Sashe 14
Sanadin Boko Part 3 complete Hausa Novel · about 8 min read
Sanadin Boko 3-05 Posted by ANaM Dorayi on 05:56 PM, 28-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Abubakar ya zo gurin Rahma ya kawo mata katin biki da duk wani abu da zamu bukata, sai hotuna da yace ta bashi dan can dangin sun matsa a kawo hotuna saboda suna son kalanda da memo. Rahma ta kirani a wata ta ce na shirya zan rakata gidan Matar kwamishinan ilmi, ta ce pls na kure adaka saboda sutura itace mutum. Ban kawo komai a raina ba, na ci kwalliya na saka after dress akai, ita ce da kanta ta ja motar tare da yi mata tsiwar cewar har kin kware da zaki cire (L) din? Ta ce, "Hannuna ya fada kinsanni da karambani." Muka tsaya wani gidan hoto mai kyau, anan ta ce min, "Hoto zamu karba ki shigo." Naje wajen hoton muka shiga, Rahma ta je tai magana da wani mai hoto na ga suna magana amma ban san me suke cewa ba, na dai tsaya a ciki. Da ta zo na ce mata, "Ina hoton?" Sai ta ce, "Wai sun kone sai dai a sake wani." Ina zaune gefe aka yi mata wajen kala 5, ya nuna mata ta ce yayi. Ya ce to nifa? Ta ce, "A'a, Hafsa ai ita bata hoto." Ya ce, "To shike nan." Na ce, "In gani Rahma." Ta ce, a'a ba zan gani ba, muka zauna zaman jiran karba, akai editin dinshi na ce, ka wanke mai kyau sosai fa. Muka karba muka fito. Muna hanya na ce, "Ina gidan Kwamishinan?" Ta ce, "Daman hoto ne, nasan idan nace miki ki raka ni ba zaki ba." Na ja tsaki tare da cewa, "To kai ni gida." Bayan la'asar lis ina duba wani littafin masu fasaha wanda yake burgeni na Ikilima, Shadad na gidan Mama na tura shi dan in nutsu ina son in samu wani abu da zan karu da shi cikin halayen Ikilima. Duk da ciki-ciki ya yi sallamar sai da kunnena ya dauko daddadar muryarsa, hannunsa rike da Shadad, na dan kauda kaina na ci gaba da duba littafin dun da na kasa fahimtar komai a cikinsa. Shadad ya rugo yana cewa, "Aunty ga Uncle." Na ture shi tare da cewa, "Waye haka? Da Allah ni matsa can." Ya bata fuska, "Aunty kin ganshi nan fa." Don kada Shadad ya fahimci wani abu sai na ce, "Sannu da zuwa." Bai amsaba sai ya bata fuska tare da tabe baki, "Na zo ne kawai in ganki, tunda kina lafiya shikenan ni na tafi." Ban motsa daga inda nake ba na ce, "A gaishe su."Ya ciro kudi ya bawa Shadad, "Je ka zauna sai na dawo." Ya ce, "In ka dawo zaka tafi da ni?" Ya ce, "Sai kayi hutu." Ya juya ya fita, na bishi da kallo hatta tafiyarshi ta lafiyayyun maza ne, komai nashi birgeni yake yi. Daidai soron ya juyo idanunmu suka kalli juna har ciki, ya zare nashi idanun ya kalli gabanshi, sannan ya bude kofar ya fita. Na lumshe ido tare da shakar kamshinsa, tsam! Na mike na nufi kofa ina leken shi, ya mike da nufin fita daga layin ina zaton ba da mota ya zoba, na bude kofar ina lekenshi har sai da na dena ganinshi. Shadad na samu yayi wada-wada da kudin da ya bashi, 'yan dari 2-2 ne guda goma, na kwashe su na koma daki na zauna bakin gado ina tunani, damuwa ta ban san zaman da zamu yi ba. Cikin kwanakin shagali na karatowa kuma karatuna na kara daukar zafi, don mun kusa mu fara Jarabawa.Rahma ke shirya komai na game da walima, ana gobe daurin aure na dawo Makaranta wujiga- wujiga, na iske gidana dam da jama'a. Rahma ce da makota har da dangin mijinta suna ta aiki, wasu na wankin naman kaji, wasu na wankin kayan miya. Turus! Na yi yayinda makota suka soma fadin ga AMARSU, guntun murmushi nayi tare da gaishe shi sannan na shige daki, a zuciyata na ce, "Kai su Rahma da karfin hali." Ita kuma sai hada murhu take yi. Ta zo daki ta sameni, "Don Allah kada ki nuna fushi ko wata alama da za'a gane da wata matsala." Na ce, "Wai ni duk ba wadannan ba, a ina kika samu kudin yin wannan shagalin?" Ta ce, "Daga taskar ango." Na ce, "Shagali, Allah ya baku sa'a."Dazu Inna ta kirani tace min tun jiya suna Kaduna ita da danginta, tace min ya kamata na taho." Rahma ta ce, "Mama ta ce gaskiya can ya kamata a tafi, to sai dai mu bar walimar sai ranar lahadi, ko me kika gani?" Na ce, "To ni dai gobe sammako zan yi." Kafin dare an gama suyar kaji an yi miya, duk ta ba wadanda suka tayata aiki. Da duku-duku muka gama shiri ni da Shadad, sai ga Rahma da direbansu, Mama ma ta shirya, Rahma ta ce, "A dibi naman da drink a tafi da su ko?" Na ce duk yanda ta gani, tunda kajin da yawa, sai ta debo sosai, goma daidai muna Kaduna.Allah Sarki Baaba! Ashe har anko suka fitar, gidan cike yake da mutane ban zaci ganin haka ba, ashe Baaba gayya ta yo, dakin Baba nan Inna ta sauka da danginta, na ji kunyar ganin 'yan uwanta, amma ganin basu nuna komai ba sai na saki jikina, suka gaisa da Mama, Baaba ta shigo muka gaisa, ta ce, "Ga fa abincin 'yan daurin aure can nasa a dafo shi a gidan wata mata da ke yin na kudi." Baaba ta ce, "Ko ko za'a sayo 'yan holokon nan ne da dan cokali na robar nan a zuzzuba a ciki?" Na ce, "Oho." Rahma ta mike, "Baaba kin tambayi wannan ita dake jin haushi sai kace wadda za'a yiwa auren dole? Bari inga abincini." Suka tafi. Inna ta ce da Mama, "Baiwar Allah nan tana kokari, Allah ya saka mata da alheri." Su Mama suka ce Amin. Rahma ta dawo tana cewa, "Abinci yayi kyau, ta zuba wadatattun kayan lambu, yanzu bari a dauko naman nan a zuba a kai, na bada kudin take away din." Nan suka zuba abincin da naman kaji, ga drinks, Innarmu ta ce, "To shi Babanku kinje kun gaisa?" Na ce, "A'a." Ta ce, "Yana dakin Malam Garba ki je." Nan na fita, Shadad ya biyoni na rike masa hannu, ina jin lokacin da wasu ke cewa, "Hala wannan shine dan nata?" Ban damu da in juya inga ko su waye ba, na fita. Mun gaida da Baba, ya dauki Shadad tare da cewa, "Muhammadun ne wannan?" Na ce, "Shine." Ya ce, "To Allah ya yi masa albarka." 'Yan daurin aure sun zo ance nan suka kwana gidan aminin waliyyinsa ko?" Na ce, "Eh." Duk da ban sani ba, ya ce, "To Hafsatu, ke dai ba kankanuwar yarinya ba ce, Allah ya kawomu lokacin auranki, don Allah kiyi hakuri ki zauna da Mijinki lafiya tare da ladabi da biyayya, ni dai in kin min haka kin gama min komai." Yayi mata nasiha sosai, ya ce, "To Alhamdulillah, Yayanki Umar shine ya sai miki gado da kujeru daidai karfinsa, Baabarku kuma ita ce ta sayi duk abinda aka dafa, sadakinshi da shi aka sai miki katifa da fuloli. Sai dai Innarki da tace ta zo da kudi sai kin zo za'a shawarceki, nima ta gefena dangi sun zo daga Maiduguri sun bani gudummawa dubu goma ce na ba Umar." Na ce, "Oh Allah! Mai rufawa bawa asiri, Allah ya saka da alheri." Ya ce, "Amin, Allah ya baku zaman lafiya." Na dawo gida na bar Shadad gurin Baba, Innarmu ta ce, "Ya miki bayanin komai ko?" Na ce, "Eh." Ta ce, "To ni nan gurina kawunanki da sauran dangi sun hada dubu hamsin, ni kuma nayi adashi na dauki na dubu sittin, sai na bada hamsin, goma kuwa na basu Ummi saboda anko da suka ce tunda Yayanki hidima ta masa yawa.Sannan ta ce, "Shi kuma Babansu Rabi'u (mijinta kenan) ya bada dubu hamsin, nan dubu dari da hamsin kenan gaba daya sai asan yadda za'a yi da su." Na ce, "Ni dai Inna duk yanda kuka yi daidai ne." Muryata ta soma rawa zanyi kuka, "Ban zaci zaku kula ni kumin wannan gatan ba, dan na riga na watsa muku kasa a ido." Kanwar Innarmu ta ce, "To komai ya wuce Hafsat." Innarmu ta ce, "Kayan kicin zaku je ke da Rahma kasuwa ku sayo yanzu tunda an ce ana gama daurin aure zaku wuce da kayanki." Na ce, "Da an sani ba'a sai kayan anan ba, don tafiya yola da kaya aiki ne, in naje can a siya." Inna ta ce suma sai da aka siya sannan suka zo, amma an ce su zo da motar dibar kaya, dan Umar ya fada ma angon cewa su zo da ita. Na ce, "To yanzun me za'a siyo?" Ta ce, "Ke kika san abinda ya kamata." Na ce, "Tab, to ni ai bani ma da komai tunda Karatu nake yi banyi tunanin auren nan kusa ba." Ta miko min kudin nace Rahma ta karba. Mun fito zamu tafi muka ga Sakina kanwata 'yar wajen Baaba nace ta zo mu tafi. Muka je a motar Rahma nan kasuwar bacci, na sai kayayyaki su TV da kayan kitchen duk na amfanina da su blender da sauransu. Mun kashe dubu chasa'in, ragowar kudn na sai kayan gara dan ma Inna ta yi cincin, dubulan da alkaki. Muka sai shinkafa buhu 2, taliya 3, semi 4 manyan galan na manja da na man gyada 2-2. Nan dai muka kashe kudi, sannan muka nufi gida. Mun samu ana loda kaya wai motar kaya zata yi gaba, don haka Rahma tace ma Yaya Umar ga wasu a saka a tafi da su. Ya ji dadin ganin garar da nayi ya ce, "Dama ita yake ta tunani ina zaya samu kudi ya saya?" Ni kam na shige gida guri tunda ya soma cika.Misalin karfe biyu aka daura aurenmu da Abubakar, lokacin da wata marokiya ta shigo tana rangada guda, jikina yayi sanyi lakwas, yau na zama matar aure, sai dai nayi missing din al'adunmu, kamar sa lalle, kamu, ko fulawa ba'a zana min ba bare gyaran kai. Na watsa ruwa na zo na zira Jallabiyyar cikin akwatin da mayafinta.