← Book details Shin So Daya Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 26

Sashe 5

Shin So Daya Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

    Baba ne yake gayawa Mubarak cewar ai gashi-gashi,be bari ya k'arashe ya mik'e zumbur!,idanuwansa sun canza launi xuwa pure hot red,ya dubi inda Mahmood ke zaune yace"Mahmood kaci amanata,ashe dama komawarka Zaria sabida ka samu kusanci da budurwata ne?ashe duk wani taimakon da kake ta ikrarin zaka min kanka kake tayiwa?Haba shiyasa Jiddan Mubarak ta canza min,kwata-kwata Idan mukayi waya bana gane kanta,koda na dawo mah Kowa beyi murnar dawowata ba sae mah tashin hankalin dana lura kowa ya shiga,atunaninku ni Mubarak ban yadda da kaddara bane ko menene da har za'a tara min mutane ana kuma min nasihu? Toh ku sani na yadda da ita,na yadda cewar abinda Allah ya rubuta cewar ba naka bane tofa komin tsiya bazaka tab'a samunsa ba,ni tun farko mah da'ace ka nuna min cewar kana son Zahra,toh wallahi ina iya bar maka ita sabida nima ina son naga kayi aure Yah Mahmood.......... " shiru yayi jin wani irin azababban ciwon kan dake nemar masa sallama.

   Duk jikin kowa awurin seda yayi la'asar,masu hawaye nayi,masu shesshek'a suma ba'a barsu abaya ba,sosae Mahmood yayi dana sanin biyewa son xuciya,ahankali ya soma magana"Brother haqiqa ban k'yauta ba dana biyewa son xuciya,cin amana yana daga cikin halayen munafurci,cin amana yana daga cikin abubuwan da suke tauye imanin mutum,cin amana yana daga cikin abubuwan da suke qasqantar da darajar mutum awajen Allah,cin amana yana sanya mutum yayi baqin jini acikin al'umma,haka kuma zalika cin amana yana zama sanadiyyar dulmiyar da mutum acikin wutar jahannama.......... "

   Mubarak baze iya jure ganin dan'uwansa na suffanta kansa da wa'ennan zantukan ba,da sauri ya isa inda Mahmood din yake ya rungumesa"No brother pls stop it,ka dena suffanta kanka da wa'ennan zantukan naka da babu dadin ji,wallahi ni baka ci amanata ba,dama can haka Allah ya rubuta cewar kai din Mijin Fadima ne bani ba,kawai ya tsara cewar ta sanadiyyata ce zaku had'e,come on brother wallahi ni na yadda da kaddara,dadina ayanxu kayi aure kamar yadda muka jima munata mafarkin faruwar hakan,and am assuring u dat Fadima Zahra will make a good home for you....... "

   Kamar hadin baki,kowa ya dau tafi da hamdala ga ubangiji,basu taba tunanin cewar komai zaizo musu da sauqi haka ba.(ni kaina Hafnan da fans dina mun dauka za'a yi yakin duniya ta uku ne kafin adaidaita,sae gashi Mubeen ya tabbatar mana da cewar shi din cikakken Mumini ne meh yadda da kaddara meh k'yau ko mara k'yau).

   Baba ya sake nasiha meh ratsa xuciya da gangar jiki,haka goggo Ladidi,da Mami da kuma Momi kowa seda ya tofa albarkacin bakinsa,daga bisani aka nemi gafarar juna da k'yau,sannan kowa ya watse.Washeqari seda muka sake cimma Mubarak agidansa,dayake aranar ya tattara iyalinsa suka koma gidansu,muka sake nemar gafararsa da k'yau,yace mana"Haba Yaya wannan wani irin abu ne?Nace maka wallahi baka min laifin komai ba,haka Allah ya tsara abinsa tun fil'azal,yanxu Idan nayi wani tashin hankali hakan na nufin ni din ban cika mumini meh kuma imani ba,tunda har na kasa yadda da kaddara,ina son ka sanya aranka cewar Fadima dama can ba tawa bace,Kila babu alheri ne acikin aurena da ita,da'ace na nace saina aureta,Kila bayan auran musifu kala-kala su kunno kai,don haka ni nama yi farin ciki da ban auretan ba,kaine alherinta shiyasa Allah ya hadaku,fatana ayanzu Allah ya yaye min sonta axuciya..... "

   Haka muka baro gidan jikinmu asanyaye.Kwananmu biyu muka dawo Zaria.Bayan kwana biyu kuma Mahmood ya kaini ganin gida,toh agaban Mahmood dinne na fayyace musu abinda yayi ta faruwa.

    "Ikon! Allah kenan,dama haka Allah ya tsara abinsa,Allah ya dada baku zaman lfy.... " shine abinda Abba da Umma suka fada.

Su Ash dasu Leedar kowa mah yayi matuqar mamaki da farin cikin ganin komai yazo da sauqi.Suma suka qara mana addu'ar samun zaman lfy.

***
_*BAYAN WATANNI BIYU*_

Hanan ta sauka lafiya tare da taimakon Mubarak,da kanta ta haihu wannan k'aron lfy qalau kuwa sabida ba k'aramin kulawace ta samu awannan cikin ba,sannan kuma addu'a baya faduwa Allah ya qarbi koke-kokensu ya sanya ta sauka lfy.Qatoton baby meh kosasshiyar lafiya ta haifo,yaro kamar Mubeen yayi kaki ya tofar.Ana gobe suna,Mahmood ya kaini kano,ah family house na kwana,washeqari da sassafe muka dunguma xuwa gidan suna,su Umma sun min kara ba kadan ba,ita,Ash,su Lubna da kuma Suhaima wanda Leedar ne ya bata izini suka zo.Ranar suna yaro yaci sunan Mahaifinsu Mubeen wato *MUSTAPHA*,se aka sakaya ana k'iranshi da *IRFAN*.,bayan kwana biyar da yin suna,Hanan ta shirya ta tafi maiduguri wajen iyayenta don kam ta dade bata je ba.se bayan 40days ta komo Kano.

       ***
_*AFTER NINE MONTHS*_

     Allah ya saukeni lafiya,yayi min baiwar da ba kowacce 'ya mace yake yiwa ba,wato haihuwar ya'ya uku atake.Mahmood ya rasa inda zesa kansa don murna,tuni ya saka aka yada agidajen radio.Har kukan murna seda yayi,shi meh son 'ya'ya kamar meh sai gashi tashin farko Allah ya azurtashi da 'yan uku,maza biyu da mace daya,mazan duka suna matukar kama ne dashi,hasken fatata ce kawai suka dauka,macen ne kawai take kama dani kamar an tsaga kara an k'arya.Mahmood yayi barin naira da kuma rarraba kyaututtuka ah haihuwar 'yan uku,ni kuwa k'yautar wata sabuwar dalleliyar motace ya min,yanxu motocina sun zama biyu kenan,ga tasa daya ban,sannan kuma da nawa da nake hawa alokacin ina budurwa wanda Abba ne ya saka aka kawo min ita alokacin mun dawo daga kano sabo-sabon amarcina.

   Ranar suna,yara suka ci sunan,baba mu'azzam ana k'iransa da Hassan,dayan kuma sunan Abbana aka saka masa wato Sa'ad,ana k'iransa da Hussain,macen kuma Zaynab aka saka mata,ana kiranta da Afra.Bayan suna na kira Ash na mika mata tsohuwar motata kyauta ko don zirga-zirgar school.Har kuka seda tayi min don murna,tana ta godiya da shima triplets albarqa.

      ****
Rayuwa ta mik'a,Mahmood na musamman ya samo min 'yan aikin da zasu dunga kula da triplets,har makaranta suke bina se su tsaya awaje harna fito lectures,sannan na karbesu na basu mama.watanninsu hudu-hudu da haihuwa amma idan ka gansu zakace sun kai 9months ne sabida yadda sukai bulbul dasu da wani irin k'yau sabida wadatacciyar kulawa da suke samu daga iyayensu da kakanninsu,kai infact kowa nason 'yan ukuna,babu wanda ze gansu beyi sha'awarsu ba.

       Abangaren Mubeen kuwa,tuni ya manta da batun wata Zahra don Hanan ta zage damtse akan nada tana nuna masa tsantsar soyayya da kuma kulawa wanda ya zarce nada.wani irin soyayyace yake wa Hauwa'u Jiddah ayanxu wanda ko kadan beji hakan ba alokacin da yake tare da Zahra.Anan ya gane kuma ya tabbatar wa Kansa da cewar lallai _*SO_* na hakikanin gaskiya kwara _*DAYA_* ce tak!.kuma shi yakewa Hanan dinsa.

      Bangaren Suhaileedar suma ba'a barsu abaya ba don rayuwar auransu mah abar kwatance ne,haihuwarta de shiru tukunna because planning sukai don ta samu nutsuwar karatunta wanda watanni kalilan ne ya rage mata ta kammala final year dinta.Tuni Leedar da Fresh suka soma bautar kasarsu ah federal high court dake nan zariar wadda justice ne ya shige musu gaba har suka Samu aka barsu anan,da zarar sun gama kuma zasuje law school na shekara guda ah Lagos before they will be call to bar.

   *****

      _*BAYAN SHEKARU UKU*_

  Tuni Leedar suka soma aiki ah babban kotuna,shi Leedar an basshi ne anan federal high court tanan Zariar,ayayin da shi kuma Fresh akayi posting nashi ah can supreme court dake Abuja,ayanxu haka sunyi aure da Ashwairiyyarsa har tana mah dauke da juna biyu.ita kuwa Suhaima tana da d'a dan shekara daya meh sunan babansu leedar wato Ahmad,ana kiransa da 'Ammur'.

    Fadima kuma tana dauke da tsohon ciki,haihuwa yau ko gobe,su triplets an girma sae uban wayau.Arzikin Mahmood se dada bunkasa take,Dr.Shamsu tsufa ta soma kamashi don haka yayi ritaya,seya mik'awa Mubarak mukaminsa.Ayanxu Mubeen ya koma _*Chief medical director Mubarak MUSTAPHA NAKOWA*_.

     Kowa na tattalin matansa da 'ya'yansa,rayuwa dukkaninsu suke abar kwantace da sha'awa.Zancen jinns kuma babu labarinsu,babu wanda yafi karfin ubangiji sede idan baka kai kukanka gareshi ba.Itama Rukky tayi auranta.Usee kuwa Bayan ya kammala master dinsa,ya sami aiki ah 'GT bank' don accountancy ya karanta.dama suna soyayyarsu aboye da Hafeezah yar gidan baba Mu'azzam har asirinsu ya toni,bayan yayi settledown se aka daura musu aure gaba daya har Afreen da Arham dinta.ita kuwa auta Rafi'ah ita kadaice ta rage don ss2 mah take ahalin yanzu.

      _*Tammat bihamdulillahi! anan na kawo k'arshen littafina SHIN SO DAYA NE?(Mijin kaddarata),mijin kaddararta ya zame mata alheri.*_

_*ba yawan litattafi shine fadakarwa ba,no sakon ciki kawai akeda buqata.wasu darussa kuka tsinta aciki?*_

_*Da fari de ku rage yiwa mutane wulaqanci sabida baku san baiwar da Allah yayiwa wannan ba,haka kuma baku san abinda ya taka ba,shi din mutum ne,aljan ne? Ko kuma wani jinsin daban? Ga example nan na abinda ya sami Rukky lema,ta wulaqanta samari Ashe abinda bata sani ba aljanu ne,su kuma suka shiga jikinta don daukar fansa,suka dunga cutar da ita ta hanyar sanyata aikata miyagun ababe*_

*sannan kuma amatsayinku na musulmai ku koyi yafiya,ga example nan ga Suhaima Sa'ad tana da riko da kuma kafiya wanda hakan ita kanta ya cutar da ita da shi kuma Leedar,if not becuz of Fadima sa'ad toh kuwa da basu kai inda suke ba ayau,ita kuwa taimako tayi wanda shima ina son kuyi koyi da taimakon,gashi adalilin hakan Allah ya kaddara auranta da Mahmood wanda daga baya auran ya zamo mata alheri.*_

_*Abu mafi Muhimmanci wanda nafi son kuyi koyi dashi shine,karbar kaddara meh k'yau ko mara kyau, don Allah bakuji Mubarak ya birgeku ba? Muna ta tsammanin za'ai tashin hankali ba kadan ba,amma se gashi ya shayar damu madarar mamaki.... Muma Allah ya sanya muci jarabobin ubangiji,wanda yake kan mana,wadda yayi mana da kuma wanda ze mana nan gaba... Amin Yah Allah!!!

   Kuskuren dake cikin littafin nan Allah ka gafarta min,alherin dake cikinsa kuma Allah ka tabbatar min dashi,Allah ka albarkaci wanann farkon littafin nawa,Allah kasa na fadakar kuma na isar da sakon dana dade ina son isarwa.... Allahumma amin. 👏

      Ku kasance dani acikin sabon littafina wanda ze fito nan gaba meh suna _*HIBBATULLAH (KYAUTA DAGA ALLAH)*_  find out about diz book Hibbatullah,karku sake abaku labari!!

    I nid ur comments,idan kin san baki taba comment ba toh don Allah yau ki fito kiyi!!!

Akullum kofata abude take na karban corrections da korafi.ku tuntunbeni tanan don korafi _*07065481260*_

      Nagode....

*HAFNAN💞*
*💘SHIN SO DAYA NE?💝*

https://mobile.facebook.com/Intelligent-Writers-Association-1194933670662901/

          *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION📖✍*
Chapter 5 · 0% Book details