa bazan iya ba

      Wani b'angaran xuciyata yace"Toh wai ba mijinki bane? Idan bazaki iya fitowa ya ganki ahakan ba toh ai se ki kwan aciki..... "

   Ah sanyaye na soma wanke bakina ba.Shi kuwa yana fita,dakinta yayi,yaje ya zab'o mata wata 'yar atampa meh red pattern da adon flowers blue,daya daga cikin kayan daya bada aka dindinka mata su kenan anan kanon.Doguwar rigace 'A shape' wacce gabaki dayan gaban an mata kwalliya ne da shining stones.

     Komowa dakin yayi ya dire mata shi asaman gado,kayan kuwa yasha guga har wani fidda kyalli yake.Shi kuwa diban kayansa yayi ya nufi dakinta don jin alamun kamar ta gama wankan amma fitowace ya gagareta.Acan yayi shirinsa cikin kananan kaya as usual,kayan sun k'arbeshi sosae.

Ni kuwa na gama wankan harna daura towel din amma fitowace ta gagareni don kunyar had'a idanuwa dashi nake ahakan,towel din ko gwiwata bata gama kaiwa ba.Can de nayi shahada na murd'a kofar bathroom din na bud'e ina dan lek'e-lek'e.Ai kuwa naci sa'a ban ganshi adakin ba.Da sauri-sauri gudu-gudu na fito naje na sanyawa kofar dakin key wato na rufeta don kada ya shigo.

   Man shafawa,powder,lipstick,turare,kwalli,underwear,bra da kuma kayan sawa na gani zube asaman gado.Cikin zafin nama na sarrafa komai,na shafa komai ah inda ya kamata na shafa.Can na saka innerwears dina,sannan na warware kayan da zan saka,doguwar rigace meh k'yau sosae kuma kayan ya bani sha'awa.Da sauri na zura,nayi mamaki sosae yadda kayan ya zauna ajikina kuma ya amsheni.Nayi daurin dankwalina meh k'yau,kana na feffeshe duk wani lungu da sako na jikina.

    Ni kaina na tsorata da haduwar da nayi,sae jifar kaina nake da Murmushi ta madubi don nasan muddin oga yayi ido hudu da wannan wankan toh tabbas yana iya zaucewa.Zuwa nayi na bud'e kofar dakin,amaimakon na fita waje,a'ah sae dawowa nayi na zauna agefen gado ina wasu 'yan kame-kame kamar wata bak'uwa.Ni da gidana amma na kasa sakewa.

    Shi kuwa ya bata lokacine donta shirya dakyau,after like twenty minutes ya nufi kitchen,ya had'o kayan breakfast akan wani tray sannan ya nufo dakin.

Da sallama ya shigo,da sauri na dago kai na zuba masa idanuwa.

   "Wowwww! yanxu Mijina ne wannan hadaddan? " na fadi hakan araina,sannu ahankali idanuwana suka sauka akan abinda yake rik'e dashi.

Da hanzari na mik'e na nufeshi,shi kuwa daskarewa yayi awaje d'aya yana kallona ya k'asa furta ko da kalma d'ayace agareni,sae yi yake kamar ze hadiyeni.K'arban tray din hannunsa nayi nazo na ajja ak'asa.

    "Wowwww! seriously is diz M.Nakowa's wife?Babyna kinga yadda kika fito sharr! dake kuwa?agaskia ba don za'ace nayi son kai ba toh da kuwa nace matata is the most beautiful creature in this world..... "

    Xancen nasa sosae yayi min dadi,kokarin magana nake sae gani nayi ya katse min hanzari ta hanyar sanya 'yar yatsarsa akan leb'ensa"Shhhh! matata pls don't deny,juz believe me ke din k'yakk'yawace.... "

    Ahankali na furta"mijina kaima din k'yakk'yawan ne ai.... "

Cike da farin ciki ya furta"Allah da gaske kike matata ina da k'yau?"

   "Har mah ka fini,fari ne de kawai xan nuna maka.... "

B'ata fuska yayi sosae yace"Ki dena cewa na fiki k'yau don ba gaskia kika fada ba.... "

     Zan musa masa yace"Shhhh! it's okay let's have breakfast am hungry my wife.... "

Nace"shine baka tadani na hada mana ba kai kayi da kanka? " na fadi hakan ina d'an bubbuga kafafuwana akasa.Kallona yake dauke da sha'awata ak'wayar idanuwansa.

    Yace"Yanzu shikenan saina tada sarauniya tana baccinta meh dadi? Ni idan mah zaki yadda zan fison ace na dunga miki bauta,naki kawai kici,kisha,kiyi ibada,kwanciya,ki kula da mijinki ta b'angaren hakkinsa,sannan kuma sae haifa mana k'yakk'yawan 'ya'ya kamarki,naki kenan...... "

Cike da kunyar jin maganganunsa na duk'ar da kai kasa,russunawa nayi har kasa nace"Mijina ina kwana? Ya jikin naka? "

    Matsowa kusa dani yayi,ya russuna kamar yadda nayi yace"Bazan amsa ba,yanxu ne gari ya waye mana har kika ganni? "

"Kayi haquri don............... "

    Wani irin k'arar bubbuga kofa muka jiyo,kofar da zata sadaka da sashin namu.Bugu ake bana wasa ba wanda hakan ba k'aramin razanamu yayi ba musamman ni wacce saurin mik'ewa nayi jiki na karkarwa kamar wacce ruwan Sama yai wa dan banzar duka.

    Ji mukayi ance"Mahmooda kana iya?Maza ka hanzarta bud'e mana k'ofa..... " da k'arfi aka fadi hakan.

Arayuwata na duniya harna mutu baxan tab'a manta meh muryar nan ba,muryar *'HAJIYARSU MAHMOOD'* kenan.

   Atsorace nace"Mahmood ba muryar hajiyarka nake ji ba? "

Cike da tashin hankali yace"Wallahi kuwa itace..... "

    Kuka na fashe dashi nace"Mahmood kaga abinda nake ta jiye mana amma kai kaki ka gane ko? Yanxu na tabbata taji labarin auranmu ne shine tazo da wannan tashin hankalin,wai kai azatonka zancen aure yana b'oyuwa ne?toh ni dai gaskia banzo da shirin fuskantar tashin hankali agidan aurena ba,dududu mah yau kwanana daya rak! da tarewa shine har zan soma fuskantar.......... "

    Karar girgiza k'ofar da ake ne ya katse min maganata,can aka ce"wai Mahmood baya jina ne ko kuwa so kake na sanya spare key na shigo? "

Agigice nace"Look Mahmood dear u juz hav to do something Cuz am not going out there to face her & her humiliations..... "

    Yace"okay abinda nake so dake kawai ki tsaya anan,ina fita kiyi saurin sanya key ki rufe k'ofar..... "

   "Okay" kawai na furta.Ya juya ya fice,ni kuwa fadawa kan gado nayi,wani dan marayan kuka ne naji yana nemar kufce min,ai kuwa da sauri na sanya hannu na rufe bakina har da matseshi sosai wai don kada kukan yayi nasarar kufcewa.

    Ahankali na furta"Yah salam! meke shirin faruwa dani ne?"

Shi kuwa Mahmood yana bud'e kofa,babu b'ata lokaci Momi ta tureshi gefe,suka samu suka shige ciki gaba d'ayansu.

  Cike da fargaba Mahmood yace"Momi........... "

Da sauri ta daga hannunta tace"You are not allowed to utter any word,you hav the right to remain silent till am done with my investigation........ "

    Da k'arfi tace"Khairat wai meh kuke jira ne? Let the investigation commence immediately,ku bincika min duk wani lungu da sako na cikin dakunan gidannan,idan har kuka ga wani abinda be dace ba toh ina son ku hanxarta fitar min dashi nan,ina fatar kun gane abinda nake nufi? "

   Khairat da Labeebah ne kawai suka amsa mata da "Mun gane Momi.... "
Chapter 21 · 0% Book details