Sashe 22
Shin So Daya Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ita kuwa Meema samun wuri tayi ta xauna,dama shi Usee tuni ya nemi gu ya zauna.Khairat ce ta nufi hanyar ainihin dakin Fadima,ita kuwa Labeebah dakin Mahmood ta nufa inda anan ne Fadimar take.
Dundu Momi ta saukarwa Meema agadon baya tana fadin"Shegia zaki tashi ne kiyi abinda nace ko kuwa sae naci ubanki? Banza kawai mara kishin uwarta..... "
Da sauri Meema ta mik'e tana turo baki gaba cike da haushin wannan bak'on halin na uwarta.hanyar wani daki ita kuma ta nufo don yin bincikenta.
"A'ah Labee dakata anan,karki kuskura ki shiga wannan dakin,na yarje muku da ku binciki kowanne amma banda wannan duk da cewar ban san abinda kuke bincike akai ba amma karde ashiga wannan...... "
Haka suka ji Mahmood ya fad'a babu alamun wasa atattare dashi.
"Dan kutumar ubanka har kai ka isa na bada umarni sannan kai ka take ka hana?yaushe aka haifeka? Ko mantawa ne kayi da wacce take tsaye agabanka take kuma bada wannan umarnin?idan kuwa mantuwar ce kayi toh ina meh tunatar dakai cewar Haj.Fatima Binta Mu'azu mahaifiyarka ce........."
Ta juya ga Labeebah wacce duk ta gama tsorata da yanayin yayan nata shiyasa taki gaba"Maza Labeebah shige ciki ki min bincike ko kuma ni nazo nayi da kaina...... "
Saukar da ajiyar xuciya yayi bayan ya tuna cewar ai ya sanya Fadima ta rufe k'ofar.
Ni kuwa ina daki ina jin duk wani abin dake wakana afalon,jikina sae rawa yake don tsananin tsoro,xuciyata kuma kamar zata fasa k'irjina ta fad'o waje don fargaba.Ina jin umarnin da aka baiwa Labeebah,da zafin nama na mik'e don tunawa nayi da cewar ban rufe k'ofar ba kamar yadda ya umarceni da nayi.
Ban kai ka isa k'ofar ba sae gani nayi ta fad'o dakin,fuska sam babu ko digon annuri akansa.Da mamaki take nuna ni tace"Fadima you?budurwar Yah Mubarak? Meh kike anan? "
Cike da fargaba na daure nace"Ni ba budurwar Mubarak bace.... Am *'FADIMA SA'AD MAINASARA'* matar *'MAHMOOD NAKOWA'*
Cike da tashin hankali tace"Shut the hell up!! karya kike,taya za'ai ki zama matar Yah Mahmo?kuma....."
"Malama investigation aka sanyaki kiyi ba interrogation ba,don haka you have no right to question me,nice nan abinda be dace ba abincikenku,so kindly arrest me,tambayoyi kuma oganki ce keda right ta min bake ba.... Let's go...... "
Na lura sosai jikinta yayi sanyi da kalamaina,shige gaba nayi na batta tsaye kamar gunki tana bina da kallo.
Shi kuwa Mahmood yana ganin Labeebah tayi nasarar shigewa dakin,ya furta "Yah salami! Shikenan ta faru ta k'are,ruwa ya k'arewa dan kada...... "
Wuf! Momi tayi ta Mik'e ah sa'ilin da tayi ido hudu da Fadima sa'ad,ita kuwa Fadimar 'yar kissa sae jifar Momin take da Murmushi.
Russunawa har k'asa nayi nace"Momi kune da sassafe haka? Sannunku da xuwa,ina kwana? "
Cike da mamaki Momi tace"Ke saurara min nan!!.... Meya kawoki gidan nan kuma meh kikeyi acikinsa? "
Fuskar mamaki nima na shimfid'a mata kana nace"Momi Kamar ya meh nake yi agidan nan? mace da gidan mijinta kuma har sae an tambayeta abinda take acikinsa?....... "
Kafin Momi tayi wata magana Khairat ta k'arbe wacce fitowarta kenan daga dakin Fadima kuma duk taji abinda ake fada tace"Wai ni ban gane xancen da ake ba anan,dodon kunnuwana sunki su yadda cewar wai Fadima budurwar Yah Mubarak ce matar Yah Mahmoh..... " (duk sun shaidata don gabaki dayansu an kaita wajensu sun gaisa alokacin da suka kai ta'aziyyar rasuwar mahaifinsu).
Momi ce tace"Ban san meh yarinyar nan tayiwa ya'yana Maza ba da har suke rawar kafa akanta,Mubarak ya wulakanta 'yan'uwansa akanta,yanxun kuma wansa ya aure masa wacce yake haukar akanta,wannan cin amanar da meh yayi kama?"
Juyawa tayi ga Mahmood tace"Munafiki,ashe da gaske din ne kayi aure shine ka b'oye min har baban Zali ya shige maka gaba,Mahmood meh na maka da har ka zab'i ka b'oye min al'amari meh girma haka?"
Murmushin takaici tayi,kana ta cigaba"Koda yake da gani ba yin kanka bane,asiri ce tayi tasiri akanku daga kai har dan'uwan naka...... "
Afusace nace"Mahmood why are u silent?why can't u open ur mouth and defend me? Meyasa bazaka fad'a musu ta yadda akayi ka aureni ba? Ka tsaya kurum ana zagina alhalin am innocent?shin haka mukayi dakai?..... "
Khairat tace"Labeebah wai meh muke jira ne da bazamu soma cin ubanta ba? "
"Ahir dinku! kada wata 'yar iska acikinku tayi gangancin tab'a matata,idan kuwa hakan ta faru toh wallahi sae na lahira yafi yarinya jindadi.... "
Tasss! Kakeji Momi ta wanke masa fuska da mari,tace"Ai dole ka fadi hakan tunda asiri ya gama cinka,Shima baba Mu'azzam din yanzun nan zanje naji dalilin daya saka ya shige maka gaba Sannan naci masa mutunci daga shi har zuri'arsa,ku kuma ku jira dawowata akaro na biyu don ban gama daku ba....... "
Ta juya gasu Khairat tace"Ku taho mu tafi..... "
Ta fice abinta,Khairat tace"U are welcome to Nakowa's family,duk wani tashin hankali is awaiting you in diz family..... "
Labeebah kuwa cewa tayi"will soon be coming back for you,a betrayer kawai..... "
Mahmood yayi wani mahaukacin taku biyu zai damkosu,ai kuwa da hanzari suka fice da gudu.Ita kuwa Meema meh k'aryayyan xuciya kamarni nan Hafnan har ta soma xubar da kwalla.
Tace"Yah Mahmo,Anty Fadima don Allah kuyi haquri,ga shawara idan zaku k'arbeta,kawai ku biyomu gidan Baba Mu'azzam din ayita ta k'are... "
"Nifa idan zasu bi ta tawa kawai subar garin if not wallahi yanzu kuwa suka soma ganin tashin hankali"acewar Usee.Wani uban harara Meema ta kwasheshi dashi tace"Kai dai wallahi baka da correct thinking of a man,shiyasa Momi ke kiranka da *'DAN RAKIYAR MAZA'*.... 😀"
Kafin yakai ga bata amsa kawai yaji Momi na kwala masa k'ira,da sauri ya fice yana meh cike da jin haushin abinda yayar tasa ta fad'a masa.
Mahmood ya saukar da ajiyar xuciya yace"Meema jeki gamu nan tahowa.... "
Da gudu-gudu ta fice don kada taci ubanta ahannun Momi.
Ni kuwa kuka nake sosae kamar raina ze fita,yanxu atunaninsu asiri nayiwa Mahmood kenan ya aureni ko meh?
"Fadimata pls tashi mubi bayansu... " haka naji ya fad'a yana meh kokarin yafa min mayafi ajiki.
Axuciye nace"babu inda zani,ni kawai ka bani takaddar sakina...."
Dakyar da sudin goshi da kuma wasu 'yan dabaru nasa ya samu ya lallasheta har ta haqura ta yarda zata bishi gidansu baba Mu'azzam din................ 📝
A/N
Yanzu meh kuma ze faru gidan baba Mu'azzam? Ku biyo
Sorry for the late post,wallahi was kinda busy ne yau!!
*HAFNAN CE💞*
https://mobile.facebook.com/Intelligent-Writers-Association-1194933670662901/
*💘SHIN SO DAYA NE?💝*
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION📖✍*
*{Onward together}*
*{ we give the reader's of ours the best out of the best's,, our inks are melodious And dropping a kinda light's to reader's}*
'''THE PEN OF LOVE 😘 HEART TOUCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 😊 GIGGLES 😁 AND MARRIAGE THINGS 💑'''
*JUST GIVE US FOLLOW.....*✔
*MALLAKAR:HAFSAT ALMUSTAPHA*
*WATPADD:HAFNANCY💞*
*IG:Hafsy___mustee*
✨✨✨
*KASHI NA BIYU:RIKICIN K'ARSHE*
*🌼BABI NA SHA DAYA🌼*
*page 29-30*
Ummata na k'ira wacce muna gama gaisawa ta rufeni da fada,wai dole na ajje wannan baccin safen nan agefe wanda ya riga ya gama bi min jiki,tace idan ban kama jiki na watsar da kiwiya agefe na dunga kula da mijina ba,toh kuwa namiji shi babu ruwansa,idan yaga bakya masa abunda yakeso toh kuwa yana iya banka miki kishiya wacce zata zo ta dunga kula da bukatunsa da kuma tattalinsa,ke kuwa awatsar dake agefe ki koma 'yar kallo.Mun jima tana min nasihu meh ratsa xuciya,daga bisani mukayi sallama.Shima Abbana na k'irashi mun gaisa.Har yake labarta min irin yanayin da Umma ta shiga alokacin da take ta k'ira amma babu amsa.Dariya nayi sosae tare da jin wani irin soyayyar Ummata na ratsa jinin jikina.
Kai tsaye na latso _*My Ashwairiyya*_.
Ita kuwa awannan lokacin ta fito wanka kenan,tana gaban madubi tana taje kanta,so take taje taga dakin Suhaima.Wayarta dake gaban madubi taji ya dauki kida,da hanzari takai hannu ta dauketa.
*'Fateenah'* shine sunan data gani yana rawa akan screen,gabanta ne taji ya bada rasss!.... Jefar da comb din hannunta tayi tare da mik'ewa da sauri har jikinta na dan rawa don tsananin tsoro da kuma fargabar abinda zataji daga sahibar tata.
"Hel....lo... Fateenah'...... " haka ta fada cike da in-inna ah sa'ilin da tayi picking call din.
Bushewa da wani irin dariya nayi don nasan abinda take yiwa wannan rawar muryar,wato atunaninta tsantsar tashin hankali zata tsinta daga gareni shiyasa take cike da tsoro. Allah sarki my Ayush komai yayi chas-chas ahalin yanxu.
Nace"Malama idan zaki daidaita muryarki toh tun wuri mah ki daidaita don ni yanxu babu abinda nakeso sama da mijin da kuka hana min saninsa da wuri sae akurarren lokaci...... "
Kwashe komai nayi na gaya mata tun wucewarsu,tarewata da kuma rigimarmu adaren farko,sae kuma sabuwar rigimarsu Momi da kuma xuwarmu gidan Baba Mu'azzam da kuma nasihunsa agaremu,sae kuma sulhun da aka nema.
Wani wawan ajiyar xuciya Ash ta sauke,cike da murna tace"Wayyyo! Fateenah' ina zan saka kaina don murna? Agaskiya naji dadi ba kadan ba da har kika haqura kika rungumi mijin kaddararki,fateenah wlh believe me Mahmood shine kalarki ba Mubeen ba,wlh ni dama can ina ta miki kwadayin aurensa sae gashi lokaci daya Allah ya amsa addu'ata,ya zamo mallakinki,yanzu dai addu'armu shine Allah yasa Mubarak ya fahimceku ya kuma gane cewar wani baya taba auran matar wani,haka zalika wata bata taba auran mijin wata........ "
Cike da sanyin murya na amsa mata da "ameen." Tace min tana shirin xuwa gidan Suhaima ne,nace yanzu Muna gama waya ita zan kira.Mukayi sallama.
"Nima ahalin yanxu babu abinda nakeso kamar matata wacce naki bayyana kaina agareta sae akurarren lokaci..... "
Da sauri na waiga tare da watsa masa wani Irin kallon soyayya,ware min hannayensa yayi.
Ahankali ya furta"Babyna I nid a warm hug...... "
Babu b'ata lokaci na isa gareshi tare da fad'awa jikinsa,sannu ahankali ya maida hannayensa ya rufe yana meh dada kankameni.kunnuwana dake saman k'irjinsa ya sanya nake iya jin yadda xuciyarsa ke bugawa da sauri da sauri.Ahankali na lumshe idanuwa ina meh jin wani irin sonsa na ratsa jinin jikina.
***
Ash cike da farin ciki ta Latso su Leedar da Fresh take labarta musu zancen Fadimar,suma din sosae sukai murna tare da musu fatar alheri da kuma addu'ar Allah yasa Mubeen ya fahimcesu.