← Book details Sanadin Boko Part 3 complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 19

Sashe 11

Sanadin Boko Part 3 complete Hausa Novel · about 8 min read

Sanadin Boko 3-04 Posted by ANaM Dorayi on 06:15 AM, 28-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Shi kuwa Hashim da suka je gidan Munnir yaron Dady yana kallonshi gabansa ya fadi, domin suna matukar kama da Shadad, a ransa ya ce, "Ko dai wannan ne Munnir din da yaci amanar Hafsa?" Sai yaron Dady ya cewa Munnir Dady ne yace na rako shi nan, wai dan aminin nan nasa ne na Adamawa. Munnir ya ba Hashim hannu suka gaisa, sannan ya ce da direbaa ya tafi, su kuma suka shiga.Matar Munnir wadda ya kira da Baby ta mike ta ce, "Angel bako muka yi ne?" Ya ce, "Eh." Suka hada ido da Hashim ya yi sauri ya kawar da kansa gefe, domin tana sake da gajeren wando da ya dame shape din mazaunanta, da kuma karamar riga da ko cibinta bata sakko ba, ga wani karin gashi buzu-buzu, kumbarta duk farata zako-zako. Hashim dai a ransa ya ce, "In dai wannan ce wayewa to gaskiya bata da wani amfani." MUnnir ya cema Hashim, "Ga matata Hasina." Itama ya ce mata, "Ga Hashim dan abokin Dady na yola." Suka ci gaba da magana cewa daman ku ne Dady yaketa bani labarin Yola yana da amini, amma saduwa tayi wuya? Ya ce, "Wallahi, haka ne daman." Hashim dai a dadare yake saboda sam ko ruwa ya kasa sha, kyankyamin farata da gashin Hasina yake, da ya gaji dai ya ce masa yana so ya huta, shine ya kaishi masauki. Yana shiga ya fada toilet domin watsa ruwa, sai da ya gama sannan ya kunna wayarsa saboda Abubakar, ai kuwa yana kunnawa sakon Abubakar ya fara karo da shi na cewar sun isa lafiya? Kuma ya yi masa bayanin yanda ake ciki.Ai bai gama karanta sakon ba sai ga waya daga Abubakar, ya daga tare da Sallama, Abubakar ya ce, "Iskanci ne ya saka kashe waya ko me?" Hashim ya ce, "Na sani saboda kai na kashe, domin zaka dame ni." Abubakar ya ce, "Ai hankalina ya fara tashi saboda ina tunanin likin da nai ya balle." Hashim ya ce, "Ko daya, domin ko gidan ma bamu je ba." A nan dai ya gaya masa yadda aka yi. Abubakar ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Shi kenan, sai Allah ya kaimu. Pls abokina ka tsare komai." Hashim ya ce, "Kai Malam sa Allah a ranka." Abubakar ya ce, "Da kai na sa a ran? -ya ce- Pls ka dan yimin kokari nasan zaka iya komai." Washegari misalin karfe 10 na safe bayan sun karya, sun kintsa Hashim ya kira Umar cewa suna tafe, nan take ya iso gidan Babansu, Umar ne yayi jagora har shagon da za'a karbe su, sun gaisa cikin mutunta juna inda suka nemawa Abubakar auren Hafsa akan sadaki dubu 10, sannan suka sanar dasu Matan 2 zai aura nan da kwana 23, don haka suka ce ahada Iyayen Hafsa. An yi komai cikin mutunta juna, sai dai suka fito Dady ya ce, "'Yar talakawa haka? Ai da kun sani kun zo gidana kun duba." Baffa Magaji ya ce, "Kai yaron nan da rore- rore yake, dubi Anguwan nan kasan talauci yayi katutu a cikin ta." Baffa Sa'adu ya ce, "Tarbiyyarta ya yaba, sannan na fada muku gwagwarmayar da akai akan auren nan da yakin da Abubakar yayi, don haka kawai ku bar zancen nan. Allah dai ya shige mana gaba." Suka ce Ameen Koda suka dau hanya Hashim yana ta yaba musu halayenta, lokacin da Abubakar ya kira Hashim sun yi nisa a titi, ya ce, "Hashim yaya?" Ya ce, "An gama komai, muna hanya yanzu, an baka auren Hafsa." "Masha Allah." In ji Abubakar, yanzu kam baya da wata matsala. Ni kam zuwan Inna gurina ya dawo min da farin cikina ta wani bangaren, musamman ma dana dawo school na samu har girki tayi mana, sai da nayi kukan dadi, gashi yau ina cin abincin Innata, ashe zan sake cin abincin Inna ta? Kwananta 3 Umar ya zo suka tafi, sannan ya sanar da ita zuwan Iyayen Abubakar.Hafsa ta ce, "Yaya Umar ya fa fasa aurena, me zaya kai Iyayenshi gidanmu?" Umar ya ce, "Kawai abinda zan fada miki shine kibi Iyayenshi, sannan ki amince masa ki rufawa kanki asiri, mutum ne nagari dan mutunci, mafi yawan Mazan yanzu suna yin auren tamore ne, basa bin abinda addini ya ce, ka aureta dan addininta, nasabarta, dukiyarta, kyanta, wannan samun Abubakar sai an tona." Inna ta ce, "Samun miji kamar Abubakar dace ne, dan haka ki nutsu." Suka min nasiha suka tafi, sun barni cikin kewa, nan da nan naji kaunar gidanmu ta isheni, don haka na hada kayana da cewa wani satin zan tafi Kd. Gidan Maman Rahma na kai Shadad, ni kuma na tafi, a hanya gani nake KD tafiyar tamin nisa, ganin nisar hanyar na yi, tunda na zo garin ban kuma bin hanyar ba. Ina sauka tashar Kawo na samu motar anguwarmu, ina shiga layinmu na ga canje-canje daban-daban, na yi Sallama a gidan aka amsa. Wanda suka sanni suka fara fadin, ""Hafsa ce yau a gari?" Sai suka shiga kallon kallo tsakaninsu, wasu suka fara shiga daki kai gulmata na dawo. Baaba ta fito da gudu ta rungumeni, sai naji wasu suna cewa, "Wannan ita ce Hafsan?" Labarin duk ya bazu cewar na zo, ana ta min sannu da zuwa, naga yara kanana da na tafi na bari duk sun girma, abubuwa duk sun canza.Dakin Baaba na shiga muka gaisa, nace mata ina Baba ta ce, "Yana dakin shi, sha ruwa ki je ku gaisa." Na tashi na shiga wajen Baba, ina zuwa naje gare shi ya ce, "Hafsatuna ke ce?" Na ce, "Ni ce Baba, kayi hakuri ka yafe min, nice duk na jawo muku." Ya ce, "Hafsa laifina ne da nayi miki baki, da ace ban miki baki ba da haka bata faru dake ba, maimakon nasa miki albarka akan abinda zaki yi sai na biki da mugun fata, na yi da- na-sani, tunda na koreku bani da kwanciyar hankali, lafiya bata isheni ba, ki yafemin Hafsatuna." Sai kuka shima Baban, itama Hafsa sai kuka, ta ce, "Ka yafe min Baba." Ya ce, "Na yafe miki 'ya ta.Na ce masa, "Baba ya jiki?" Ya ce, "Jiki da sauki, daman akwai ciwon rashinki, amma yanzu gaki kin dawo Alhamdulillah." Na sauna na ci abinci cikin jin dadi da ganin gidanmu, na kira Umar nace masa na sauka lafiya, ya ce to yana nan zuwa gare ni. 'Yan gulma an fara shigowa gana Hafsa wai ta dawo, akwai wata kawar Innarmu sai gata ta zo, "'yar nan ke kuwa mai yayi zafi haka zaki tafi kawai a wayi gari baki nan? Ina kika tafi? Ina cikin da kika tafi da shi? Me kika haifa?" Raina ya baci da tambayoyin ta amma sai na ce mata, "Yana can inda yake yaron." Baba ya ce, "Tabawa ai komai ya wuce tunda ga Hafsa gare ni, kuskure ne aka samu." Ta sake cewa, "To yanzu ina ki ke?" Cikin kosawa na ce, "Kano kuma karatu nake yi." Maza na shiga kiran wayar Rahma don bana son wadannan tambayoyin, na kara wayar a kunnena ina ji tana cewa, "To gun wa kike? Kuma duk tsawon lokacin nan baki yi aure ba?" Na yi mata shiru, Rahma ta daga na ce mata ga Babana, ta ce haba? Na ce, "Kina shakku ne? Gashi ku gaisa." Na mika masa tare da cewa, "Rahma ce wadda nake tunanin ka samu labarinta a gurin Umar." Ya ce, "Kwarai kuwa, mutanen arziki." Suka gaisa, daga nan na tashi na koma dakin Baaba, na bar Tabawa nan zaune tana damun Baba da tambayoyi, anan ne yake fada mata cewar zanyi nan da lokaci kankani, ta fito tana cewa, "Abu yayi dadi, ai gwara tai auren." Ta fito tana maganar, matan gidan suka ce ai gwara auren ina amfanin zaman bariki? Su a zatonsu yawon dandi nake, raina na ce kanku ake ji Lokacin da nazo fita ni da Faty zata rakani gidan Yaya Umar, ina jin Ade tana cewa, "Duk yanda aka yi dan Bariki ne irinta, ko kuma kara da kiyashi za'a yi." Asabe ta ce, "Daukar mara sani kenan." Na wuce ban tanka musu ba. Gaskiya Baaba mutum ce domin bata shaida musu batun aurena da zuwana ba, gidan Yaya Umar na kwana, da safe na zo gida Ummy ta makale min dan itace wadda muka shaku, sauran kuwa basu dokin zuwana, domin an gaya musu nice sanadin tafiyar Innarsu, Ban ga laifinsu ba don kuwa ni ce naja musu, duk zancen da muke da Baaba da Baba tare da Yaya Umar, duk magana ce akan na daure na yiwa Abubakar halacci, na rike shi amana, dan mutum ne mai sona, yayi jihadi a yadda nake ya aureni, har suna cewa samun kamarshi sai an tona. Sai nake tambayar kaina, "To wai saninshi suka yi suke masa haka? Ko kuwa zuwan da yayi ne suka yanke masa wannan hukuncin?" Haka na shirya na koma Kano, inata karatu da zuwa aikina. Wata ranar Juma'a ina zaune gaban computer ina latse- latse na gurin aikina, kawai sai naga Manaja ya miko min doguwar takarda, na ce, "Me ya faru?" Ya ce, "Masu gurin ne suka buka ci a sallame ki." Na ce, "Ni kuwa me nayi za'a sallame ni? Me nai musu?" Ya ce, "Wannan kuma sai ki tambaye su." Na ce, "Shike nan." Na tashi nayi bankwana da su Musa.Gidan Rahma na je da kuka na, dan aikin da nake ji dashi yake rufan asiri an tsigeni akai, dariya ta saka min wai gurin fa na Maman su Abubakar dinki ne. Na ce, "Ai nawane ma Abubakar din?" Ta ce, "Eh mana, jiya ya zo nasan dai kun sasanta." Na ce, "Ni ban ganshi ba."Cikin mamaki ta ce, "Bai zo gurinki ba?" Na ce, "Ban ganshi ba." Ta ce, "Dazun nan yayi sallama damu ya koma." Na ce, "Um, to don Allah a haka zaka auri mutum?" Rahma ta ce, "To har bikinku ya kusa don haka sai ki soma shiri." Na ce, "Rahma abubuwan da suke faruwa a kaina tamkar a mafarki, to yanzun auren dole za'a min ko kuwa? Ban san komai ba akan auren." Rahma ta ce, "Saura sati 2." Na ce,
Chapter 11 · 0% Book details