Sashe 8
Sanadin Boko Part 3 complete Hausa Novel · about 8 min read
Sanadin Boko 3-03 Posted by ANaM Dorayi on 09:35 PM, 27-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Ya ce, "Suna nan, Baba ne dai ba lafiya, ya fi shekara baya fita." Idanuna suka ciko da kwalla na ce, "Allah ina zaton halin da na saka su a ciki ne ya sa shi rashin lafiya." Umar ya ce, "A'a lalura ce kawai." Na ce, "Ina Ummi?" Ya ce, "Ummi ta yi tsawo, sai kin ganta." Na ce, "Inna fa?" Ya ce, "Inna tana Funtua." Na tsura mishi ido, "Me take yi a can? Ko suna da dangi ne?" Ya ce, "A'a, tayi aure can da Yaranta ma 2." Nan take na dafe kirji, kuka ya kuma kwace min na ce, "Ban yiwa Iyaye na adalci ba, sun soni, sun min dukkan abinda iyaye kewa dansu daidai karfi, amma ni sai na tarwatsa su." Yaya Umar ya ce, "Komai mukaddarine kada ki damu." Tsaki Abubakar yayi tare da tabe baki, ni dai na kauda kaina gefe. Likita ya shigo a nata 'yan hirarraki ya bani sallama. Daga nan Sagir ya kwashemu mu 6 banda Abubakar, don yace muje kawai, muka fice zuwa gidana. Mama dama ita bata shiga ba gidansu ta wuce, sai ga Shadad ya rugo da gudu, Mama ta ce mishi na dawo shine ya taho. Mama tana barinshi gida ne saboda rigima da yake yi a asibiti, ya fada jikina yana min oyoyo Aunty. Umar ya zuba mishi ido, shi kam sai yanzu ya tuna fa ashe da ciki na bar gida, ya ce, "Dan da kika haifa kenan?"nace shine, sunansa shadad, idanuna suka soma kawo ruwa, nace jeka gurin kawunka, yamike yaje gurin umar, umar yace tabbas wannan dan munnir ne, kamarsu ta baci, kinga ko dolensa ya amshi danshi, nace ai yaya wlh baxan bashi yaron nanba, koshi ya bukata, inkuma kunsan zakuce in kaishine tobazan koma gdaba, daganan gabama zanci.... da sauri umar yace, toshikenan anbar maganar, kusan karfe 1 har sagir da hashim sunyi mana sallama, sai kuma gasu sun shigo da kayan abinci, karamin buhun shinkafa ne da taliya, sagir ya mikoma rahma kudi batare da yayi mata mgn ba, yafita. sannan ya kirata a waya, wai tabani inji abbkr ne, amma tace inji sagir, rahma kuwa tabani tace inji sagir, nace kaiba zan amsaba kashe kudin yayi yawa, dubi kwanciyata a asbitifa, tace a'a asbitinki ina ganin hashim ne, na amsa tare da cewa, ko wanene ma dai nagode.Rahma ce tadafa mana abinci mukaci, misalin karfe 3 yaya umar yashirya tafia kd, nace yasakebi ta gidansu maman rahma yayi mata godia, don tun bayan fitarsu sagir na bashi labarin komai, tundaga tafiyata har iyanzu har tsakanina da munnir ban boye masa komaiba, yacemin yana ganin munnir shima a wata jibgegiyar mota lkc zuwa lkc, yafadamin dukkanin abubuwan da suka faru bayan barina gda, nayi kuka sosai, yace karna damu komai yafaru da mumini daga Allah ne, kuma sakayya tana nan tafe tsakanina da munnir, insha Allah sai kowa yagane fyade ya miki, nidashi da rahma mukaje gdansu mama inda yayi mata godia bisa godiya bisa rkon datayimin, yayi addu'a ga likita hindu wadda tamin gata, munayi masa rakiya saiga sagir da abbkr, yace da umar yadan jirashi.suka shigo gurin rahma ashe sallama yayo mata, suka kira umar gefe sukayi sallama dashi, sannan abubakar yabashi kudi tare da tabbatar mishi da cewa tsakanin gobe zuwa jibi iyayensa zasuzo, don haka yasanar dasu, bansan mesuke tattaunawaba, yazo dai yacemin zasu saukeshi a gareji, nace to saimunyi waya, don nakarbi lambarshi, yasoma yakira inna muyi mgn nace mishi a'a baxan iya mgn awayaba, washe gari naje skul, ashe na danji sauki, kuma yanzun na rage kuncin zucia kamar da, ina zaune ina krt wata baiwar Allah tayimin sallama, nakalleta tanamin murmushi tare da sallama, na amsa mata nima cikin sakin fuska, tace nadaina ganinki kwana 2 lfy, naga kindan rame, nace banda lfy ne, har na kwanta asbiti, taxauna tare da cewa eyya, Allah yasauwake, saita danyi shiru daga baya kuma tacemin sunana sa'adatu sulymn, kekumafa? nace sunana hafsa, tacemin inaso muzama kawaye inba damuwa, nace bakomai, mun danyi hira, sannan tatafi, abinda yafi cizon raina yanzu a wane matsayi abk ya ajiyeni? da nayi zaton yabarni har abada, amma sai gashi yazo asbiti, duk dabaimin mgn ba, kuma naganshi a layinmu yazo gidan mama yakira yaya umar, kenan har yanzu yana sona? bari in isa gda in kirashi, ta gidan rahma nabiya, ban boye mata komaiba abinda ke raina, itama ta amince da cewa inkirashi mu gaisa na masa godia, donfa gaskia shine ya nauki nauyin asbitinki, tace, hatta jinin da aka karamin nashine yabada, amma baisan cewa su sagir sun saniba, tace keko shinkafar nan da kudin nan shine yakawo nace sagir ne don kada kiki karba, bayan tayi shiru, sai kuma takara da cewa, abk yana sonki, matsalar karuwancin dakika dorawa kankine, kinsan maxa sunada kishi, kuma gaskia yana kishinki, yakuma ki sauraron kowa cikinsu sagir bare suyi masa bayanin danayi musu, nace, kinbasu lbr komai game dani ne9 tace, sun bukaci nafada musu, shine kawai yaki sauraro, na jinjina kai nace, toba ance shima bashida lfy ba? tace eh, saidaya bada jini ko sallamarshi ba'ayiba, wani sanyi naji cikin raina, jinin abk yana gauraye da nawa? na sauke ajiyar zucia na kalli rahma, anjima zan kirashi, to waima in nakira nace masa me? rahma tace kirashi yanzun, nacije nace to bari nakira, nalatsa lambarshi ta tafi, nace to rahma mexance masa ne don Allah? wayar tasoma ringing, daidai lokacin yana zaune a babban falonsu, yana tare da wasu daga cikin danginsa sunzo dubashi, aciki harda fadima, ya kalli number dake jikin wayar, tamkar yashare, amma saiya kasa, don lokacin ma itace azuciyasa, ya amsa sallama ta bayan ya daga wayar, na kalli rahma mexance? ( amma da hannu nayi mata alama) ta harareni, ku gaisa mana, ta fada a hankali, nace ina yini, ka isa gda lfy? ba zato naji yaja tsaki, sannan yakashe wayar, na dubi rahma nace, tsaki yaja sannan yakashe, tace duk kece kika jama kanki, yaxa'ayi ki dora ma kanki halin daba nakiba? nace magana zarar bunu, na riga nafada ta fito bamai iya maidata, wasu zafafan hawayen son abk tsantsa suka soma sulalomin, ina sonshi rahma, idan yabarni dakyar in zan moru, bansan hakaba sai bayan dana furta kalmar datajamin tsana a gurinsa, tace kidaina kuka, duk abinda yasamu bawa daga Allah ne, kuma abk yana sonki, na tabbata zai aureki, na sauke ajiyar zucia tare da share hwy, koba gaskebane zancenki nadanji sanyi, kitayani da addu'a, rahma tace, tuni nake tayaki, nace ngd, Allah yabar zumunci, bari inje in dauko shadad in wuce gda, nasan yana jirana, tace to saimunyi waya, na daukoshi sannan na nufi gda, raina cunkushe, kunnuwana basu daina amsa kuwwar tsakin da abk sadiq yaminba, duk da tsananin son danake masa amma baxan juri wulakanciba, ban taba tunanin wata rana zatazo da namiji zaimin hakaba, domin banmayi tunanin cewa zan kalli namiji a matsayin mutum ba, tun bayan abinda munnir yayimin, ina yan aikace aikacena, lkc zuwa lkc inajan tsaki sbd abinda abk sdq din yayimin, dakuma tunanin cewa nidashi mun rabu kenan? Sallamar mamansu Rahma naji nafito daga kitchen ina amsawa turus na tsaya na tsaya ina kallon matar da suke tare, itace ko kuwa dai mafarki ne? bakina ya furta Inna! sai kuma na juya daki da gudu na zauna ragwaf,na kifa kaina cikin cinyata, kuka na saki wanda ya farkar da shadad daga bacci Mama tace ji wani sakarci shigo daga ciki" ta umarci inna,inna ta shigo ta zauna itama ta zauna shadad ya taso yazo ya dafa bayana yana son yayi kuka yana cewa Anty wanene ya dukeki? mama tace kyale wannan antyn taka mai kukan tsiya harsai an doketa? mama ta ci gaba to wannan kukan na menene? inna tace na rashin son gani nane, don haka ma yanzun zan tafi Da sauri na fada kanta ina cewa inna ki yafeni inna ban kyauta miki ba, inna na tuba natuba" inna kawai sai tasa kuka, mama tace haba maman hfsa, yaya kuma zaki taya ta?Da kyar ta lallashe mu. Na kasa hada ido da inna,duk da dadin da naji na ganinta. shadad na zaune a cinyarta, muryata a dusashe nace "yaya umar ne ya kawoki? tace ehh shine amma ya juya sbd suna da bakin da zasuje kd din gobe. Lkcn da muka zo kina mkrnta, shine yace bari ya kaini gdan maman taku" Na sauke a jiyar zucia, ina su kawu?tace kowa lpia. ina nan ina malumfashi kika ki nemanmu shekara da shekaru? Ina cikin bakin cikin kunan rai yanda kika gudu yafi bata min rai abisa cikin da kikayi. abinda ya kona min rai dake kenan Allah yasani hfsa banso kika guje min baNace inna bazan iya hada ido dake bane abnda kike min fada akanshi kullum na kiyaye ban kiyayeba. Amma wlh ba da gangan na aikataba munir fyade yamin ta karfi inna " inna tace umar ya fada min komai,Allah zai fidda ke ta shafa kan shadad Allah yayi maka Albarka ya tsareka da hali irin na munir, shi kuma Allah shine yasan yadda zaiyi da shi, mama tace komai dama mukaddari ne ga bawa Allah ya shige mana gaba. sannan game da yaron nan mai sonta kuyi mata fada,dan mutuncine tayi auranta tare da yin karatunta adakinta. Aure da haihuwa basa hana neman ilmi, yanzun baga rahma ba! da bamu bata goyon bayan taci gaba da karatu ba Amma yanxun da tayi aure mijin yace shifa matarsa fa makrnta zata koma, Nace dama rahma nason karatu gashi ta samu" mama dai ta tafi gda ta barmu. ranar kwana mukayi hira nida inna hirar bayan rabuwa, munyi kuka mun gaji. Da safe muka je makaranta nida shadad muka bar inna,duk wanda ke makarantarmu yau yasan ina cikin farin ciki, shi kuwa Abbkr lkcn dana kira dinnan ya min tsaki, yana kashewa ya mike ya nufi dakinsa ya kira umar suka gaisa. yace, umar don Allah idan iyayenmu sun zo gobe kada ka bar wata baraka da zata nuna cewa yarinyar nan ba a gda take ba" umar yace To insha Allahu ba wata matsala yace sannan ku amshesu da karamci suna son haka" umar yace insha