← Book details Sanadin Boko Part 3 complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 19

Sashe 17

Sanadin Boko Part 3 complete Hausa Novel · about 8 min read

Sanadin Boko 3-06 Posted by ANaM Dorayi on 05:57 PM, 28-Sep-15 Under: SANADIN BOKO yana cewa, ai munata yin waya dasu sagir, sun tabbar min kuna lfy, na tabe baki yace, to yaya kuke? Tace lfy, mungama shirya muku komai, gobe asubanci zamuyi gda, yace au, kuna nufin baxaku tsaya ayi budan kaiba? Tace ai mun gama budan kai tunda munkawoma ita. yace to nawa zan fansheta? Rahma tace mekenan? Nima na tashi zaune tare da kara matsowa, sannan na kara kanga kunnena, yace, toni kam bansan yadda zan muku bayaniba, amma zaifi kyau ku tsaya dan kar kubar mata abin gori, kunsan halinku dai mata, rahma tace, to zamu tsaya, sai daifa mu bamusan yanda kuke gabatar da al'adunkuba, sannan amarya bata da dinkakken kaya, yace meya hanata dinkawa? Kodai bata shirya aurenaba? Tunda tun asali bani takesoba? Rahma tace, wannan batun aiya wuce, don dama bata da wanda takeso, zuwankane kakoya mata soyyaya, yace rahma kenan! Ai ina zaton soyyayar da kawarki ta iya niban kai gurinba, amma dai ya wuce ta bakin naki, sannan kuma za'a kawo mata kayan sawa, mu nan garin dama haka ake kai kaya, don amare basa amfani da kayan akwatin sai dai ayi musu a gidajensu, rahma tace, hali keyin haka, mukam talakawa irinmu kuwa lefen muke amfani dashi, ta canza batun da cewa, ina angona? Yace mun saidashi, tace tabdi! Ba'a kake, da kunga gayyar kanawa, don Allah yana kusa banishi inji muryarsa kona samu nai bacci, ya saki daria, na lura kin shagwaba sagir dayawa, shiyasa yadamemu da tadinki, na sulale a hankali na kwanta, da alama bata fahimci abinda yake nufiba, suka gama surutunsu da mijinta sannan sukai sallama da hirar soyyayarsu, dare ya tsala, kowa na kwasar baccin gajia, amma niban dani sbd hakikanin gaskia kalaman abkr sun soki zuciyata, mutsu mutsu nane yatashi rahma, tace a hankali lfy? Nace rahma mekika fahimta da mgnr abkr? tace namefa? Na juyo da cewa, yace damacan bashi nake soba, sannan yace soyayyar dana sani shi baikai gurinba? Lkcn dakikace zuwanshine ya koyamin soyy, rahma tace, kinsan nifa bakoda yaushe nake zama nazarin mgn irin hakaba, amma ke mekika fahimta? Tace wlh rahma koyaya mutum yai zance nasan meyake nufi, inada wata baiwa tadaban akan karantar mutum, ko zolaya yayi ina gane manufarsa, nufin abkr damacan munnir nakeso bashiba, sannan na iya soyyayar da baikai gurinba, to sbd soyyaya nasakarwa munnir kaina har na samu ciki shiko bai taba hakanba, rahma tayi shiru itama ta fahimta, amma don kada na tashi hankalina agane inada damuwa sai tace, kada kiyi masa wani zato, ta yiwu ba nufinsa kenanba, (kai abkr na gasawa hafsa mgn gaskia, yan'uwa kuja mai kunne mana) nace hum! Rahma tuni na hararo irin zaman da zamuyi da abkr shiyasa nake gudun aurena, yanda na fahimci halinsa, shi mutum ne mai tausayi dason kyauta, sannan mai jajircewa ne akan abinda yakeso, wanda bai kaucema addini, sai dai kash! Yanada naci tare da mita idan an masa laifi, sannan baya bincike bare saurare, kinga kozansha wuyar zama dashi in nayi la'akari da irin halayen nan, sannan zai dinga jefamin mgn, hwy suka soma zubomin tare da sintiri afuskata, Rahma tace, duk wannan hasashen nakine, don haka kibar mummunan zato a kanku, kiyi fatan alheri, nace to Allah yaxaba mana mafi alheri, sai kusan assalatu sannan nasamu bacci ya daukeni, da safe karin kumallo mai kyau mukayi, kunun gyadane da lafiyayyen kosai, da kuma kayan tea gamai muradi.natashi nashiga wanka bayan mungama, kayan rahma nasaka cikin sabbabin kayanta, rahma tace bari tadan fita cikin gdan tagani, jim kadan tadawo tace, wai gaskia babban gdane, gasu da tarin zuri'a, nace hum! Allah yasa mudace, rahma tace amin, can saiga wasu yanmata 3, 2 manya, 1 karama, ina zaune bakin gado suka shigo har ciki, biyun sunyi kama da abkr, duk yanda akayi kannensane, duk suka tsuramin ido, bayan mun gaisa, su kuma sai mgn suke cikin fillanci harda daria, (nidai nagane gulma suke) karamar cikinsu ta matso kusa dani tana cewa cikin harshen turanci, aunty sunana ummi, wannan kuma sunanta rukayya, yayatace, wannan kuma sunanta husna, abokiyar wasanmuce, dukkanmu kannen hamma ne, nace to sannunku da zuwa, ta dubi sauran tana sauraron abinda suke cewa, sai naga tahade rai, sanna itama taci gaba dayi musu mgn cikin fillancin, abinda nake zargi ni suke kushewa ita kuma bahaka tasoba, saina samu kaina da tsarguwa, su 2 suka tashi suka fita suna daria, nace musu sai anjimanku, sukace to, ita kuma ummy tadawo kusa dani tazauna, tacemin hammansu yana sona da yawa, dan Allah na kula dashi, nayi yar daria nace to ngd ummy, kuma zanbi shawararki, sai naji yarinyar tashiga raina mai hankalin manya, tace kinyi kyaufa, anjima za'ayi budan kai nace, ya akeyi? Tace kubakwayine? Nace a'a, tace yanada kyau, zaku zaunane sai a bude fuskanki inkin rufe, anayi ana gada, daga nan sai dangi suyi fansa, nace mekenan? Tace kudine za'ayi ta zuba muku, sai kuma a kawo faute daga gidan amare, nace shikuma mene faute? Tace ba ankai muku suddajeba? Na tsura mata ido, mene suddaje? Tace kayan dangi mana, ba ankai mukuba? Nace eh, tace toshine suddaje din ai, nace to menene faute? Ina nufin me akeyi dashi? Tace kayane su kuloli dasu. Kaya dangin amarya suke badawa wasuma harda gado sukeyi, nace to, rahma tace in kuma mutum bai sanibafa? Tace ai duk zuri'armu sun sani, rahma nace abinda mukeyi acan zamuyi sai mubasu hkr muce bamusan sunayin hakaba, tace, ai baza'a damuba, tunda an sani cewa baku saniba, karfe 4 daidai lkcn gdan yacika dam kidan sarauta ke tashi, kai zuri'ar abkr akwai kyau, sunata shigowa kallona, ummi taje kiran da abkr yamata, don tuni sunyi waya yasan cewa tana gdan, ta shigo dauke da katuwar leda, tace anty canza kaya donga adda fadi nan sun iso, kuma nasan hamma da abokanshi ma sunata shiri, shine yace in baki kayan nan, muka bude nida rahma nace, kila dai a dinken yasiyo, rahma tace, daga gani don gasunan a ledarsu, nace Allah yasama to sumin daidai, daya leshine da aka hada da swis, dayan kuma leshine zalla, sai shadda doguwar riga taji aiki, sai atamfa, nace toni wanne zan saka? Rahma tace kisa leshin nan, ummi tace aunty kisa shaddar nan mana gata ja tunda keba fara bace, zakiyi kyau, nace rahma duba akwatii akwai takalmi ja cikin kayan can? Saiga ja takalmi gami da mayafi, ummi tace kiyi amfani da bakake, kuma hamma yanason jan abu ga mata, don in zai saya mana zani dole saikaga ja aciki, na sake yo wanka na zauna gaban madubi nadauki kwalliya, harsu ummi suna cewa gaskia nai kyau, na saka sarka da sauran tarkacen karau, suk su rahma da sakina kowa yayi kwalliya, zuwacan abokan wasansa suka shigo sunamin tsiya wai in fito, yan'uwana suka takamin baya muka nufi gurin. Katuwar darduma ce shimfide, tun kafin mu karaso na hangi hamma sanye da shadda blue mai kyau da tsada sai sheki take, gefenshi fadima ce wato kishiyata, tana sanye cikin wani yadi, tsananin kyan yadin ne yake bayyana tsadarsa, taci gwargwaro, ga gwala gwalai, gabana ya fadi don kyawunta ya wuce misali, ina isowa kanshinsu yadaki hancina, duk sai na jini na zama wata ga daini nan, donko nasan ko a kyau baxan kama kafa da itaba, muka kalli juna nida ita ido cikin ido sannan na dauke kaina na zauna, guda ta soma tashi, sai aka umarcemu da mu rufe fuskokinmu da kyau, duk muka rufe sai aka kira kannenshi wai su fara bude uwargda, rukayya ta bude fadi, mai guda tafarayi sannan danginta suka shiga zuba kudi, daganan saini, ummi ce ta bude fuskata nima, nima dai dangina sukadan watsamin abinda ke garesu, bandamu da kudin da aketa zuba musuba, musamman abkr don al'adace da addiniba, (inama ni suka bawa kudin nan) can kuma saiga iyayen fadi sun kawo faute wajen dangin abkr, kayan gado dan italy na kwali, da kuloli da sauransu, aka shiga sanarwa, rahma ta duko kusa dani tace ya za'ayi? Nafito musu da garar nace suma abasu, buhunan shinkafa talia, dasu dubulan da alkaki da yan samirun damukazo dasu, haka kuwa sukayi, basuce komaiba da aka basu, rahma tace suyi hkr bamusan yadda suke abubuwansuba shiyasa, nan naga anata raba kalandu zuwa jakunkuna da memo da jota, dadi sauransu, hotuna nake mamakin inda akasamu nawa, kamar tare muka dauka? To suna nufin tare muka dauka? Yana tsakiyarmu ya kwanta bayan fadima, nikuma na kwanta a bayanshi, dukkanmu muna daria. ina sanye da jallabiya, al'ajabi ya cikani, sai daf da magrib aka tashi, muka koma dakina, dama na kosa mu koma, na janyo daya daga ciki jakunkunan da akaba dangina nace, yaushe ne har mukai wannan hotunan ni hafsa? Rahma tai daria tace lkcn daxamuje gdan kwamishina, idan nace kizo muje baxuwa zakiyiba, shiyasa nahada baki da mai hotan yamiki baki saniba, computer kuma tatsara abubuwa, daman fuskarki kawai muke bukata kuma gashi munsamu, rahma tabude jakarta tace ga hotunan yanzu kigani, tabani na kalla, amma nace Allah ya isana amma, nace dubi yanda nayi acikinsu kamar wata yar aikinsu, badai shine yaji kuma ya ganiba inji rahma? Nace ga yanmatan nan kannenshi zasuyi rainin wayo, rahma tace, kedai tsakaninki da kowa mutunci, nace shima sai wani shareni yake, shiyasama da ana hotunan nan da danginsu ban cusa kainaba ciki, nayi zugum ina kallon fadima, kishinta nacin raina, nace rahma, fadima tana da kyau, ina zaton abkr yafi sonta, me kamar wannan mezai damu kansa dani kila ya aurenine don wata manufa, rahma ta mike cewa, saikiyi kuma, nikinga tafiyata zan sallah, gara ke hutu kike, saiki zauna kiyi tayi ke kadai, bayan sallar isha'ine aka kawo mana abinci cikin kuloli, nan aka shiga ci tare da lbrn karamcin mutanen yola, dan bikin nasu ya burge dangina, tabbas yola nima zance sunada karamci, ina kwance tunanin yanzu abkr yanacan tare da matarsa, sai mukaji sallama, rahma ta amsa, tace rufe fuskarki ga angonki nan, nace mezaizo yayimin? Rahma tace inya shigo saiki tambayeshi magulmaciya, koda baki fadaba nasan tunaninshi kikeyi, nace kada kimin sharri, tunanin me zan tsayayi? Kafin tace wani abun sun shigo, hashim yace sai mun sayi bake kenan? Naga amaryar tasha lullubi,
Chapter 17 · 0% Book details