← Book details Sanadin Boko Part 3 complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 19

Sashe 15

Sanadin Boko Part 3 complete Hausa Novel · about 7 min read

Rahma ta zo ta sani sai da nayi kwalliya na shafa turare, sannan ta taya ni na zabi sarka da 'yan kunne da abin hannu zuwa zobuna, nan take na yi kyau. Jallabiyyar ta sha ado. Ta ce, "Ki zo ku gaisa da su Hashim da Sagir za suyi Yola, mu sai gobe da Asubahi. Kinge kenan muna da lokaci yau da yamma sai muje muyi gyaran kai tare da yin fulawa.Na ce, "Ke nifa in dai da Abubakar ba zan fita ba don kada ya yarfani a cikin mutane." Ta ce, "Suna wani shago can da Umar ya kaisu, suna cin abinci." Muka nufi shagon gurin su Hashim, Abubakar bai zo ba Sagir ya soma min tsiya, "Gata ango, gata Ango, cancadin shagali." Hashim ya ce, "Yi ma Umar waya ya turo mana mai hoton nan dole Ango ya ga hoton wannan shiga, sai kace Balarabiyar Sudan Masha Allah!" Na ce, "Kuna dai zagi na ne, kuma na gode." Muka gaisa Hashim ya ce, "Baffanmu sun tafi don Jirgi zasu bi mu kuma da ku Asubanci zamu yi." Na ce, "Gaskiya mun fa shirya Walima a Kano." Rahma ta ce, "To sai dai randa kika dawo kuyi." Na dubi Rahma, "Gobe zamu bar Yola ko? Don ina son yin karatu nan da kwana goma zamu fara zana Jarabawa." Hashim ya ce, "Ture batun komawa Kano gobe don Yola goben ne zamu soma namu biki." Sagir ya ce, "Mu ma sai an gama biki zamu wuce, na fada gurin aikina." Na ce, "Um!" Tunani na daya ban dinka komai ba, waton bani da sabon kaya, Rahma ma tayi wannan tunanin, amma bata ce komai ba lokacin wayar Hashim ta yi ruri ya daga kawai sai na ji ya ce, "Yawwa Munnir, ka shigo layin? In ka shigo layi na 3 din muna nan a wani shago jikin masallaci." Tsigar jikina ta soma tashi, kafafuwana suka yi rauni har na kasa rike kaina, na jingina da bango. Duk sakamakon sunan da naji an kira "Munir." Duk da bani da tabbacin akan cewa wanda na sani din ne. Ban ankara ba na ji muryarshi a kofar shagon yana sallama, numfashina ya yi sama da kyar na kwato shi, yana shigowa gurinmu ya soma jeho idanu shima mutuwar tsaye ya yi yayin da muka kalli juna ido cikin ido.Hashim da bai kula ba fadi yake, "Abinda ka makara, tuni an daura auren." Sam Munnir ya kasa kauda kanshi daga dubana, ban san nufin kallonshi gareni ba, amma ni kallon tsana ce da kiyayya mai tsanani nake masa, zuciyata ta shiga fadi min cewa, "Tashi ki shake shi, wanke shi da mari." Tsam na mike na fice a fusace, Hashim ya ce, "Zo mana Hafsat lafiya?" Rahma ta mike ta kwala min kira, "Hafsat! Hafsat!" Sam ban saurara ba ko ganin gabana bana yi, da ganin Munir gara ganin mai daukar raina. Na share zufa bayan na zauna, sam ban ji me su Innu suka cewa ba, ashe wai ina ta tsallake mutane ina wucewa.Rahma ta zauna tana tmbyata "menene? sai alkcn hawaye suka soma sin tiri akan fuskata. ckin kunnena tasa tana cewa shine baban shadad ko? naji sunansa munir tunda hashim ya ambata" Ban tanka taba, sai da nayi kukana ma'ishi, tun mutan dakin suna tmbyata har suka hkra. Rahma tace, fada min idan shine' nace shine me zaki masa? ta mike nace koma ki zauna" tare da riko ta. Na sauke numfashi Rahma barshi, abu daya nake son san menene dangantakarsu da abbkr? indai yan uwane to fa in sama da kasa zasu hadu ba zan zauna da shi ba, Rahma tace daina msalin nan babu kyau yanzun ki bari zan kirasu gashim anjima Na ce ki barsu kawai zan bncika a sannu, sukam su sagr mamakin hafsa ne ya cika su,sai dai shi hashim ya zargi wani abu.Lallai shadad yana matukar kama da munir ya dubi munir wanda ya kasa zaunawa yace zauna mana ranka ya dade, ga abnci, munir ya zauna bayan ya ciro hankici yana share zufa,sagr ya mika masa hannu suka gaisa, haka ma hshm. Nan dai suka juya hira,ya nuna sagr "wannan ne angon? Hashim yace a'a yana yola, kasan na fada maka mata 2 zaya aura. shadad na rike a hannun yaya umar, dawowarsu kenan daga gdan yaya umar din. yace kawu bari in je gurin antyna, tana can dakin? umar yace "Ehh don shigarsu dakin ne yAya umar ya fita shi da shadad sai yanzu suka dawo. ya shiga da sallama jikin sagr ya nufa yana me fadin Uncle ina antyna? sagr yace tana gda. munir ya tsurama yaron ido,gabanshi yana wata irn faduwa ya bi yaron da ido lkcn da yaron ya fita a guje. tamkar ya cafko yaron yakeji don ya sake kallonshi da kyau,ko kuma duk cikn firgicin ganin hafsa din ne? ya mike cikin tashin hnkali,yace to Hashim Allah yasanya alkhairi, nizan tafi. Hashim yace da sauri? munir yace em inada dan wani uzurine, suna fita yi masa rakiya sai waiwaye2 yake,ya shiga motarsa ya tada tafe yake yana zantuka shi kadai, tmbayr kansa yake" shon wannan yaron mai matukar kama da shi dan hafsa ne? cikin sane kenan ta haifa?a fili yace lallai zan amshi dana dubi yanda kaunarsa ta zirga ckin jinina,amma kuma.... ya doki kan styarin motar tare da cwa tab nasan za'ayi rigima,yanxun wama zan tunkara da wannan magnar? tunda iyayena ba wanda yasan zancen? ko gdansa yakasa zaune da tsaye,duk ya damu gashi badama ya fadawa matarsa. sai dai ya yanke shawarar dadynsu da zancen, Nikam ban da tursasawar Rahma bazan yi wani lalle ba,amma haka tasa sakinarmu da ummi suka nemo mai zanen fulawa ta yarfa min a hannuwa. tasiyo man shamfo sbd anwuce da akwatunana (lefa) dama kayan dangi daban suka kawo wai suddaje. don haka ba'a taba nawa ba,tayi min don tayi tayi nace bazani saloon ba, na manta da wani abn takaicin da rahma tamini tarkacen mata ne wai sai nasha. Nace matama gwara takwashe tarkacenta inba hakaba zatayi asarar kudinta, don zubarwa zayi, tace gashinan cikin jakata in naso naje nazubar, inkuma na shirya sha to inkirata taimin bayani yadda ake amfani dasu, nace kanki akeji, gdan yaya umar mukaje kwana, sam na kasa bacci, gaskia bansoba naga munnir sai naji nakara tsanar maza, Allah ya sani indai dan'uwan abkr ne toba zan zauna cikin zuri'arsuba, ke amarya tashin manta doguwar tafia ke garemu? Wanka kawai nayi don ina fashin sallah, na kintsa jikina sosai muka fita tare dasu ya umar, ummi da matar ya umar duk tare zamu tafi dasu, dangin inna duk tare muka tafi dasu, nida sakeena da rahma a motar hashim da sagir, harda shadad aka tafi, lallai yola akwai nisa, tun muna tafia ina hira har nai bacci dan bantaba doguwar tafia irin hakaba, bamu isaba sai gaf da magrib, tunda karfe 6 na safe, kuma wai haka dinma sai naji ana cewa munyi sauri, dankareren gate ne muka dosa, sai kace na gdan yari, muna shiga gdan dam da mutane haske ko'ina, mayafi naja na rufe fuskata, lkcn naji gdan yadauki guda anata fadin gasu nan sun iso, rahma ce take rungume dani, har zuwa kofar shiga tace, kishiga da kafar dama kiyi addu'a, hakan nayi, sannan aka zarce dani can dakin, nan da nan zugar dangin suka cika falon, har dakin da nake, sai fillanci ke tashi, daidaikune suke mgn da hausa irin wadda bata goge din nanba. wata ta duko kaina, amarya bude fuskarki muganki, ke kam wane irin kyaune dake har hamma yafita hayyacinsa danke? Na sake sunne kaina cikin cinyoyina, wata tace, nana ke kam baki ganta acikin hotunan kalanda ba? Tace nagani, sonake inganta afili, rahma tace, sai kingaji da ganinta, tunda nan zamu bar muku ita, ankawo kulolin abinci, shinkafa da miya da nama, sai kunun gyada da sauran drinks, suka dan rage nan muka shiga cin abinci, nikam wanka na mike zanyi, bayina acikin dakina yamin kyau, nafito na zura kayan bacci, sukuma suka shiga sallah, rahma tace, shine zakisa kayan bacci? Nace ina naga sabon dinki, tsofaffinma banzo dasuba, na saka katon hijabi, sukuma cikin daren nan suka hau yin jeren dakina, sun saka kujeru a falo ina juyosu suna tababa, anan za'asa, anan zaifi kyau, suka dawo daki suka hada gado, suka dibi na kicin sukaje suka jera wanda shima kenan falon, matsayina na yar talaka amma iyayena sunyi kokaro, suka hau gado suka kwanta nikuma nakwanta kan kafet dan nasaba da kwanan kasa, rahma tazo kusa dani takwanta, sai wayarta tashiga ruri, nace to masoya ga angonki nan, ta fito da wayar tana cewa, yanzun nanfa muka gama dashi, kurum sai naji tana cewa, ango_ango, munyi fushima, baka kira ba muna hanya, mun iso tuni ka sharemu, ina jiyo muryarshi .......
Chapter 15 · 0% Book details