← Book details Sanadin Boko Part 3 complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 19

Sashe 5

Sanadin Boko Part 3 complete Hausa Novel · about 8 min read

Sanadin Boko 3-02 Posted by ANaM Dorayi on 10:53 PM, 26-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Hannuwanta a sama hawaye na sauka a kan kumatunta. Lallai duk wanda ya ganta ya san tana cikin damuwa. Maman rahama tana gefe kan tabarma tana bacci tamkar yashiga yaga me tak ma kuka? Menene matsalar ta? Ba shi da mai bashi amsa, haka ya cigaba da tsayuwa yana kalonta har ta gama ta jin gina da bango, fiskarta na kalon saitin window din. Da zata kula sosai zata hangoshi, amma batayi tunanin da mitinin da zai fito cikin sulisin daren ya zi ya tsaya ba. Yana kalon ta, tadago ido sama alamun tana tunani, bakinta kuwa yana motsi, ga alamu istigifari takeyi. Wayarta tana gefenta, ya koma ya jin gina da bango, ya curo wayarshi yana karanta sakonta. Nan take ya rubuta karya kike bakya sona, kuma daka ki kara min tex. Ni kuma bana sonki, ba zan aureki ba. Da ya tura sai ya koma leketa, da sauri ta dauki wayar, ganin labar shi tayi dan mur mushi, amma da ta gama karanta dan sakon sai yaga ta toshe baki da da hannunta tana kuka tare da sake daga hannunta sama tana fada ma Allah. Ya jingina da bango tare da rintse ido. Hakika tana son shi, to me yasa ta fada mishi ita karuwa ce a gaban Hashim? Sam baiji takun sawo ba. Ya de idanun shi a hankali yana me fatan ace hafsa ce,ganin hashim yasa shi yin kame-kame don baya so su fahimci har yanzu yana sonta. Hashim yace, mr. Man ka amince haryanzu kana son Hafsa, kulun ina jin fitarka kana zuwa lekenta. Aure a gurinka yake in ba zaka saurari ainihin kaddarar da ta hau kanta ba, to ka amince muje gurin iyayenta don tautana batun aurenka. Abubakar ya nufi dakinshi yasan dare ne kila tana ji. Hashim ya biyo bayan shi suka zauna suna fiskantar juna Hashim yace, na fada maka Rahama ta fada muna komai. Ta tabatar muna fyade akayi mata. Yace, agaban Rahama akayi? Ni dai kawai ina sonta zan aureta. Sannan ina son kai ka rufa min wanan asirin, mubar shi a tataba aure, don Allah kada ka bari dangi suji zancen nan, amana na baka. Abu na gaba kuma muje gurin iyayenta kafin mu koma gida. Hashim yace, haba nawan, yaya ma ba zan rufa wanan asirin ba? Koda ban santaba ai zan rufa mata, balantana kaddara ce ta sameta. Zuwa washegari na kara samun sauki, har da wanka ina canja kaya. Wayar Rahama tayi kara, tace min tana zuwa, Sagir yana kiranta, tana zaton yana harabar asibiti. Nace, to. Su 3 ta samesu cike da murmushi tace, Abubakar jiki yayi kyau. Yace, wlh gashi ma an sallame ni. Hashin yace, Rahama dama muna so ne kiyi mana cikkaken kwatancen inda zamu samu iyayen Hafsa. Rahama tayi shuru tana dan nazari, can tace ni dai a kwatancen da tamun acikin labarin da tabani, ta ce mun a kaduna, sunan unguwarsu rigasa. Layi kuma ko abuja road tace min? Na dai manta. Sagir yace, ni anawa ganin Abubakar ka bari ta kara samun sauki sai aje gaba daya da ita. Hashin yace, shinema zaifi zuwa da sauki. Abubakar yace, a a, ina da nawa dalilin zaku fahinci nufina daga baya. Rahama abinda nake so kafin gobe ki dan tambayeta cikin dabaru muji koda sunan layinsu. Rahama tace to. Ina kwance da wayan rahama a hannuna ina kalon hotona, yawanci duk hotunan bikin ta ne tasa a ciki. Na tsaida ido na a kan hoton abubakar me yasa ban fada mashi gaskiyar lamarina ba?Me yasa nace mashi ni karuwa ce, alhalin nasan wanan mumunan sunan da na kira kaina dashi zai iya bina? Ko dayake inma ban fada mishiba zaiji a wani gurin, cewa nayi ciki na gudu, tunda babu wanda yasan cewa fyade akayi min. Wasuma zasu ce masa ni karuwa ce. Amma da yaji abakina fa? Ko da ya sake ji a wani gurin bazai ji komai ba. Rahama ta ka tsemin tunani da cewa, hafsat ki tuna min kwatancen layin ku, wai in kai shadad. Na dubeta banyi maki kwatancen layin mu ba? Tace, kince abuja road, nace Allah to ban san nace ba. Rahama tace, har sunan layin kika ce ko me? Gidan wanene? Atake layinmu ya bayyana a idona, ban san na furta gidan 12 layi na 3, wasu suce gidan yawa. Na kali Rahama ina tuno rayuwar da nayi a wanan gidan, ina kewar gidan ina burin in sake zuwa gidan. Rahama tace mai zai hana in kin sami sauki muje? Nayi kokarin in tare hawayena, amma ba zasu tsaya ba saboda girman bakin cikin dake zuciyata. Nace rahama lokacin zuwa na gida baiyi ba, tace saboda me? Na sha fada maki abaya sai na kama aiki ko na sami mijin aure. Rahama tace, yaushe har kika saki fuska bare ki samu mijin aure? Taci gaba. Ba ma wanan ba, me yasa kika cewa abubakar ke karuwa ce? Nace, Rahama duk wanda zai aureni sai ya nemi asalina, kuma na tabbata duk wanda yaje unguwarmu don neman labarina za a fada mishi na shiga duniyar karuwanci,nakuma tafi da cikin shege, wanene ma yasan munnir fyade yayi min? Bale ma a dan kare ni? Shiyasa na fadi haka. Rahama tace, kamata yayi ki bashi asalin labarin abinda ya faru yanda zai fahimta, in sha Allahu zaya taimaka miki. Nace nifa kinsan Allah rahama? Bana son amaimaita min na baya, naga babu wata hanya da zan kori Abubakar da ya wuce in fada mishi hakan dan ya rabu dani. Duk da yanzu ina na damar hakan. Na dubeta sosai yanzu bana jin kunyar in furta ina son Abubakar, don bansan ina sonsa ba sai yanzu da na koreshi. Rahama tace kila kiga ya dawo, amma in yazo kada ki kuma kuskuren da kikayi a baya. Nace, Rhama na rokonki dakada kimin karya don hankalina ya kwanta, na tabata ko Abubakar yana shaye shaye ba zai dawo gareni ba. Tuni na dangana dashi, tun ranar da na tura mashi wani sako da dadare, kin ga amasar da ya bani nan acikin wayata. Na sauke ajiyar zuciya tare da share wani hawaye da ya biyo kan karan hancina yayi min dan maimayi. Rahama na gane kuskurena da nasani nabi innata nasan ba zan tozarta ba, zasuyi hakuri dangin uwata zasu rikeni da ko na hadu da Abubakar bazanji komai ba. Lallai barin gaban iyaye matsala ce katuwa. Rahama tace, ita dama mace guri 3 yakamata ta kasance, in bata gidan ubanta to a sameta a dakin mijinta. Idanto ya kasance baki can to a sameki a kabari, ta cigaba da cewa, duk inda mace take a sameta a karkashin wani uba ko miji, ko wa, ko kani, ko daki. Idan aka sami mace bata kar kashin ko 1, lallai ba wanda zai ganta da kima ko daraja. Kare da doki suna iya kawo maki hari tunda ke yar kanki ce, don haka duk lokacin da Allah ya kawo maki miji to kiyi aure zafin da kika dauka kan maza ba inda zaya kaiki, tunda sune a bokan rayuwa.Rahama tayi wa abubakar text din kwatancen da na ambata cikin hiran mu don haka washegari suka dunguma suka nufi kaduna har da sagir inata yi wa rahama mitar sallama in likita yazo ta fada mishi saboda sagir na kashe kudi wanda a zatona shine me kashewa ta ce min in nutsu in warware tas,sun isa kaduna shekaru masu yawa bai tsaya a garin kaduna ba tun daya bar ta sai de ya wuce ta a mota tambaya suka yi aka nuna musu rigasa haka ma abuja road sai dai sun sha wahala da ta sama suka yi mamakon ta kasa sun shiga layi na ukusun tambaya gidan yawa amma babu shi sun zaga sun gaji har sun fita daga abuja road sun fada makarfi road Abubakar ya ce mu dai koma kan abuja raod din mu sake yin tambaya daga bisani suka yi tambaya a wani masallaci da ke layin na ukun bayan sun idar da sallah nan mutane suka basu shawaran suje ta kasa Ikon Allah suna shiga layi na uku Abubakar ya gane gidan su Hafsa domin tsawon shekaru gidan yana nan yanda yake baa kara komai ba saidema kara lalacewan da yayi suka tsaya kusa da gidan yara nata wasa a kofar gidan cikin kasa sagir yace kana da tabbacin cewa nan ne gidan yaya ma akayi ka sani abubakar yace nazo shekaru da dama bayan fitowar yarinya daga gidan yasa su yin shuru yar doguwa marar jiki tana sanye da doguwar riga ta farin yadi da kore kalar tutar nigeria gadukkan yan kaduna duk wanda ya ganshi yasan cewa yadi ne na makarantar primary ta gwamnati tana rataye da yar jaka ta buhu mai dauke da littattafanta na makaranta kafarta sanye cikin sandal na roba wanda igiyoyinsa suka ciccire,Abubakar gabanshi ya fadi, tamkar hafsat a shekarun baya. Yace yanmata zo mu tambaye ki mana. Ta tsaya nesa dasu, abubakar yace nan nan gidan su hafsat? Ta maimaita sunan hafsat? Yace, eh. Tayi shuru tana son tunano wacece hafsat a cikin gifan nan? Ta dubeshi karama ce? Yace, baba ce, suman mamanta inna ta zaro ido inna? Yace eh. Duk yan dakinsu suna da labarin hafsa yayarsu, duk da itace karama kwarai a lokacin da abubuwan suka faru ba zata mance da sunan hafsa ba. Sai dai kamanin hafsat sun bace mata. Inna kuwa ai uwarsu ce, wace babansu ya kora sanadin abin kunyar da akace hafsat tayi. Ta dubeshi tace, hafsat bata nan, hakama inna. Yace, ina suka je? Cikin kagara tace, nima ban sani ba. Inna dai tana funtuwa. Yace, to baba fa? Ta nuna gida da yatsa, yana ciki bashi da lafiya, sagir yasa baki. Kice masa yana da baki. Tace, saidaifa ku shiga, don baya iya fitowa. Hashim yace, to fada masa sai mu shiga. Tana juyawa, sagir yace, wanan yarinyar tana matukar kama da hafsa. Abubakar yace, donma baka santa tana karama ba, da cewa zakayi itace. Tafito tace, yace in shugo daku. Suka rufe mator suka bita. Lallai gidan yawa ta sunan nanshi inji sagir. Kansu a kasa saboda yawan matan gidan da yaransu, wasu kuma suna
Chapter 5 · 0% Book details