Sashe 14
Shin So Daya Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Su Mama Jamila ne suke ce min zasu wuce,ai kuwa kuka na sakar musu ina cewa nima binsu xanyi.
Mama Sadiya ce tace"Yau ga sakarya,Yo! ai wannan itace ake kira da auren ai,gashi mun kawoki gidan mijinki inda kike ta mararin xuwa..... kinga ni cika min gyale..... "
Haka su Mama Sadiya mah suka min,suka tureni suka fice har su Ash. Sae kuka nake wiwi kamar wata k'armar yarinya,su Mami kuwa sae aikin rarrashina suke.
Sae bayan isha'i akace min nazo mu tafi ga angona ya taho daukata,mamaki nake tayi wai ace da daddaran nan ne xamu kama hanyar Zaria? Kamar na tambayi su mami ko Zariar ce zamu tafi da daddaran nan amma sae naji na kasa.
Falon Baba kamar yadda naji ake k'iran mahaifinsu Hafeezah aka kaini,anan naga angon nawa Xaune akasa yana sauraron jawabin Baba.
Kun san wanene mijin nawa?? Its still Engr. Mahmood Mustapha dai nake gani zaune agabana,sae ayanzu na tabbatar da cewar Yes! shi din ne de mijina.
Tuni naji wani irin tashin hankali ya min sallama,taya akai ya sami aurena? meh yayi wa mahaifina har ya bashi aurena? Dama ze iya cin amanar Mubarak ban sani ba? Inasu mummy da sauran kannansa don ga dukkan alamu ya nuna cewar basu da masaniyar auren,kamar b'oye musu yayi,sannan kuma su waye Baba Mu'azzam da kuma Mamin Hafeezah agareshi? Anya ba hayar iyaye yayi ba don su tsaya masa akan wannan aure ba kuwa?
Wani murmushin takaici nayi ina meh raya wasu al'amura araina,ni kadai kurum nasan tashin hankalin da zan haifar muddin muka sanya kafa muka bar nan gidan.Ni kadai nasan tanadin dana yiwa Engr. Mahmood bayan ya gama labarta min dalilinsa na auren *'BUDURWAR KANINSA'*..................... 📝
A/N
Tofa my people mun fa iso gun.... Wani kudiri ne kuma ke ah cikin ran Fadima? Meh take shirin yiwa Engr. Mahmood? Ku dai biyoni.
*IT'S HAFNAN*
*💘SHIN SO DAYA NE?💝*
*MALLAKAR:HAFSAT ALMUSTAPHA*
*WATPADD:HAFNANCY*
*IG:Hafsy__mustee*
💥
*KASHI NA BIYU:RIKICIN K'ARSHE*
🌼BABI NA UKU🌼
*Page 6-9*
"Mama bara naje nima na kimtsa kada su wuce wajen reception d'in nan bani..." acewar Anty Hajaar wacce tana gama fad'ar hakan ta mik'e tabar dakin xuwa sashin da aka saukesu.
Kaka rigima ta rakata da "Toh! adawo lafiya Hajara,Allah sarki an girma ba'a san an girma ba,yanxu fisabilillahi taron k'ananun yara mah sae sunje.... Koda yake Allah ne ya kawo mu xamani..."
Ai dole ne Anty Hajar tama je wannan reception din ko don taje tayi ciye-ciye ta kuma nunawa duniya cewar ita din fah uwar amarya ce.Maminsu Hafeezah mah zataje don ita da Mahmood suna mugun d'asawa da k'yau.
Ash ce xaune tare da Zuzu ah barandar sashin da aka saukesu.Hirar Khaleed Zuzu ke bata wanda ga dukkan alamu ya nuna cewar gayen ya gama tafiya da imaninta.Ita Ash din mah da akewa hirar amsawa kawai take da "uhmm" ko kuwa "a'ah",don kusan xan iya cewa gabaki daya hankalinta ya tafi ne ga su Fadima.Sae ayanxu ne take ganin wautarta na k'iran shi Mahmood d'in daya zo ya lallashi Fadimar bayan tasan muddin Fatin nata na had'a idanuwa dashi amatsayin mijin da aka aura mata,toh kuwa komai na iya k'wab'ewa,anything can happen!.
Oh! Allah!! akace dana sani yakan zo ne bayan ka aikata ba daidai bah,akan k'irashi da *'dana sani mara amfani'*,data sani kawai ta lallab'ata ta saka kayan don tasan Fatinta komin fad'arsu de tana jin maganarta,kuma tasan xata sauko ne har ta haqura taje reception din,amma da yake iyayi yayi mata yawa,kai tsaye ta k'ira Mahmood din da yaxo gareta,iyayinta ya janyo tana neman haifar da tashin hankali acikin jama'a wanda ta fison ace sae an kai Fadimar gidansa,asannan kowa ya kama gabansa kafin tasan wanene mijinta,tasan duk wani tashin hankali da ze biyo baya alokacin zai iya xuwa da sauki.Wurin reception mah ba lalle ne Fadimar ta gane Mahmood din ba tunda duk'ar da kai zatayi tayi,balle mah tasan halin Fadimar sarai da alkunya,zaiyi matuk'ar wuya ta masa kallon tsaf acikin jama'a.Koda ace tama gane shi,tasan Fadimar baxata tab'a kunyatar dashi idanuwan mutane ba har sae sun k'ebe.
Toh! yanxu gashi ta janyo k'ebewar tasu da wuri tun mutane basu gama watsewa ba,kuma tasan anything shitty can happen.
Axuciyarta tace"Ohh! ni Ayshatu wat have I done? meya kaini k'iransa? "
Xuciyarta babu abinda yake yi illa bugawa da sauri da sauri,kasa kunnuwa tayi tana meh jiran ta jiyo hayaniyarsu Fadimar sannan tayi ciki wuf!.Zuzu de data ga sam hankalin Ash din baya gareta,sae kawai taja bakinta tayi shiru,ita Allah-Allah mah take su Fadimar suyi su gama soyayyarsu kamar yadda take tunani sannan ta shiga taje ta tsalawa Khaleed dinta kwalliya.
Anty Hajaar ce tazo shiga sashin,da hanxari Ash ta mik'e tare da shan gabanta.
Wani irin kallon banza ta jefawa Ash din,kana tace"marasa kunya meye kuma haka? Ko de wata sabuwar salon rashin kunyarce ta motso miki shine hadda wani shan gabana?"
Dan murmusawa kawai Ash tayi,kana tace"Yana de gab da motsowa.... So nake kawai nace miki ki d'an dakata,ango na ganawa da amaryarsa aciki........ "
Hab'a Anty Hajaar ta rik'e,kana tace"ikon Allah!... nide tunda na budi ido nayi wayau ban tab'a ganin rashin kunya da da'a irin wannan ba,Muido da wannan angon nata sam basu da alk'unya ko kadan musamman mah angon nata,ai sae ya bari iyayenta su tafi kafin ya shiga wurinta suyi shashancin nasu son ransu........ "
Wani kallo ta watsawa Anty Hajaar,ta dubi inda Zuzu take taga mah sam hankalinta baya garesu,hasalima wayarta take daga can d'an nesa da inda suke tsaye.
Ahankali Ash tace"Dad'ina dake Anty akwai ki da iya jan k'aramar magana tayi tsayi da kuma janyowa kanki raini awajen kananan yara,ina ruwanki da koma meye ya shiga yi? Ina ce ko matarsa ce ba dadironsa ba? Don Allah Anty Hajaar ki dunga kama girmanki kada ya gama xubewa ah idanuwanmu mu yara..... "
Tana gama fad'ar hakan ta koma mazauninta,sae duba agogo take awayarta,yanxu haka takwas ta wuce da mintuna goma,akalla Mahmood ya shafe kusan mintuna ashirin aciki yanxu.Ita kuwa Anty Hajaar jikinta ne yayi sanyi qalau don bata tab'a jin k'unyar kwab'o ba arayuwarta sae yau da Ash ta mata.Sae taga rashin dacewar maganar daya fito daga bakinta.Jan jikinta tayi xuwa ga wani k'aramar kujera ta tsakar gida ta xauna.(lol maganin irinku kenan Anty Hajaar... Ash kin biyani....)
***
Idanuwana dani k'aran kaina mun kasa gasgata cewar wai *'ENGR. MAHMOOD MUSTAPHA'* dan'uwan Mubarak ne tsaye agabana amatsayin *'MIJIN KADDARATA'*
Sake kai yatsu nayi ina murza idanuwana akaro na uku don tabbatarwa kaina cewar mafarki nake kuma wanda ke tsaye agabana ba 'ENGR.MAHMOOD' my brother inlaw bane.Harda mitsilin kaina nayi wai ko mafarki nake na farka,amma uban Zafin dana ji ne ya saka nasan ba mafarkin nake ba,this is reality!!!.
Da rawar murya nace"Don Allah meh kake yi anan?"
Gaban Engr.ne ya buga wata irin ganga,fargaba da kuma tsoron actions din da Fadima xatayi taking duk ya cika masa xuciya fal! amma da yake shi din namijin duniya ne,sae be bari ta gano weakness dinsa ba.
Fuskar mamaki ya shimfid'a mata,kana yace"Ban gane meh nakeyi anan ba? all what I know is dat wajen matata nazo...... "
"Wacece kuma matar taka? " na fadi hakan sanda naji xuciyata na wani min mugun zogi.
"Of cours! Fadima Sa'ad Mainasara amaryar Engr.Mahmood Mustapha...... "
Da hanzari na katseshi"k'arya kake mak'aryacin banza,mak'aryacin wofi,you can never be my husband ko amafarki,ni bah kai na aura ba,ni *'MAHMOOD NAKOWA'* na aura not *'ENGR.MAHMOOD MUSTAPHA'* because am very pretty sure dat brother inlaw bazaka taba cin amanar d'an'uwanka ba,bazaka tab'a yaudararsa ba,haka kuma nasan bazaka tab'a bin bayansa ka k'wace masa ni ba...... "
Wani irin mugun d'aci ne Mahmood keji aransa na jin irin wannan kalaman da Fadima take jefarsa dashi,yab'onsa take ko kuwa maganace mara dad'i take jefa masa?
sassauta muryata nayi,da rawar murya meh had'e da kuka na cigaba da magana"pls brother inlaw meya kawoka gidan surukaina?ko kuwa kaima kana cikin abokan ango ne? kuma ina mijina yake da har ya barka ka shigo har inda matarsa take?okay yanxu na gane,ka samu labarin cewar nayi aure shine kazo kaci min mutunci don na yaudari d'an'uwanka ban aureshi ba..... "
Had'a hannuwa wuri guda nayi kana nace"pls na rokeku don Allah kuyi haquri ba laifina bane nima din biyayya kurum nayi,don Allah kacewa d'an'uwan naka daya gafarceni ba laifina bane,albarqan iyayena nake nema shiyasa na amince da xab'insu.... Pls brother inlaw ka tafi kada mijina ko wani ya shigo ya ganka anan....... "
Wasu 'yan kwalla ne yaji sun ziraro masa saman kunci na tausayin kansu daga shi har Fadimar,da hanzari ya juya ya fice daga dakin kamar yadda ta buqata.k'aron farko daya soma ganin rashin dacewar auren Fadima da yayi gashi yanxu tana denying dinsa akan bashi ne wanda aka aura mata ba don baze iya cin amanar dan'uwansa ba.
Maganar 'cin amanar' data ambato shi yafi tsaya masa arai.Anya kuwa ya k'yautawa Mubarak kuwa? Taya kuma xasuyi zaman aure da Fadima bayan Mubarak dan'uwansa ne,his blood brother,ai kuwa kusan koda yaushe Ze dunga haduwa da Fadimar musamman ah family house. And anything bad can happen!.
Shi fa bema taba tunanin hakan ba,burinsa kawai ya mallaki Fadima shikenan an gama komai.Gashi yanxu ya mallaketa din ba tare da sanin mahaifiyarsa ba,yan'uwansa da kuma shi uban gayyar wato Mubarak.wani irin yakine za'ayi idan Mubarak din ya dawo? amsar da be sani ba kenan.Amma shi de abinda ya sani shine,*'MATAR MUTUM KABARINSA'*.... Dama can Allah ya riga ya rubuta cewar Fadima matarsa ce shiyasa lamarin aurensu yazo da hakan.Shi de addu'arsa Allah yasa Fadima ta fahimci dalilinsa na aurenta sannan kuma ta soshi su xauna lafiya.
Koda ya fita daga dakin,wurin Haj.Faiza ya nufa wato maminsu Hafeezah don gaya mata cewar anyi cancelling xuwa reception din,don baze so ya matsawa Fadimar mah azo ayi tashin hankali yadda mah yaga yau idanuwan nan nata atsattsaye suke na shirin sauke kwandon bala'i.baze so ace komai ya k'wab'e musu agaban jama'a ba don su karan kansu Baba Mu'azzam da iyalensa basu san Fadimar bata san cewar Engr. ne mijinta ba,all their taught ta sani kuma tana sonsa shiyasa ya shige masa gaba wajen neman aurenta.