← Book details Sanadin Boko Part 3 complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 19

Sashe 18

Sanadin Boko Part 3 complete Hausa Novel · about 7 min read

rahma tace dame kake zato? Nan dai sukayi addu'oi tare dayi mana nasiha, sannan suka mikawa rahma kudi da ledar kaza, daya daga cikin wadanda bansaniba yace, to tunda anbiya saiki bude mana fuskarki mugani, nayi musu shiru, haka nan naki bude fuskar sugani, nayi shiru sannan suka mike dukkansu, abkr ya dubi rahma, saiku zama cikin shiri, kunayin sallar asubahi in Allah yatashemu zaku dauki hanya, tace to, abokan suka fita, rahma ma tafice, saini saishi, duk mukayi shiru, yana dai tsaye, yace, inbaki da mgn nizan tafi gurin amaryata, uwargidanki kenan saida safe, da sauri na dubeshi bayan na janye mayafin kaina, shima ni yake duba, bansan me yake zuciyarshiba, nidai tawa zuciyar kishine fal, na kauda kai cikin takaici nace, to dama akwai wanda yace ba amaryarka bace? Allah yabamu alheri, na mike tare da tura kofar toilet na shige, banjin fitsari amma dole nayishi, don banason tsayawa kusa dashi, dana fito yatafi, ina jiyosu sunayiwa sauran yan'uwana sallama afalo, Rahma tashigo, har kunyi sallamar? Nace na lura bazaki rike mijinki da kyauba, kada dai kimanta cewa ku 2 ne, nace um! Niba shine agabanaba, kuma bazan wulakanta kainaba, don na lura bana cikin yan kayanshi, abinda nasani shine, duk zaman daya zaba shi zamuyi, rahma tace shikenan, in kinyi tunanin yanda zaki kama mijinki a hannu kya kirani a wayata, tajawo ledar gabanta, bari mu tayaki cin kajin tunda ba ango, nace ke ango ya dama, niko ajikina, tace, abakiba, nan tafito da kaza daya, nace su dauka suka tace a'a, bansan meya hanani bacci ba wannan dare, alwala na dauro nazo na duka inata nafila, sai naji raina yayi sanyi harma bacci yana dibana, kacaniyarsu rahmace ta farkar dani, sunata shirin tafia, nima na tashi nahau shiri, rahma tace, waike inazaki naga kina diban kaya cikin karamin akwati? Nace kano mana, karatuna zanyi wasa dashine? Tace kun shirya hakan keda mijinki? Nace um! Zancen kikeso.Sai gasu sun shigo, waisu fito yan kd, nace ni yan kn zanbi, damasu mama sun tafi da shadad sbd makarntashi, na zura hijabina, yan gdan sun shigo sunata godia ga yan kd, tare dayi musu alheri wai inji lamido, turaman zannuwa ne da kudi na shan ruwa a hanya, har sun shiga motoci saiga abkr akan mashin ya tuko, yana sanye da farar jallabiy mai gajeran hannu, dama ina cikin tunanin watonba zayazo yayi sallama da yan'uwanama, kallo daya nayi mishi nakau dakai, duk sai naji haushi yake bani, musamman da zuciyata take rayamin cewa daga ganinshi yasha amarci, ina kallo shima yaciro kudi ya mika musu, motarsu tatashi ta nufi gate, na juya nabarsu nan tsaye dasu rahma, ko karyawa na kasa, duk tsananin son masa (waina) danakeyi, sagir yana kiran rahma waita shirya, nima na hau kintsi, rahma sai daria takemin. Can suka shigo dasu abkr, sai kamshi tare da kyallin goshi yake, daga ka ganshi ango dai sosai, yasha boyil mai ruwan kasa, hula minista baka, takami ma haka, suna gaisawa rahma tace, waida hafsa zamu wuce kn? Na zabga mata harara, wai nema? Ya dubeni da mamaki, mexakije yi kn? Nayi farin rashin kunya tare da murguda baki, menakeyi da jarabawa na tahowa zaman me zanyi anan? Rahma tace zaman aure, nace hum! Sai naga yayi murmushi, sagir yace, kibari ai angon zai kawoki ida lkcn zana jarabawar yayi, nace nidai gaskia tafia zanyi, idanuna suka kawo kwalla, sagir yace to abkr amaryar nan shagwaba takeji, abkr yace, tayi son ranta, amma tafia sai nai niyya, rahma tace ni tunaninama Allah yasa miyar nan bata lalaceba, sannan walimarmu tasha ruwa. Nace in kinje kirabawa makota, rahma tace to, narigasu isa wajen motar, nakama murfin zan bude, abkr ya dallamin harara, na matsa ya bude musu suka shiga.bayan tafiyarsu rahma, ina tsaye na cije lebe ina kallonsu, zuciyata tana tukuki, da sauri na juya daki, nafada gado ina kuka tamkar yarinya, tausayin kaina nakeyi, bansan irin rayuwar dazanyiba, kamshin turarensane ya cikamin hanci, don haka saina zaci yana tsaye, da sauri na dago kaina tare da waiwayowa, shine kuwa, yace sbd kina zaton za'a cinyeki shiyasa kikeson tafia ko? Na zuba mishi ido ban tabkaba, shima ni yake kallo, ya dauke kanshi daga kallona, koda yake dama bani kike soba, na sunkuyar dakai, yace gaba, ance so dayane tak! Kuma tuni kin dorashi kan wani, na dago da sauri muka hada ido, na juya mishi baya cike da suyan rai, kana nufin bana sonka? Yace basaina maimaitaba, in kuma ba hakaba, menene dalilin kukanki? Nadubeshi, duk wata amarya tanayin irin wanan kukan a wannan ranar, dole nayi kewar yan'uwa, yace ko? Amma dana zaci ba yauce rana ta farko dakika soma rabuwa dasuba? Gabana yafadi don na fahimci mgn yajefamin, ka iya fadin duk abinda ranka yaso game dani, don naga kamar don hakan ka aureni, na zauna bakin gado cikin bakin ciki tare da tausayama kaina, yatako ya matso kusa dani, don haka na aureki, kuma zanci gaba da fada miki duk mgnr da tazo bakina, sbd baki iya tauna mgn ba kafin ta fito daga bakinki, duk sanda na kalleki saina tuna cewa ke karuwa ce ada, na mike a fusace, zamanmu bazai yiwuba matsawar zaka dinga kallona wa wannan fentin, ya zauna kan madubi yace, waya shafa miki fentin? Inace kece da bakinki kika shafama kanki? So yajaki kika zubar da kimarki, kuka ya kufcemin, cikin kukan nake cewa, nikam tafiya zanyi, kasakeni.Yayi yar dariya ' ina sonki tsakanina dake babu batun saki. Tafia ce dai in kince zakiyi ta bazan sha mamaki ba tunda mahaifanki ma kin tafi kin barsu bare ni. Yanzun ma kya iya tafia in kinso ya juya ya fita, nace 'subhanallah' wannan wace irin rayuwa ce? Nayi kukana na qoshi sannan na share hawayena babu me bani haquri. Na kira Rahma suna hanya cikin dusasshiyar murya nace Rahma Abubakar yazo yaci mun mutunci ni gsky bazan iya zama dashi ba. Rahma tace meya fada miki? na sanar da ita komai tayi shiru na dan lkc can tace kiyi haquri duk laifin kine da kika sanar dashi ta bai baishi kuma mutun ne mai mita tare daqin saurare. Munyi munyi ni da sagir kan cewa ya sauraremu dan muyi masa bayanin gsky lamarin sai yace"Ai kin gama magana shi ba zaya iya jin wata kwaskwarima ba sannan yayanki umar yace masa da soyayya ya yaudareki kika bada kanki don haka yanzun shawarata itace kiyi shiru da duk abinda zai ce kada ki tanka shi. Na kula yanada mugun kishi ne nace ko gidan karuwai ya ganni yace yana so bai dace yazo kuma ya dinga ca6a min magana ba. Rahma tace kada ki damu zai zo ya yi nadama nace kinga dai ga jarabawar mu tazo bana zaton zan zana ta. Na sake rushewa da kuka shekara ta ta qarshe Rahama tace ki daina damuwa addu'a itace kadai mafita Allah zai kawo sanadiyyar da zaya fahinci gsky nace shi kenan. Ranar har magriba ban kuma ganinshi ba abinci daga cikin gida ake kawominsanda saudatu ta kawomin na dare na rana ko bude shi banyi ba. Tace ke kam baki san cin abinci gashi kina ta kuka kiyi haquri aure kenan zaki saba damu in kin saki jiki. Mu kam bamu da wata matsala nace to nagode nayo wanka don na fara sallah. Nayi shafa'i da wuturi sannan nayi shirin bacci sam bana kojin yunwa na hau gadona kwanta. Text ya shigo cikin wayata na duba shine angon nawa. Yace bazan samu shigowa ba don fadi bata san in fitavqila sai gobe. Duk suyan da raina ke yi sai na rubuta cewa Allah ya kaimu ka gaisheta. Na share hawayen da ya zubomin sannan naje na rufe qafata. Abubakar dake kwance kan gadon shi tsararre tun da ya shigo daha salkar isha'i yake kai kwance. Gaban mudubin dakin fadi ce tana fesa turaruka shi masu qamshi sanye take da rigar bacci me shegen kyau tare da ma'ana. Daga inda yake kwance yana kallan ta zuciyarshi fadi take ina ma ace hafsat ce haka a gabanshi. Me yasa ta fadi mishi cewa ita karuwa ce? Me yasa ta kasa adana masa kantahar zuwa lkcn da zai aureta?.Shin maza nawane suka kwanta da ita? Abinda ke sashi ganin ba zaya kusanta kanshi da ita ba kenan. Dalilai 2 suka sa shi auranta na 1 tsabar santa da qaunarta na 2 kuma.....
Chapter 18 · 0% Book details