← Book details Sanadin Boko Part 3 complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 19

Sashe 6

Sanadin Boko Part 3 complete Hausa Novel · about 7 min read

wasu ayyukan. Sun dan gaisa da wadanda suke bakin hanyar zuwa dakin, yarinyar da ta shugo da tabarma ta shinfida musu a gefe suka zazzauna suna fuskantar tsohon. Yana kwance kan tsohuwar katifar shi, wadda ta lakume. Suka gaisa, dakin yayi shuru lokacin yarinyar ta kara dawowa da kwanan sha na silba mai dauke da ruwa ta dire masu. Baba yace, kai cema babarku ga baki. Itama ta shugo su gai sa. Baba yace, kin shaida su? Tace, a a yace samari daga ina? Abubakar ya zunguri sagir, nan take sagir yace."Baba mu baki ne daga Kano." Baba yace, "Kano gurin wa kenan?" Ya ce, "Ba za ka shaida mu ba, ni sunana Sagirn wannan kuma Abubakar. Sai kuma wannan Hashim." Sagir yayi dan shiru saboda tunanin ta inda zai fara maganar. Can ya ce, "Wato Baba za ku ji mamakin cewa mun zo neman auren Hafsat ne." Baba ya yunkura ya zauna wanda baisan lokacin da yayi hakan ba, domin in zai irin wannan zaman sai an kama shi. Ya ce, "Hafsatuna?" Hashim ya ce "Ita" A rude Baba ya ce, "A ina kuka ganta? Don Allah ku fada min, kun ganta ne?" Tausayi da kaunar tsohon ya ratsa zuciyar Abubakar, ya ce "kada ka damu Baba, Hafsat tana nan lafiya." Ya ce "Alhamdulillah, Allah yasa ba irin mafarkin da na saba yi bane, tare kuke da iata? Hashim ya ce "Ba mafarki bane Baba, kuma ba tare muke ba." Ya nuna Abubakar. "Ga mai sonta da Aure nan, mun zo ne mu sanar da kai magabatanmu za su zo. Sai dai matsalar da muke tunani kada su zo kuma wani ya basu labarin cewa ta bar gida. Kila sanadin hakan iyayen mu suki amincewa." Baba ya ce "Wannan ba matsala ba ce, in sha Allahu, Amma kafin nan ina son Hafsat ta zo gida, yarinya tafi daraja idan tana gaban mahaifanta."suka ce To Insha Allah za su kawota, ko kuma su tafi da wani ya ga inda take. Baaba ta ce, "Kai amma wannan abu ya yi dadi, amma ku jira wanta yanzu sai ku gaisa, batun zuwa kuwa nice zan biku, ko kuma muje tare da Umar wansu din." Suka ce A kira shi. Sagir ne ya dauki lambar, bugu daya ta shiga ya dauka tare da Sallama, Sagir ya amsa ya ce, "Mu baki ne daga Kano, gamu nan gurin Mahaifinku, zamu samu ganinka?" Ya ce, "Lafiya?" Sagir ya ce, "Lafiya lau." Umar ya ce, "To gani nan zuwa, zan shigo layin da fasinja." Sagir ya ce, "To."Suna zuwa kan layin Umar ya cema kwandastansa ya kara dasu shi zai shiga gida, ya basu hannu suka gaisa sannan ya yiwa Baba sannu da Jiki. Cikin doki Baba ya ce, "Jiki da sauki, sun zo ne da labari akan Hafsatuna, abin dadi har da mai son aurenta, gashi nan tsakiya." Da tsananin mamaki ya ce, "Da gaske kun ga Hafsa? Allahu Akbar!!! dama tana raye?" Sagir ya ce, "Tana raye." Umar ya ce, "Ikon Allah!" Baba ya yiwa Umar bayanin komai da yanda suka yi. Umar ya ce, "Baaba ki zauna ni zan je naga inda take kafin, in yaso kwaje daga baya." Baba ya ce, "Haka ma yayi Umar." Umar ya ce, "Shawarata anan ko za a ce bakin suje can Funtua wajen Inna a karbi auren?" Sai Baba ya ce, "Ba komai nan ma yayi Umar. Allah shine mai yanda ya so."Umar ya shiga motarsu, inda suka je gidanshi suka ci suka sha, sun huta sosai, sai karfe 5 suka ce zasu tafi. Abubakar ya kasa hakuri ya ce, "Yarinyar can tana kama da Hafsa." Umar ya ce, "Ummi, 'yar autarmu ce." Ya ce, "Masha Allah." Duk yaga sauran kannanta yanzun saura Inna, suna gidanma Umar ya kira wayarta, bayan sun gaisa ne yake fada mata cewa cewa Wadansu bayin Allah ne suka zo da labarin Hafsatu, cikinsu har da wanda zai aureta. Cikin tsananin mamaki ta ce, "Da gaske kake?" Ya ce, "Gasu nan ma." Ta ce, "Harda Hafsat din?" Ya ce, "A'a, zan dai bisu muje in ga gurin da take." Ta ce, "Ko zaku biyo mu je?" Ya ce, "Kada ki damu Innarmu ni kadai na isa, tunda gida zata dawo." Inna ta ce, "To."Biyar da rabi suka dauki hanyar Kano su 4 ne. Suna hira a nan Umar ya samu wadan su labaran game da Hafsat, nan ne ya ji cewa bata san sun zo ba, bata da lafiya don haka ya ce, "To in mun je ku bari in fara shiga."Kusan karfe 8 suka iso Kano, sai da suka yi Sallar Isha'i sannan suka isa gidansu Rahma. Tana ganin Umar ta gane dan'uwan Hafsa ne, saboda kama ta jini. Da sun ce a bari sai da safe a je gurinta, Umar ya ce shi kam yanzun yake son zuwa. Dole suka tafi, daga bakin kofa suka tsaya Umar ya shiga da sallama.Mama tana sallar Isha'i, ni kuma ina bakin gado. Ina jin a jikina tamkar wani bakon al'amari zai same ni. Muryar Yaya Umar ta katse ni, da sauri na dubi kofar, zumbur na mike tsaye jikina yana kyarma na ce da sauri, "Yaya Umar! Yaya Umar kai ne ko mafarki ne?" Ya yi murmushi, "Ni ne Hafsa." Na zuba masa ido, ya sake zama magidanci, ya tako ya rike hannuna, na ce, "Kai da wane ne? Wa yace maka ina nan?" Ya zaunar da ni a bakin gado ya ja kujera ya zauna dai dai lokacin da Mama ta idar da Sallah.Na ce, "Mama ga Yayana Umar." Ta juyo suka gaisa, su Sagirr suka shigo har da Abubakar. Shi na zuba ma ido tamkar wadda na warke makanta. Shi kuwa ya hade rai kamar wanda zai fadi sakon tashin bom. Mama kadai ya gaisar, bai kalli inda nike ba ya ci gaba da karanta wata takarda da aka lika a jikin bango, ta masu gargadin ciwon kanjamau. Hankalina ba ya tare da su, don haka ban san me suke tattaunawa ba, yau wane irin mafarki nake yi? Ga Yaya Umar ga Abubakar? Mutumin da na cire rai da sake ganin shi, ya dawo ne? Ko kuma daman yana nan? Ashe wai a fili nayi zancen, sai na ji Sagir ya ce, "Wa?" Na dube su cike da damuwa ina zare ido. Na kalli Abubakar, "Don Allah ku fadi min ina mafarki ne?" Sagir ya ce, "Hafsa mune muka zo da Umar." "Kun je gidanmu ne? Wa ya kaiku?"Nan take na mike don watsa ruwa na fito na jawo jakar Rahma na murza hoda. Ta ce, "Iye! Har da su hoda? Kina son birge Abubakar." Na ce, "Ina ruwana da shi?" Mama ta ce, "Sauki ya samu ta 'ki saka hoda? Har da kwalli radau kayanki." Na ce to. Sannan na ce Rahma ta dan hada min tea. Lokacin da Sagir ya isa masaukin nasu, ya same su suna karyawa, hira suke yi inda Umar ya basu labarin barin Hafsa gida, ya ce kowa ya sha mamakin faruwar matsalar saboda Hafsa nitsatstsiya ce, ko yawace- yawacen nan na 'yan mata bata yi, bata ma da kawaye, son bokonta ne yasa wannan saurayin ya yaudareta har ya kai ga yi mata ciki, kasan mata da karamar kwakwalwa, idan saurayi na kashe musu kudi babu wuya an yaudaresu. Hashim ya ce, "Labarin da Rahma ta bamu fyade yayi mata shi saurayin." Umar ya ce, "Ta yiwu haka ne, don lokacin da abun ya bayyana Babanmu bai kwantar da hankali an ji yadda lamuran suka faru ba, kawai ya kore su ne." Abubakar ya ce, "Ta bakin Umar ne mace idan tana son namiji ta hadu da Shaidani, to ba zata yi wuyar bada kai ba." Sagir ya ce, "To duk dai komai ya wuce. Allah ya tsare mana zuri'a kuma ya rabamu da rudin shaidan." Ameen ya Rabbi, suka amsa. Ran Abubakar fa a bace yake amma bai nuna ba, a nashi ganin ba wani fyade, ita dai dan tana son shine taje don sakarci ta bashi kanta, har saida yayi mata ciki sannan za tace yayi mata fyade, dan ta kare kanta ne kawai, wa ma yasan adadin kwanciyar da tayi da shi. Ya ja tsaki.Sun shigo ina shan tea, na ajiye ina kallon Yaya Umar na ce, "Ina kwananku?" Suka amsa amma ban da Abubakar wanda ke latsa wayarshi, a raina na ce, "Mutumin nan fa har yanzu bai huce ba." Na dubi Yaya Umar na ce, "Ina Baba da su Baaba?" Ya ce, "Suna nan...
Chapter 6 · 0% Book details