← Book details Sanadin Boko Part 3 complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 19

Sashe 12

Sanadin Boko Part 3 complete Hausa Novel · about 6 min read

"Um!!! Ni dai zanga ikon Allah." Ina zuwa gida na tarar an canja min kwadon kofata, na yi turus! Na jiya na nufi gidansu Rahma, cikin fara'a Mama ta tareni muka gaisa, ta turo min kwanon danwake tana cewa, "Maza ki ci mutumin naki." Na ce, "Mama ba ta cin danwake nake ba, na zone naga an canjamin makulli." Ta ce, "Yaron nan Abubakar ya kawo, ya gaya min ai kunyi sallama ko?" Na dubeta ina so na fahimci Abubakar ya zo ne? Ta ce, "eh, harma ya bani dubu 2 kyayi masa godiya ma." Na ce, "To, amma nifa ban ganshi da idona ba." Mama ta ce, "Ya hausar baki ganshi ba? Ya ce min kun zanta yanda bikin zai kasance saboda lokaci ya kure." Na ce, "To bansan an yi ba." Mama ta hauni da fada, wai in dai nutsu ina sone in kishi. Na dai ce a bani Makulli, ta bani na nufi gida na bude kofar, buhun shinkafa ne karami sai sabulun wanka da na wanki, sai kayan tea da kudi dubu 5 na gani, sai takarda akan kayan, ga abinda takardar take cewa, "Na san cewa kin san komai game da auranmu dake gabatowa, wadannan kayan abincinki ne, na san zasu isheki kafin bikin, sannan na haramta miki zuwa gurin aiki, Makaranta kawai na aminta ki je."Duk son da nake yiwa Abubakar sai da naji haushi ya kamani, wace irin kaddara ce wannan? Wane irin iko ne Abubakar yake min? A haka zan je gidansa yana min wulakanci? Ni fa Allah ya sani ba zan dauki wulakanci ba. Ni kadai na dinga Jaraba ina mita, daga bisani na yanke shawarar kiransa a waya, sau 2 tana yi tana katsewa yaki dauka, na kara cika dan takaici, na zauna na rubuta masa text, "Ka sani fa bana son ka, sannan ba zanyi auren wulakanci ba, don kawai kana sona saika dinga nuna min iko? Don kasa an sallameni a gurin aiki ko kana takama naku ne? To zan nemi wani, kuma ban ce ina neman taimakoba har da zaka kawo min abinci tare da karfin halin canzamin kwadon kofa." Ina kammalawa na tura masa sakon text din, zuciyata cike da fushi da takaici.yana jin shigowar sakon amma bai duba ba, domin yana zaune gaban Dadarsu, yana so yayi mata batun dake tare da shi, ta ce, "Ina jinka." Ya ce, "Daman Dada ina so nayi magana ne akan kayan lefen da za'a kai, inaso idan naje Dubai na karo wasu." Dada sai ta saki baki kawai tana kallonshi, lallai Abubakar ya zo da sabon salo, sai ta ja tsaki ta ce, "Kai yanzu yaron nan har kayi girma da kudin da zaka zo kace zaka hada kayan aure? Ka manta kenan duk abinda Lamido yake yi kai bai ma be kenan? Sanin kanka ne duk wanda zai yi aure a cikin zuri'armu Lamido ne yake mishi komai, shine ni zaka zo kace wai zaka yi wani kaya, to shike nan kaje kayi amma ba da yawuna ba, kai baka da tunani ne? Wace irin yarinya kake nema da kake rawar kafa a kanta haka? Ni dai ba zaka jawon magana ba, ka tashi ka bani wuri."yal tashi jiki a sanyaye, tare da cewa, "Ki yi hakuri." Ya ce, "Kuma duk abinda kuka yi daidai ne." "Sai ka zuba ido kaga abinda Lamido zai yi, shike nan jeka." Yana fita suka hadu da Hashim, yake gaya masa yadda suka yi da Dada, ya ce, "Kaima ka yi laifi, kana so ka jawowa Hafsa tsana a dangi ko? Ka bari kaga iya gudun ruwansu, ai sun san komai a kai." Ya ce, "To shikenan to!!" Tabbas familyn Lamido auren farko yi maka za'a yi, in kuma ka cika zakewa yanzu za'a ce maka rashin kunya, balle Hamma da yayi fice tunda ya dauka 'yar waje (bare). Bayan sun gama magana da Hashim, yana kashewa sai yaga text din, ya bude ya duba ya ja tsaki, ya mike ya zauna bakin gadon tare da dauko wayarshi, nan take ya ga ya dace ya bata amsa don haka ya rubuta cewa, "Ban damu ki soni ba, asiri fa zan rufa miki, in bani ba dinma wa zai auri 'yar gagara? Zancen aiki kuwa, kya iya komawa, baki ji maganar Iyayenki ba ni zaki ji tawa? Kya iyayin duk abin da kike so tunda kina da 'yanci, barikin kenan."Lokacin da sakon ya shigo wayata kuka na saka, Mijin da zan aura ke fadamin haka? Na kira Rahma ina kuka wiwi na fada mata komai, ta ce, "Ki yi hakuri zan kirashi." Na ce, "Kada ki yi masa magana, illa kawai ana daura aure zan kama gabana." Rahma ta ce, "Ki yi hakuri ina nan zuwa." Su da Sagir suka zo da dare, lokacin na idar da Sallar Isha'i kenan, Shadad yana kwance kusa da ni, ko abinci na kasa ci. Suka yi sallama na amsa, suka zauna Rahma ta ce, "Wai mai ya faru?" Na ce, "Rahma duba text din nan." Na mika mata wayar ta karanta, tana gamawa sannan ta mikawa Sagir, shima ya ce, "Ki yi hakuri, wallahi ni nasan Abubakar yana sonki, kiran kanki Karuwa da kika yi shine silar fushinsa." Rahma ta ce, "Kuma yaki ya saurari kowa ya ji yanda abubuwa suka faru." Na ce, "Ni dai gudu zanyi matsawar aka ce yau shine mijina, duk da cewa nasan ina son shi." Sagir ya ce, "In kin gudu me Iyayenki zasu dauka? Wace rayuwa zaki samu a gaba? Kuma zaki sake samun wanda kike so kamar shi? Duk wadannan tambayoyin ya kamata ki yiwa kanki su, sannan ki amsa su duka." Na fashe da kuka, bani da zabin da ya wuce hakuri, domin Sagir gaskiya ya fada min, Allah ka shige min gaba. Rahma ta ce, "Ya zo ne akan batun wane irin shagali zamu yi saboda katin da za'a bugo, na san dai baki wuce Walima ba shiya sa na fada masa haka." Na ce, "Wa na sani da za'a buga kati? Ni walimar ma ba zanyi ba." Rahma ta ce, "Ka jita ko? Shiya sa nake ta gaban kaina, na san ba zata bada hadin kai ba." Sagir ya ce, "Yanzu dai Hafsa a shawarce ki zuba mana ido, naki bine kawai." Na ce, "A'a, kun zo da abinda ya sabama shari'a ba zan baku goyon baya ba." Suka yi dariya, haka suka yita lallashina tare da kare Abubakar har dai na danji sanyi suka tafi, bayan Rahma ta yi delete din text. Ana saura kwana 10 biki, danginsa suka nufi Kaduna da lefe, saitin akwati mai 5 dauke da kaya masu tsadar gaske, Goggonninsa sunyi mamaki gadin gidan da Abubakar ya nemo aure takalawa ne lis, sai dai an karbesu cikin karamci, da kayan abinci da nasha masu kyau wanda Murja Matar Yaya Umar ta yo. Dakin Baba aka share aka shimfida darduma, bayan sun ci sun sha sukai sallah, sannan aka bude kaya. Matan gidan suka shigo sunata yabawa saboda irin wannan kaya haka, daya daga cikin 'yan kawo kaya ta ce, "Ina amaryar ne?" Baaba ta ce, "Tana can Kano tana karatu a can." Umar ya kawo dubu 10 na tukuici tare da cewa su yi hakuri sun gode. Ko da suka dawo sun ce an karbesu hannu bibbiyu, kuma suna da karamci Iyayenta sai dai talakawa ne lis. Dada ta ce, "Shi dai ya sani kuma ya jiyo." Waya Rahma ta kira Sa'adatu ta makarantarmu, take gaya mata batun aurena yadda zasu shirya, sannan ta ce don Allah gobe zata zo har makaranta ta bata kati dan ta rabawa kawayenta. Sa'adatu ta ce, "Allah ya kaimu." Rahma ta dubeni ta ce, "Kin ga illar kin shiga jama'a, wallahi ki canja hali, dan family din da zaki shiga suna da yawa." ......
Chapter 12 · 0% Book details