Sashe 9
Sanadin Boko Part 3 complete Hausa Novel · about 6 min read
Allahu, haka nan da dare suna tare da hashim yana sake fada masa cewa "Don Allah in sunje kada ya bada wata kofa da Za a gano yarinyar nan ciki tayi" hashim yace Haba nawa, Insha Allahu komai zai zo da sauki, ka kwantar da hnkalinka, babu wanda zai fahimci komai, Tunda yaya umar ya dawo daga kano ya sanar da baba zuwan baki, don haka baba yace ya kira masa Amininsa Malam garba da malam mamman. suna zuwa ya shaida musu komai,suka ce To insha Allah goben bazasuyi nisa ba, sannan sukayi masa murna da dawowar yar'sa HAFsat.Sun shawarta a amshi bakin A shagon gdan malam garba ,don yana da girma,don haka tun ranar yasa ya'yansa su gyara shi,umar kuwa kaji ya siyo da cefane akayi sa'a matarsa murja tana 'yan karance2 ltattafai don haka taiya grki. ya siyo lemuka kaloli aka zuba a ckin frdge.tun safe Babah ta kimtsa baba,yanxun ma yakan dan kokarta wanka da kanshi tun baya n da akaga hafsa ta fito masa da kayan sallar da umaryayi masa lkcn yana cikin ciwo bai sasu ba, yar ciki da malum malum yasaka an shimfida manya manyan tabarmi. umar yakawo chines carpetdinshi aka shimfida. Babah kuwa harda turaren wuta ta zuba a kasko tace akai shagon da za a sauki baki,Tun asubahi Abbkr ya rbuta txt ga baffa sa'adu, bayan gaisuwa ta girmamawa yace"Baffa ina fatan zakuyi hkri da yanda zaku samu gdansu hafsa, ina nufin talakawane.Da fatan wannan ba zai zama matsala ba,ka yafeni innayi rashn kunya" murmushi baffa yayi lkcn da ya karanta sakon,yayi kiran layin Abbkr. ckin grmamawa ya dauka tare da gaishe shi ,Baffa yace "Hamma kada ka samu damuwa, talaka da mai kudi duk dayane a gurn Allah,in talaka yafi mai kudi tsoransa ma to yafi mAi kudi agurinsa, Lura da cewa kudi ba komai bane face jarabta,duk da mafi rnjaye cikin zurarmu masu kudine amma muna da talakawan,so kada kadamu" Abbkr yace, Na gode BaffA Allah yakai ku lpia ya dawo da ku lpia" shi kuma yace ameen, shi yasa yake son baffa sa adu akwai saukin kai ba irinsu Baffa magajiba. Hashim yazosunyi sallama a inda ya sake sanar da shi damuwarsa, bayason suji cewa tayi ciki, ko ta bar gda,Hashim yace kada ka damu" tun da suka tafi yake cike da fargaba,tafiyarmaitsawo ce tsakanin yola zuwa kd. duk da sammakon da suka doka sai kusan mmagrb suka iso, don haka baFfa sa'adu yace da hashim bari ya kira amininsa dake zaune kd don su sauka gurinsa. washe gari sai su shiga gdan da suka zo,Hashim yace to. A nan take baffa ya kira abokinsa, basu samu matsalaba don yace gashi nan zai zo ya taho dasu da kansa. direba ya jawo shi har zuwa by-pass,shi ne ya gano su dai dai inda yace su tsaya. baffa da abokinsa sunyi murna da ganin juna,don sunfi shekara goma basu hadu ba sai dai waya sbd yanayin aikin kowannensu, Tare suka yi karatu a jami'a (ABU) a gdan shi da ke makarfi road ya saukesu a sashin baki, umar ya kira HAshim yace to "to yanzu ya zamuyi da abincinku? ko ka sanar daniunguwar da kuke sai na kawo maku"Hashim yace makarfi road dai naji ance amma bari in tmbyi yaran gda ya fada wa su baffa sai baffa yace.To ba laifi, in ankawo din dama su nan ba su san da zuwanmu ba,Baffa ya sanar da abokinsa sai yace haba dai su barshi yanzunnan za a yo musu take away, Yace a a bari dai su karboan nan take hashim tare da direban gdan suka nufi layinda hashim ya fada masa ashe babu nisa, umar ya fito suka gaisa,sannan ya fito musu da kulolin tare da samiru har da kayan shaye2 marmari masu dan dano, Baffa magaji yace ashe babu nisa da nan?sai da sukayi sallah sannan suka zauna zaman cin abncin. duk da babu wanda ya furta koMai amma kowa ya yaba wannan sauka tare da dadinn grkin, sunci sunyi kat har sun rage. nan gdan ma matar gdan ta gabatar musu da ciye ciye, sun dai dan taba sannan yace hashim yaje gdan dansa munir ya hada shi da direba yace ya kaishi shi can. sannan su baffa su ka zauna zauna zaman hira. inda abokin baffan yace sai kaji rasuwar 'ya'yanka ko? baffa yace suwa? su munir? yace a'a su bashir, banayi maka txt ba? baffa yace subhanallah, wlh ban ji ba,banga kuma txt ba duk tsawon lkcn nan ,baka ga banyi maka ta'aziya ba,tun yaushe ne? yace sun kusa shekara 2 baffa yace Allah ya jikansu hadari ne? yace a'a kasan yaran nan da rashin jin mgna can ne a malesia gurin karatu suka yi ri gima suka harbi junansu,yanzu saidai munir kadai, baffa yace auzubillah Allah ya yafe musu,mukuma ya kyautata tamu. Daddy ya ce Amin, Baffa ya ce, "Shi yasa fa nafi son mu dinga barin yaranmu suna karatu a gabanmu, saboda irin wadannan matsaloli shaye-shaye da harbe-harbe bashi da amfani gurin matasa, ba 'afi mu jami'oi ba, amma sai mu dage mu dinga raina namu, mu daukesu mu fita da su ba maisa muna ido a kansu, mu tura musu kudi, kuruciya tana dibansu, dole ne su ringa sheka ayarsu san ransu." Dady ya ce, "Nima sai yanzu na gane haka, kaga shima Munnir din gurin bin matanshi yanzu haka yana fama da (HIV/AIDS), matan ne kawai na tsira da su." Baffa ya ce, "Allah ya kyauta. Amma ya kamata mu farka, boko tana da kyau matuka, amma mu daina sakin 'ya'yanmu sakaka saboda tana da nata illolin, mu tsaya mu gyara skul dinmu na gida, kuma mu bar 'ya'yanmu su yi karatunsu a nan a gaban mu. Haka zai basu damar ci gaba da karatun addininsu, muna yin wani kuskure." Dady ya ce, "Wane iri?" Baffa ya ce, "Muna fifita boko kan na Islamiyya." Baffa Magaji ya ce, "Sosai kuwa, in ka yi la'akari irin kudin da muke kashe wa karatun boko, Islamiyya bama kashe mata, duk da cewa kudin Islamiyyar baifi kudin takardun Bokon ba, sai muke kyashin biya." Baffa ya ce, "Kuma in munyi kokari sunyi wannan 'yar saukar ta zamani shikenan sun gama, maimakon nan ma mu dafa musu su ci gaba."Dady ya ce, "Um!!! ai nayi kuskure Sa'adu sosai, don kuwa Bokon zalla yarana suka yi, sam ban damu suje Islamiyya ba." "Kash!!!" Inji Baffa Magaji, "Kayi kuskure, Allah fa baya turo mu duniya mu yi boko bane, ya turo mune dan mu bauta masa, to baku nemi ilmin bauta masa din ba bare kusan yadda zaku bauta masa din, don Allah kayi kokari har kai kanka ka shiga Islamiyyar manya." Baffa ya kara da cewa, "Ubangiji ya umurcemu da mu kare kanmu da Iyalanmu daga wata wuta, to Basu san Allah ba, ba ka koyar da su yanda zasu bauta masa ba, kenan kare su daga wannan wutar ba. Wadda aka ce makamashinta mutane ne da duwatsu." Haka dai sukai ta masa fatawa har yace ya gane kuma zai gyara sosai, zan dauki malami harda ita Mominsu ana koya mana. Baffa Magaji ya ce, "Da kuwa ka kyauta."Dady ya ce, "Sa'adu danka ne zai yi auren?" Ya ce, "Eh dan kanina ne, suka hadu da ita a Kano tana Makaranta." Dady ya ce, "Yaushe kuka soma auren waje?" Baffa ya yi dariya ya ce, "Wannan ne karo na farko." Dady ya ce, "Lallai to, shi wannan dan gurinka ne naga kuna kama?" Ya ce, "Hashim dana ne, shi tuni yana da Iyalansa harda 'ya'yanshi." Dady ya ce, "Lallai kaji dadi, nima dana bar wadan can sunyi aure yanda suka nuna min suna son auren, aida tuni ina da jikokina., to me zai hana ga yara nan cikin 'ya'yanka Sa'adu a samu wani ya duba?" Baffa ya ce, "Ai kusan duk wadanda suka isa auren suna da matansu, sai dai nan gaba in Allah yasa da rabo."