← Book details Sanadin Boko Part 3 complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 19

Sashe 2

Sanadin Boko Part 3 complete Hausa Novel · about 8 min read

bana ganin kowa daga maman rahama sai sagir da rahama.shadad ma yana can gidan su maman rahama da mahaifiyarta. Hashim da sagir sun fita sun bar abubakar kwance yau har kwana 3, amma baiji son Hafsa ya girgiza daga zuciyarsa ba, sai ma son ganin halin da take ciki da yake. Tunda aka ce mashi bata da lafiya tana kwance a Asibitin. Yaji ranshi ya kasa kwanciya, gashi tun da yace masu sagir baya son jin labarinta suka daina zancenta. Dan haka bai san koyaya jikin nata yakeba yanzu. Ya mike jiki babu karfi yafita, da nurse suka ci karo yace mata wane daki ne aka kwantar da wata Hafsa? Ta nuna mishi ta wuce. Ya nufi gurin, ta window ya tsaya yana kalonta tana bacci. Ta rame matuka. Gadonta na jikin window ba kowa a dakin, tamkar ya shiga a fili yace, me yasa kika cuceni? Me yasa kika zama kazamar rijiya wanda kowane kazami zai jefa kazamar gugarsa? Ya lumshe ido tare da sauke ajiyar zuciya. Ina sonki Hafsa, ban taba ganin abin da nake so ba irinki. Ya juyawa window din baya, wasu kananan kwala masu dimi suka biyo gefen idon shi,kin cuceni. Ya sa hannu ya share idon sa, dai dai lokacin da ya hango su Hashim, nan take ya soma tafiya dan barin gurin. Sagir yace, ina kaje? Ko gurin Hafsa kaje? Tsaki yaja, inje in mata me? Na dai dan taka ne. Suka kalli juna sukayi murmushi, Sagir da Hashim. Sannan sagir yace, Abubakar ba‘a yiwa so miskilanci, ka nutsu a warware komai. Hashim yace, daga gurin Rahama muke, tayi mana bayanin gaskiyar lamari. Abubakar ya dubeshi da sauri ta taba aure ko? Tana tsokana tane dan na barta ko? Hashim yace a a bata taba aure ba Abubakar yaja tsaki. To ba zan saurareku ba, in bata taba aure ba ina ta samo yaro? Agurin karuwanci? Ya nufi cikin daki yana fadin ada na tsani inji an ce ta taba aure, duk da ina matuka son danta, amma yanzu har fata nike so nake inji an ce auran ta taba yi. Sagir yayi ma Hashim alama da hannu, wai ya kyale shi. Ni kam dama ina da tsohon ciwo na a jiki bai taso ba, sai yanzun da yaji ni a gadon asibiti. Yau in likita yace nan ne ciwo kaza ne, gobe sai yace har da kaza ma, yau da ya shugo kuma ya gama duba ni, wai zama asamin jini. Na bude ido da kyar, jini? Na fada a hankali, yace, eh mana, jininki ya tsotse, dama tunda kukazo baki da ishashen jini. Maman su Rahama tace, saya za‘ayi ne? Yace, eh to, da dai tana da wasu yan uwa haka sai su bata, in da wanda zai iya bata, don ba mu cika son siyan jini ba. Mama tace, to bari su shigo muji. Bayan yafita nace, mama wai wanene ke dawaibiya dani? Mama tace, to ni dai ban sani ba, ko wanene cikinsu? Oho! Ni dai likitan bai taba kawo kaza ba. Zai kawo magani, kuma zaizo ya dubaki, don haka bansan wanene ke daukar nauyinki ba. Lokacin da sagir suka shugo da hashim, mama tace likita yace sai an sa jini a jikinta,suka ce, sagir yayi mana bayani, anjuma zamuzo a gwada jininmu. Nace nifa zanfi son ku barni in mutu. Mama tace, kuje ku kyaleta. Aikinta kenan zancen mutuwa, kuma nasan da zataga mutuwa guduwa zatayi. Su sagir suka sa dariya, ina so in tambaya shi wanan dan uwa Abubakar dama a nan yake in kuma tare suka zo in Abubakar din? Ina son sanin halin da yake ciki, ina ma wayata? Bansan cewa a fili nayi yambayar ba, sai da naji mama tace. Wayarki tana hannun rahama, ta kira gurin aiki ma ta fada musu ma. Shuru nayi ina tunanin tare da fatan bataji sauran zantukar zuciyar tawa ba. Suna fita suka nufi gun Abubakar, can kusan minti 30 likita ya shugo ya dubi Abubakar yace mishi ina ganin kai zuwa gobe zamu sallame ka. Yace, Allah ya kaimu. Ya dube Sagir, ku kuma muje a gwada jininku din. Abubakar ya dubesu da sauri, lafiya? Hashim yace Hafsat tana bukatar jini. Abubakar ya tsurawa Hashim ido, jini kuma? Kikita yace kwarai kuwa. Daga nan bai sake magana ba, ya dauki wayarshi yana dan danawa, amma cikin zuciyarshi a rikice take, kadafa ta mutu! Suna fita yaga sun nufi gefab dibar jini da gwajin su, nan da nan ya nufi dakin da take. Bai shiga ba ta window ya tsaya yana lekenta. Tana kwance, amma da alama idonta biyu. Rahama tana zaune tana cin abinci. Yayi tamkar ya shiga, amma sai ya fasa. Ya fita harabar asibitin ya nemi guri ya zauna karkashin wata bishiya. Ya saka fiskarshi cikin tafukan nannayenshi, yanzu ya gama gane cewa soyayayarsu da Hafsa wata mai wahalar fassara ce. Muhimmiyace kuma hamshakiya. Ba zai taba daina sonta ba har abada. Menene mafita? Wata zuciyar tace mafita kenan, ka aureta. Hashim ya fada a bayan shi. Abubakar ya dago kai, idonshi jajir. Hashim yace, don Allah ka sama kanka salama, kana son Hafsat ka aureta. Abubakar yace, ba zan iya kwantar da hankalina ba, kasan kuma aure da zargi yana bata aure ko? Please, bar maganar aurenan ba zan iya ba. Ya mike ya bar Hashim a gurin, cikin ta kaicin rashin sauraran shi da Abubakar baiyi ba. Kai-tsaye ofishin likita ya nufa, yana zaune kan katon tabirin shi yana ta hada wasu fayal. Ya dubi abubakar. Ranka ya dade ya kakara gyagijiwa kenan? Abubakar ya zauna kan kujera batare da ya nemi iziniba. Ya dubi likitan. Likita wai me ke damun yarinyar nanme? Likita ya tatara hankalin shi gurin Abubakar, kana nufin sister dinka? Abubakar yace, eh. Likita yace, gaskiya bata da lafiyap gaban Abubakar ya fadi. Me ke damunta? Likita yace, tanada hawan jini, ga zuciyarta ta dan tabu, typoid ma tana dashi, dan muna zaton shinema ya tsotse jininta. Yanzu haka tana bukatar jini, muna gwada na sauran yan uwanka ba zai yi ba, amma da irin naka ne zaka iya ba kowa jini. Sannan mun sami jininta dan da ya hau ya sauka. Abubakar yace, likita ina so kudibi jinina kusa mata. Likita yace, kaima baka da lafiya, don haka ba zamu dibar maka jini ba. Yace, bani da ishashen jinin ne? Likita yace, kana da jini don jini. Yace, to a diba saboda ko ba ku diba ba zanje wani gurin su dibain kawo,in ma shi kenan ya rage min zan hakura ita ta rayu.shuru likitan yayi, can yace in na diba zan fasa sallamarka gobe. Yace dama ko ka sallameni sai na jira ta. Likita yace, matarka ce? Abubakar yace, ina fatan haka in Allah yaso. Sanan don Allah kada ka fada ma yan uwa na nine zan bada jini, shi kuma abu na gaba, inaso kayi mata gwajin (H I V) don Allah. Likita yace, in sha Allahu zanyi. Yace to jinin yaushe za‘a diba? Likita yace, gobe ne. Yace to in Allah ya kaimu sai adiba. Amma jikin nata yana sauki ko likita? Ya cigaba don Allah aluran min da ita sosai. Likita yace, tunda ka fadamin ko ita wacece to za a duba ta fiye da da. Yace to na gode, game da kudi ba matsala, na fada maka ai. Yace, nasan haka. Washegari sai dai sukaga basu ganshi ba da safe. An dibi leda 2 suka tace, duk da sunce ba komai a cikin sa. Aka bashi magun guna ya sha, suka rubuta mashi wani tare kuma da ya rika cin abubuwan kara jini tare da shan na kara ruwa Hashim yaji mamakin ganin shi sharkaf a kwance, ba wai ciwo bane, a a jikinshi a sanyaye yace, ina kaje tun dazu? Ya kali Hashim na dan fita na motsa jiki, shine nagaji. Hashim yace mai makon kayi mana magana mufita tare? Har nace kodai kaje ka bada jinin ne? Na tambayi likita yace an siyo jinin. Abubakar ya daure fuska, in bata jini a kan me? Ko su samu ko kada susamu ina ruwana? Hashim yace matsalaka kenan kin fahimta, kana son yarinya har a gidan karuwai ana dauko mace a aureta bare ita wanan da kadara ta fada mata. Abubakar yace, kada ka daurewa karya gindi, wanan ba kaddara bace. Ita kadara ma kanta mace ta kama karuwanci sanan ace kaddara? Hashim yace, zan so ka aje wanan kishin ka saurara muyi maganar. Abubakar yace, amma tuni na fada maka banson jin ko? Haushi ya kama hashim kada ka so zancenta, amma ka iya labewa ka lekata ko? Abubakar yace me zan leka? Hashim yace, zakaga kamar banganka ba ko? Ya tashi ya nufi dakin Hafsa, lokacin har jinin Abubakar ya soma diga cikin nata. AL‘amarin so babu karya acikin shi, amma shi amma shi kanshi Abubakar yana al‘ajabin irin son da yake ma Hafsa. Likita ya tabatar bata dauke da cutar kanjamau, domin tunda abubakar yace ayi mata gwajin (H I V) hankalinshi yafi da tashi. Kamar jinin take jira, gari na wayewa ta soma samun sauki, har tana tashi zaune, kuma har da sallah. Mama da Rahama suna tayi mata tsiya dama jini kike bukata, gashi har kin gyare. Itama ta danyi yake, tace Rahama ina wayata? Rahama tatashi ta balle jakar ta ciro wayar tana cewa. Ke wayarki da ita da babu duk daya ne. Na dubeta da alamun karin bayani. Tace, to tun da natafi da wayar nan babu wanda ya kira ki. Na amsa ba tare da ce mata uffan ba, sako nasamu kaina da rubutawa. (ABUBAKAR SADEEQ) NASO IN MUTU SABODA NA SAN BA ZAN TABA SAMUNKA BA, KA YAFE NI. INA SO KA SANI CEWA INA MATUKAR SONKA, KUMA HAR IN KOMA GA ALLAH BA ZAN DAINA SONKA BA. DON ALLAH KADA KA MANTA DANI, DUK LOKACIN DA KA TUMONI KA MIN ADU‘A ******** natura masa ne zan katse sakon ashe yariga yaje. A zatonshi fadi ce, don kullun zata kira shi sau kusan 4 banda tex na kalaman so da kauna tare da bege. Sai dai shi bai taba jin haka ya burge shi ba ko acikin ranshi, sai dai bai taba nuna mata bai ji dadi ba. Sai kusan minti goma sha
Chapter 2 · 0% Book details