Sashe 1
Sanadin Boko Part 3 complete Hausa Novel · about 8 min read
Sanadin Boko 3-01 Posted by ANaM Dorayi on 11:29 PM, 19-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Jikin abubakar sai bari yake, lokacin da suka shigo mota shida Hashim ne a baya, yayin da sagir ke tuki. Yace, innalillahi wa ina ilaihi raji'un, lallai na fada cikin jaraba. Dama Hafsat karuwa ce? Ya kifa kanshi ta baya. Hashim yace cool down my broos. Ka bi ahankali. Yace, Hashim daina cewa inbi a hankali, ka dai san promise da nayi dasu lamido kafin su yarda in aure ta, kuma ko yanzu ina kar kashin dokokin ne. Me kake zato in suka tashi bincike suka gano wanan matsalar? Sagir yace, amma sai dai in da ne tayi karuwancin, yanzu dai bisa tarin alamu batayin harkar. Abubakar yace, zazzabi nakejifa, ku kaini Asibiti. Hashim yace please Hamma kayi cooling mind dinka mana, wane irin Asibiti kuma? Yace Sagir dan Allah muje zazzabi nake ji. Sagir yace naso muje gurin Rahama, zamuji gaskiyar magana. Abubakar yace please, ku daina min zancenta, bana sonta, ba zan auri karuwa ba,zuwa wani lokaci bacci ya dauke shi, suka je office din likitan dan amsa kiran shi. Bayan sun zauna ya dube su a natse yace, ya shiga wata damuwa ne wadda lokaci 1 ta kumbura zuciyarsa, kokuma ya tsorata. Ya dan saurara, kafin ya cigaba da ce musu zai kwanta na dan kwanaki don kauce ma abin da zai biyo baya, sanan dole ne ya kaucema duk wani abu da ka iya tashin hankalinsa. Suka ce, to in sha Allahu za‘a kula. Suka dawo gurin shi suna dan tau tauna maganar Hafsat. Sagir yace, nayi zaton Hafsat tayi haka ne don Abubakar ya rabu da ita. Hashim yace, anya? Ni kam ina ganin rabon ba za akai mana bara gurbi cikin zuri‘a bane. Iyayenmu ba zasu amince da wanan auren ba. Sagir yace, amma Abubakar zai shiga wani hali in kayi la‘akari da matsanancin son da yake mata, dube shi fa lokaci kan kani yanda ya zama? Baka ganin zai iya mutuwa, zai fi masa sauki, in dai akan ya auri karuwa ne,zuri‘ar mu suna da tsuri, auran shinnan shine na farko da za‘ayi auren bare, kuma in yazo da matsala zasu kafa shi hujja ga yan baya. Sagir yace, hakane. Kusan 11 saura sagir yaje mota ya fito musu da dardumar sallah, sannan ya tafi taredacewa sai dasafe. Kusan karfe 4 dare Abubakar ya farka, jikinshi lakwas yake jin shi, kansa da kirjinsa kuwa sun masa nauyi. Ya dora hannu a kirjinsa, sam baya san tuno abin da ya faru ko kadan. Amma zuciyarsa ba zata iya amincewaba ko na sakon. A fili ya furta Hafsat! Hafsat!! Karuwa!!! Yai juyi ya kwanta akan hannun damansa. Allah ya cire min sonta, don ina da matukar kishi a kanta. Tabbas yana kishinta dayawa, da ya tuno ta taba aure sai yaji kuna a ransa, ina ma shine mijinta na fari! To ashe ma ba haka bane, ita Dattice, Bolace da kowane kazamin zai zo yazuba shararsa. Tir! Tir!! Da shi ya aureta. Ya sake juyawa. Tabbas nasan cewa idan ina son abu ina yimasa so tamkar rai, amma in naga zai bani matsala ina hakura dashi, nasan zuwa jibi zanji ta fita daga raina.Da wadannan tunane tunanen ya jiyo tada sallah daga massallacin da ke cikin Asibitin ya kai hannu ya dafa kan Hashim wanda ya jingina kansa bisa gadon yana bacci a zaune kan kujere Hashim ya bude ido Abubakar ya ce cikin fulatanci an kira sallah shima ya yunkura zai tashi sai yaji jiri yana diban shi ya komaya zauna bayan fitan Hashim da kyar ya lallaba ya tashi ya nufi toilet ruwa ya sakar ma jikinshi kafin yayi alwala sallar ma a zaune yayi ta don bazai iya tsayuwa ba kafin ya idar zazzabi ya rufe shi da likitan ya shigo ya yita masifa meyasa zai watsa ma jikin shi ruwan sanyi da safen nan? Lokacin da sagir ya isa gida Rahama na zaune, don duk ta damu sunyi dare. Ya shigo jiki babu karfi, ta dubeshi Hafsat takiko? Ya zauna yace, dauko mun ruwa in sha. Ta kawo tare da tsiyaya masa a kofi ya sha, sannan ya dube ta. Dama Hafsat ba yan uwanku bane? Tace, me kagani? Yace, ta fada mana cewa ita karuwa ce, zaman kanta takeyi. Rahama ta zabga salati, mai ya kai Hafsat yiwa kanta shairi? Ta rike haba cikin al‘ajabi. Yace, ga dai Abubakar can a gadon asibiti sakamakon furicin da tayi. Rahama tace, kuma? Yace, to wai menene labarinta? Nasan kinsan komai tunda tayi wanan furucin yanzu ke kadaice zaki wanke ta a gurin Abubakar, domin ance magana zarar bunu, in ta fito ta fito kenan. Rahama tace, gobe zaka yarje min inje gidanta dan muyi magana, idan ta bani izini to zakuji komai, ina zaton tace haka ne don ya rabu da ita. Sagir yace, in ko sun rabu zasu sha wahala, don itama ko da bansani ba yanzun haka tana cikin damuwa. Rahama ta shigo gidan, shadad tagani kan tabarma lamo da alamu yunwa yake ji, ko kuma damuwa bai da lfy. Tace, yau babu makaranta ne? Ina antyn taka? Yace, tana ciki. Ganin halin da take ciki ya tsorata Rahama, har tadau waya ta kira sagir, tace ta tashi su tafi asibiti, tace a a ta bari mutuwa zatayi, amma ga amanar yaron ta nan. Tace, in kinje kaduna inda na fada miki lokacin da nake baki lbrina, zaki sami lbr iyaye na, ko da baki samesu ba kice suyafe mun. Ki nuna musu dana shima ya san dangina. Rahama tace, haba hafsy, kitashi wanan ba ciwon mutuwa bane, ciwon son Abubakar ne, kuma in sha Allahu zaki sameshi. Ta fita, sagir kazo kayi mata magana. Da kyar ta yarda ta bisu saboda magiyar da sagir ke yi mata. Asibitin da yake suka kaita, likita ya dubani wai nima zuciyata ta motsa, kuma jinina ya hau.daga nan sagir ya tafi dakin da Abubakar ke kwance ya sami Hashim na waya, shi kuma yana kwance. Yaba hashim hannu suka gaisa. Sanan ya nufi gun abubakar bashi hannu shima suka gaisa. Duk da cewa abubakar din da kyar yake magana, yace Sagir kasa Rahama ta kawoma Hashim abun karyawa, saboda yana da ulser. Sagir yace, Rahama tana gurin Hafsa a nan asibiti, ta je tasamu halin da take ciki takirani muka kawota nan. Da sauri ya mike me ya sameta? Sai kuma yaja tsaki ya koma ya kwanta. Sagir suka bari suje suyi take away. A hanya sagir yake ba hashim labarin abin da ya faru har suka kawo hafsa nan . Hashim yace yanda za‘ayi yanzu zamu samu Rahama ta bamu duk abin da ya faru. Sagir yace, kaji batu. Ko kallon inda suka ajeyi abincin da suka suyo mashi bai ma yiba, ya damu kwarai. Wayarshi dake hanun hashim tayi kara, hashim din ne ya dauka. Abba ne. Yace tuk da kuka kiramu da kuka sauka har yanzu shuru, ko lafiya? Hashim yace, Abba akwai matsala fa. Da sauri Abubakar ya duro dakarfin da bai san yana dashi ba, a hankali yace kada ka fada mashi komai game da Hafsa please. Hashim yace, abba kace me? Bana ji? Abba yace me ya faru nace, kun samu wata matsala ne game da yarinyar? Hashim yace, Abubakar ne bashi da lafiya, yanzu haka anbamu gado muna asibiti. Subuhanalilahi!Me yasameshi har haka? To likitan dai yace ciwon zuciya ne, zuciya ne e dan kumbura. Inji hashim. Abba yace, ikon Allah! In sha‘Allahu gobe muna zuwa. Hashim yace to Abba sai kunzo. Abubakar yace kace da sauki, ni kam ba sai sunzo ba. Duk da haka Abba yace zasuzo. Zuciya ai ba abun wasa bane, da suka gama wayar Abubakar yace, kai dai banza ne, wa ya fadanmaka ana fadin ciwo? Hashim yace, da fa zan fadan mishi matsalar Hafsa ne kace a a ba dole in fada mishi ciwo ba, tunda bani da mafita na riga dai na fara fada.Abubakar yace, ko sunzo kada kayi musu maganar hafsa, na san yanda zan warware matsalar, domin insukaji Hafsat karuwace to fa zasu kara reke wanan al‘adar da hannu biyu. Kaga kokarina na baya ya zama banza, har yan gaba ba zasu amfana da komai ba. Amma in munyi shuru koni banyi ba kannan mu zasu iya yi. Hashim yace, shikenan. Amma itama zamuyi bincike. Abubakar ya kalleshi da sauri, zakuyi binciken me? Bana son wani bincike, ni na hakura da ita. Hashim yace, gama malam bana son gadama, yanzu bagaka a gadon asibiti kana ciwon so ba? Abubakar yace, inji uban wa yace maka ciwon so ne? Ai ni tun jiya na daina sonta, ciwon daga Allah ne, sai kace wani wawa zan tsaya ciwo akam mace kamar a film? Film din ma na indiya? Sagir da ke jinsu yayi dariya tare da cewa, kai da ita duk cutar so ke damun ku, don haka ku nutsu zamuyi bincike. Abubakar ya hade rai kunsan Allah, wlh na fasa. Hashim yace harda rantsuwa? Abubakar yayi tsaki ya kwanta. Washegari su Abba suka iso su 5, harda dada, amma yan da suka ganshi duk sun damu. Bawai jikinsa ya tsananta bane, amma yana cikin damuwa. Likita ya fada musu matsalar zuciya tana da girma, subishi a hankali, kuma damuwar da yake ciki suyi kokari su kau da ita, sukace basa zaton yana cikin wata damuwa, aMMA zasu zauna dashi. Abba da baffansa guda 2 da dada da kuma gogonsu kuma surukarsa, wato gogo jami, suka sashi gaba bayan sun gama cin abincinda Rahama ta girka musu. Sukace ya sanar dasu damuwar shi, nuna musu yayi ba komai, ciwo ne kawai.Goggo jami tace, ina hafsatun? Da sauri yace taje kaduna, dama nan ai karatu tazo, to bamu sameta ba, amma zata zo gobe don ban fada mata bani da lafiya ba. Hashim ya saki baki yana kalon Abubakar, amma bai ce komai ba. Sagir shine ya sauke su yayi dawainiya dasu. Su dada gidan Rahama suka kwana, yayin da maman rahama ta zauna dani. Dada ke tam bayan rahama game da halayane, wai ance ni kawarta ce. Rahama tace tana da tabbacin ina da halaye masu kyau da biyayya. Washegari suka juya tunda yana tare da Hashim, ni kam ban san yana Asibitin bama,