← Book details Shin So Daya Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 26

Sashe 15

Shin So Daya Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

       "Haba Mahmood wannan wani iri xance ne kake yi wai an fasa xuwa reception? Kasan fa abokanka baza suji dadi ba don ba k'aramin kudi suka barnatar ba....... "

Mami ce ke wannan maganar alokacin da 'yarta Afreen yayar Hafeezah ke sak'ala mata abin wuya da 'yan kunne.

    Mahmood dake tsaye da hularsa ahannu yace"Mum Fadimarce bata jindadi,she's sick........ "

Akid'ime ta mik'e tana fadin"What?? Bata da lafiya? Meke damunta??

     "Zazzab'i ce,pls kada ki d'aga hankalinki Mami dama tun acan gidansu ne ta soma rashin lafiyar amma yanzu da sauki,zafin jiki ne da dan ciwon kai kawai...... "

Saukar da ajiyar xuciya Mami tayi,kana tace"Mahmood ina ganin kawai ka kaita asibiti Doc.ya dubata...... "

      Cike da faduwar gaba yace"A'ah Mami ba sae an kaita asibiti ba,nace miki da sauki kije mah ki dubata da kanki ki gani...... "

Kafin ya sake magana tayi wuf! ta fice,Afreen da Hafeezah dake tsantsara makeup suka take mata baya.

    Shi kuwa Mahmood ajiyar xuciya ya sauke,ahankali ya furta"Ya salam! Wannan wani irin aure ne nayi? Wani irin tashin hankali da bala'i ne nake nemar jajibowa rayuwata?"

Ficewa yayi daga dakin,ya nufi waje,Su Ash na ganinsa suka mik'e,so take ta masa magana amma sae kuma taga ya daga mata hannu yayi gaba da sauri-sauri.Da hanzari Ash sukayi ciki gabanta na meh cigaba da dukan tara-tara.tabbas tasan wani abin ne ya faru don yadda taga Mahmood ya fita babu walwala akan fuskarsa.Toh koma meye ya faru Fatin ta birgeta,don basu ji wata hayaniyarsu ba,komai silently sukayi shi.

    **
Ina ganin ficewarsa naja jikina dakyar na xauna agefen gado da k'arfi tare da rik'e kaina dake barazanar fashewa don azabar ciwon kai.Hawayena sun kafe sunki zuba,abubuwan daya faru yanxu tsakanina da Engr. sun girmi k'wak'walwata don so nake nayi tunani da kuma nazarin kalamansa amma brain dina ya gaza yin hakan,k'wak'walwar tawa ta kasa bani damar tunanin komai.

     Ina cikin wannan halin ne naji muryar Mamin Hafeezah tun kan ta k'araso dakin tana fadin"Fadima d'iyata kina ina? "

Axuciyata nace"Ban gane ina ina ba? ya wuce dakin da kuka saukeni....? "

   Ganinta nayi ta shigo arud'e tare dasu Hafeezah biye da ita,sae ayanzu hankalina ya tashi kar de ace sunga fitar Engr. daga cikin d'akina??

    "Fadima yah kike jin jikin naki yanxu da sauki de koh? Idan babu tun wuri muje asibiti... "

Sae ayanzu hankalina ya dan kwanta ganin ba abinda nake tunani akai bane,kafin nayi magana naji sallamarsu Ash,biye dasu Anty Hajaar ce dasu Mama Jamila wanda ga dukkan alamu dawowarsu kenan.

    "A'ah kaina ne kawai ke ciwo Mami.... " na bata amsa cikin sanyin murya.

Tace"Toh bari na kawo miki maganin ciwon kan.... "

    Da sauri nace"A'ah Mami karki damu akwai ah purse dina.... "

Da hanzari na dauko purse din na ballo paracetamol,na dibi dan ruwa ah jug na hadiye maganin.Sae sannu ake ta min.Su mama Jamila mah sae duk suka ji ba dadi da kuma tausayina,duk aganinsu zazzabin bankwana dasu nake don lafiyata qalau sae yanxu dana soma jin jikina ba dadi.

    So nake nayiwa Ash wasu yan tambayoyi amma presence din su mama jamila da dangin mijina ya hanani k'eb'ewa da ita.Agaskia naga gata sosae awurin dangin mijin,nan da nan suke tayi dani kamar wata kwai da ba'a son ta fashe.

    Ina ke miki ciwo? Meh kike son kici?duk tambayoyin kenan wanda rana ta farko kenan dana ji na soma qaunar wannan auren.

Amma shi mijin nawa ina yake ne da har yanxu banga ko inuwarsa ba?

       **
Shi kuwa Mahmood yana fita,sae da aka kai ruwa rana kafin abokansa su haqura da xancen reception din.

   Ce musu yayi"Idan ta kudin da kuka barnatar ne shine kuke jinsa ajiki,toh kuyi haquri xan biyaku amma ni lafiyar matata ya fiye min komai...... "

Sae kuma suka ji duk jikinsu yayi sanyi da maganarsa.Haka de kowa ya kama gabansa duk rai babu dadi.k'iran wasu abokansu sukayi wa'enda suke venue din already suka sanar dasu cewar an fasa,Suma din sunyi d'an korafi amma da sukaji dalili se kuma suka dan sassauta. Shima Mahmood din wucewa gidansa yayi dake 'court road' don baze iya sake komawa cikin gidan ba.Gobe mah sae dare ze taho d'aukarta,don zasuyi kusan sati uku akano kafin su koma Zaria.

      Washegari wajen qarfe goma akayi walima acikin filin gidan,ba wasu jama'an Kirki ne suka zo ba kamar namu ba,kuma ba laifi malamar tayi nasiha meh ratsa xuciya wanda nayi kuka sosae.

Itama Suhaima anata b'angaren,qarfe goma akayi walima ah k'ayatacciyar filin gidan,ana gamawa direct akayi da ita b'angaren da xata zauna,sannan jama'a suka watse,tayi kuka sosae sanda kawayenta da wasu mamamninta suka zo wucewa wa'enda suka kwana.Dakyar ta bari suka wuce tana kuka wasu mah suna kuka.Yanzu ya rage ita kadai acikin dakinta,sae angonta da xata jira.

    Su Mama Jamila ne suke ce min zasu wuce,ai kuwa kuka na sakar musu ina cewa nima binsu xanyi.

Mama Sadiya ce tace"Yau ga sakarya,Yo! ai wannan itace ake kira da auren ai,gashi mun kawoki gidan mijinki inda kike ta mararin xuwa..... kinga ni cika min gyale..... "

    Haka su Mama Sadiya mah suka min,suka tureni suka fice har su Ash. Sae kuka nake wiwi kamar wata k'armar yarinya,su Mami kuwa sae aikin rarrashina suke.

Sae bayan isha'i akace min nazo mu tafi ga angona ya taho daukata,mamaki nake tayi wai ace da daddaran nan ne xamu kama hanyar Zaria? Kamar na tambayi su mami ko Zariar ce zamu tafi da daddaran nan amma sae naji na kasa.

     Falon Baba kamar yadda naji ake k'iran mahaifinsu Hafeezah aka kaini,anan naga angon nawa Xaune akasa yana sauraron jawabin Baba.

Kun san wanene mijin nawa?? Its still Engr. Mahmood Mustapha dai nake gani zaune agabana,sae ayanzu na tabbatar da cewar Yes! shi din ne de mijina.

     Tuni naji wani irin tashin hankali ya min sallama,taya akai ya sami aurena? meh yayi wa mahaifina har ya bashi aurena? Dama ze iya cin amanar Mubarak ban sani ba? Inasu mummy da sauran kannansa don ga dukkan alamu ya nuna cewar basu da masaniyar auren,kamar b'oye musu yayi,sannan kuma su waye Baba Mu'azzam da kuma Mamin Hafeezah agareshi? Anya ba hayar iyaye yayi ba  don su tsaya masa akan wannan aure ba kuwa?

    Wani murmushin takaici nayi ina meh raya wasu al'amura araina,ni kadai kurum nasan tashin hankalin da zan haifar muddin muka sanya kafa muka bar nan gidan.Ni kadai nasan tanadin dana yiwa Engr. Mahmood bayan ya gama labarta min dalilinsa na auren *'BUDURWAR KANINSA'*..................... 📝

A/N
Tofa my people mun fa iso gun.... Wani kudiri ne kuma ke ah cikin ran Fadima? Meh take shirin yiwa Engr. Mahmood? Ku dai biyoni.

     *IT'S HAFNAN*

*💘SHIN SO DAYA NE?*

      *MALLAKAR:HAFSAT ALMUSTAPHA*

       *WATPADD:HAFNANCY💞*

        *IG:Hafsy____mustee*

                     ✨✨

*KASHI NA BIYU:RIKICIN K'ARSHE*

           🌼BABI NA SHIDDA🌼

    *page 15-18*

         Can de na cije na sanya 'yar yatsa na sharce hawayen da har xuwa wannan lokacin sunki daina zuba,sae mah dad'a gangarowa suke kamar ana korosu ko kuma nace tamk'ar ruwan famfo.

"Brother inlaw har kayi round up na labarinka banji ka ambaci kalmar *'NAKOWA'* ba wanda abinda nafi k'osawar naji inda ka sami wannan sunan kenan.... " Na kafeshi da jikakkun idanuwana ina meh jiran naji bayanin da ze biyo baya.

     Saukar da wata wahalalliyar ajiyar xuciya naji yayi,kana yace"Fadima da fari dai don Allah ina son kiyi cancelling wannan *'Brother inlaw'* din da kike k'irana da ita,pls stop it banaso,am now ur husband so pls kindly upgrade my name to a romantic one,I want to feel being love again..... "

Wata uwar harara na watsa matsa,amsa nayi niyyar bashi amma kuma se na tuna cewar ban gama jin duk abinda nakeson naji daga gareshi ba,don haka se nayi ladab tare da maida wuk'ar.

     "Naji dear nah daga yau na sauya maka suna .... " na fad'a in a very romantic way.Har cikin xuciyarsa yaji dadin wannan sunar,ji yayi kamar Zeeynsa ce ta fada masa hakan don haka take k'iransa da *'Dear nah'*.

Ni kuwa da gangan nace *'Dear nah'* don na sosa masa xuciya yaji kamar Zaynab din ce agabansa.

    Axuciyata nace"Kaji dan malohon har ya wani susuce don na k'irashi kawai da 'Dear nah',lallai na yadda mace de shed'aniyace,ko shaid'an din mah yana Sara mata,tasan ta yadda zatayi ta zautar da d'a namiji,kissa da kisissina da duk wani salon yaudara duk atafin hannun mace suke...... "

Ji nayi ya katse min tunanina,yace"Nakowa de da kike taji ana fada family name dinmu ne,tun asali mahaifinmu ne ya sami wannan sunan daga bakin jama'a,sabida shi din mutumin mutane ne,kowa nasa ne,haka kuma yana da tausayi da kuma taimakon na k'asa dashi,dalilin daya saka mutane ke k'iransa da *'NAKOWA'* kenan,ba dukanmu muke amfani da sunan ba,ina daya daga cikin wa'enda basa amfani da sunan acikinmu,shima Mubarak din baya amfani da ita,we're juz bearing *'Mustapha'*,ta siyasa na tambayi Mubarak ko ya tab'a fad'a miki family name dinmu? Sae yace wallahi be tab'a ba,so yake idan yazo gabatar da Kansa awajen mutanenki,sae asannan ne ze bada cikakken sunansa,sosae nayi murna da hakan da kuma ganin wautarsa,shiyasa na bada wannan sunan awajen mutanenki don nasan tabbas bazakiyi saurin d'agowa ba....... "

     Tafa hannaye na soma yi kamar wata 'yar coci,shi kuwa kallo ya bini dashi,k'wayar idanuwan nan nasa dauke suke da tsananin tsoron actions din da xanyi taking.

Nace"Wow!wow!bravo!!... so smart & intelligent being.... Hmm! Nakowa's family..... "

     Sake maimaita sunan nayi cike da alhini"Nakowa's family........ "
Chapter 15 · 0% Book details