← Book details Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 36

Sashe 8

Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau sopy anacikin farin cikin zuwan uncle kabeer,, sai hidimar girka masa abinci takeyi, inna taji dad'in yanda taga tasaki jikinta yau tana walwala, dan tunda abinnan yafaru basa ganin dariyar sopy,
Amma yau daka kalleta zaka gano farinciki a tareda ita.
"Sai wajen k'arfe biyu uncle kabeer ya iso, shima yayi farincikin ganin yanda jikin sopy yayi k'yau saidai kawai ramar datayine, tana zaune kusada uncle kabeer dake cin abincin data dafa masa,, takalle sa uncle kana ganin baba zaiyyarda da k'udirinmu kuwa? ?? Uncle kabeer ya ce, "aii dama tunda naga farincikinki ya yauta nasan akan maganar damukayine", karki damu zanyi iya k'ok'arina tayanda zai fahimceni, insha ALLAHU zai amince.
Sopy ta ce, "danayi farinciki mai tarin yawa uncle, nasan hakan zaik'ara nisanta zuciyata daga damuwar data tsinci kanta.
Uncle kabeer yay murmushi hakane my daughter! Insha ALLAHU nan gaba kad'an komai zai zama labari, kedai kiyi k'ok'arin cika min burina,, dan yanzu zaki shirya muje makarantarku mu amso exam d'inki.
Cikin zumud'i ta ce, "angama my dear uncle! Inna dai tanajinsu bata tankaba, dan bata fahimci inda zancen nasu yadosaba.

Sun karb'o sakamakon jarabawar saidai sopy batayi k'ok'ari a WAEC nataba.
Uncle kabeer ya ce, "sopy ya akayi haka tafarune?? Sopy tad'an sosa gefen wuyanta, wlhy uncle! Sannan ina cikin wani yanayine!!
Uncle yay murmushi sannan kina cikin shauk'in son Abdul ko?? "Tasa hanu ta rufe fuskarta tana fad'in "kai uncle".
Ya ce, "i, mana hakane", amma babu damuwa saimuyi amfani da NECO kawai, dama mun gama magana da abokina,, shima malamine a "B,U,K", nasan zai taimaka mana sosai.
To uncle nagode sosai ALLAH yabiya ka kaidai!! Yay murmushi to amin sopy na.

Sai dare uncle kabeer yasamu zama da baba, bayan sun gaisa ya ce, "yaya dama maganar yarinyar nan ne yakawoni.
Baba ya ce, "wace yarinya kenan??
Uncle yagyara zama, yaya yarinyar dazan aura!
Baba ya ce, "to miya faru da ita??
Babu komai yaya babanta ne , dama ya rok'eni akan dan ALLAH nabarta ta k'are karatunta, tunda saura shekara d'aya kacal, to nima sainaga hakan zai taimaka minma na k'arasa gidana, amma yaka gani??
Baba yaja numfashi, to idan haka yafi alkairi ALLAH ya tabbar abba, mudai kullum addu'ar fatan alkairi muke maka, da fatan gamawa lafiya, dan kai yaron kirkine, nak'agu naga ka ajiye iyali kaima.
Uncle kabeer yay murmushi karka damu yaya insha ALLAH zanyi adai k'ara tayamu da addu'a,, sai dai yaya bayannan inada wata buk'ata awajenka!! Inhar ban takuraka ba??
Baba ya murmusa karka damu mai sunan baba fad'amin buk'atarka indai batafi k'arfinaba zan yi maka ita.
Uncle ya ce, "batafi k'arfin kaba yaya! " dama dan ALLAH ina son kayarje min namaida safiyya makaranta, dan wannan zaman nata bashida wani amfani, karatu zai matuk'ar taimaka mata wajen mance abubuwan dasuka faru abaya..................✍🏻

💕Bily💕
💕💕Mrs Abdus'salam💕💕💕
💕I LOVE YOU MY FAN's💕💕
💕
[12/19, 7:24 PM] mrs bilkisu: 15~October ~2016

🔷🔹NI DA AMINIYATA 🔹🔷

NA BILKISA IBRAHIM 💕

🔶🔸1⃣5⃣🔸🔶

...............Baba yaja numfashi, abba ban katse maka hanzariba, amma da dai anhak'ura da karatunnan hakanan, tunda ansamu na zaman duniya, sai kuma ayi aure.
Uncle ya ce, "hakane yaya, amma yanzu naga bawani tsayye bane ahannu, amma dazaman banzar gara ace karatu takeyi,, kotana karatun tasamu miji saitayi aurenta.
Baba ya kalli inna, to hajara kinji abinda abba ya ce, "amma ya kika gani??
Inna tai dariya, malam nikam banida shakku akan babnmu, dan haka kabashi dama, nima inaga hakan zai taimakawa safiyya wajen mance wasu abubuwan.
Baba ya ce, "to akira safiyya muji ta bakinta"
Uncle yay murmushi karka damu yaya indai safiyyace mungama magana da'ita.
To, to, kace dama saida kuka gama shawararku sannan aka tuna damu! Dariya sosai uncle yakeyi "cikin dariya ya ce, "A'a yaya mu mun isa; nan dai sukayita hirarsu da wasa da dariya.

TUNATARWA:- inaso naja hankalin iyaye akan ilimin 'ya'yansu, mafi yawan iyaye sukan d'auki ilimin 'ya'ya mata ba'abu mai muhimman ciba,, ni anawa ganin ilimin d'iya mace yafi na kowanne muhimmanci, karku manta uwa itake bada tarbiyya, kuma yara suna tashi ne da harshen mahaifiya, kunga kuwa ilimin d'iya mace yanada muhimmanci matuk'a,, dan zata zama foundetion na ilimin 'ya'yanta,, wannanma kad'ai ya isa yazama abu mai muhimmanci ga bawa mace ilimi,, sannan ko a gidan aure zakaga mace mai ilimi tafi kowa iya rik'e miji da tattalinsa,, dan haka mubama 'ya'yanmu mata ilim addini dana zamani,, ALLAH YASA MU GANE.

UNCLE kabeer yanata k'ok'ari wajen nemawa sopy Admission a (BUK ) da taimakon wani abokinsa aka dace,, dakansa yaymata komai.
To ALHAMDULILLAH komai dai ya kammala,, ranar monday sopy zata fara zuwa makaranta,, 😅dan haka tafi kowa fareenciki,, harta k'agara ranar tazo.

Su dai su inna sunata yima sopy nasiha, akan tazama mace tagari mai rik'e mutuncinta da darajarta,, idan ance 'ya mace taje tayi ilimi, bawai ananufin taje tayi iskanciba,, dan dayawa 'yan uwa mata idan suka samu saken zuwa nema ilimi,, sukan d'auka sun samu wayewa daganan sai afara iskanci,, kaiconmu wlhy 'yan uwana mata, har yanzu wasunmu basu fahimci miye wayewaba dayawanmu muna jahiltar wayewa,, ballagar mace wadda ta maida kanta akuya ba ita bace wayayyiyaba,, wanna itace bagidajiya jahila,, mace mai kamunkai da girman kai awajen maza marasa tarbiyya,, mai adiini itace wayayyiyar mace, kuma suma mazan sunfi sonta,, zakaga duk iskancin namiji da mugun halinsa yana burin auren mace tagari, kodashi bai kasance miji nagariba, to 'yan uwana ya kama ta mu gyara, kodan cin ribar rayuwarmu, ALLAH dai yasa mugane.
Su inna dai sunyima sopy nasihohi masu ratsa jiki da zuciya,, sunkuma yimata fatan alkairi da samun nasara arayuwa.
Saboda yanayin rayuwa,, sai uncle kabeer ya nema mata gurin zama a hostel, dan kar wataran kud'in mota ya gagareta,, itama hakan yayi mata dad'i, dan zaman anguwar yana d'an sata tayita tuna wasu abubuwan,, kuma idan tafita sai mutane suyita kallonta,

wasuma har nunata sukeyi, to, tasan idan tayi nisa da anguwar zata sake, ta kuma manta da abubuwan dasuka faru abaya.

Ku kasance dani akoda yaushe, ina muku fatan alkairi ...................✍🏻

💕Bily💕
💕💕Mrs Abdus'salam💕💕💕
💕I LOVE YOU MY FAN's💕💕
💕
16~October ~2016

🔷🔹NI DA AMINIYATA 🔹🔷

NA BILKISA IBRAHIM 💕

🔶🔸1⃣6⃣🔸🔶

.............Sopy ana makaranta, komai yana tafiya yanda takeso, sai dai tak'i sakin jiki da kowacce k'awa, duk da ana nuna mata anabuk'atar yin k'awance da'ita, bakamar wata zaliha, itadai sopy tana burgeta, sai dai sopyn tak'i bata fuskar dazata kusanceta, itakam sopy tana tsoron makirci irin nad'an adam ne, dan wadda ta yarda da ita, ta amincewa ita tafara saka mata shakku game da halayen d'an adam, wannan yasa take nisantar 'yammatan makarantar, sai dai tadage tana fahemtar abinda ake koya musu, kuma yanayin tasiri arayuwarta da kuma alk'awarin data d'aukarwa kanta da uncle kabeer.
Yau tanada lectures d'in safe, dan haka ta tashi tayi shirinta, cikin siket da riga na atanfa jaa da kore, tad'akko fareen hijjabi har k'asa tasaka, tad'an fesa turare mai sauk'in k'amshi, dukda bawata kwaliya tayiba tayi k'yau, dan sopy tanada k'yau irin wanda in kacika kallonta zai k'ara k'ayatar dakai, dukda bak'ace bak'inta yanada k'yawun kallo, gata da jiki maik'yau, irin wanda mutane sukan kirashi karuwan jiki, dolene idan kaga surar sopy komin ustazan cinka ka k'yasa, dan haka koda yaushe takan sance cikin hijjab, saboda idan har tasaka gyale tafita sai tasamu samari samada goma sunce suna sonta, wasukuma kwarjinin ta yake hanasu furtawa.
Tafito kafad'arta rataye da jar jakka, tafiya take cikin nutsuwa kanta ak'asa, tad'an kalli agogon hannunta mai sauk'in kud'i, tad'an tab'e bakinta, kai barima nazauna anan tunda munada sauran lokaci.
Tana nan zaune, saitaga d'alibai nata saurin shiga aji,wasuma harda d'an gudu, ita dai kallonsu takeyi, amma batayi wani yink'urin tashiba, zaliha tak'araso tana fad'in "lallai safiyya kina ganin kowa yana k'ok'arin shiga aji, amma ke kina zaune, yau munada lectures da "uncle G" kuma idan har yariga ki shiga aji tofa "k" bazai barki kishigaba......tak'arasa fad'a tana k'ok'arin tafiya, kafin sopy tace,"wani abu tuni zaliha takai k'ofar class.
Sopy tamik'e itama tanufi class d'in sai dai kash tana kaiwa ga k'ofar ajin shikuma malamin da zaliha takira uncle G yashiga.
Sopy ta tsaya cak abakin k'ofa, ta daure ta ce, "malam good morning!
Saida yay mata wani kallo na rainin hankali, sannan ya ce, "morning! da ganan yaja bakinsa yay shiru.
Sopy tai tsaye abakin k'ofa domin bai bata izinin shigaba, tana nan tsaye wasu 'yammata suka k'araso suma, d'aya acikinsu ta ce, "A'isha yaukam munzo arashin sa'a uncle G!! yarigamu shiga, wadda aka kira A'isha ta tab'e baki, ki ce, "sarkin 'yan girman kai yashiga, nikam wannan malami bansan miya d'auki kansaba???
Sopy dai tana tsaye tana jinsu, sai dai zuciyarta cike da tambayoyi, akan toshi wannan malamin wayeshi??? Ita dai yau kwananta hud'u a school d'innan, amma bai tab'a shiga a jinsu ba sai yau, to shikuma waye????
Ta maida kallonta gareshi, yana sanye da wani farin yadi mai laushi, rigar da kad'an ta wuce d'uwawunsa,k'afarsa sanye da bak'in takalmi,hakama hannunsa yana d'aure da bak'in agogo,, idanunsa cikin farin gilas siriri,, dukda dukannin kayan dake jikinsa bawasu masu tsada bane, amma shikam sun zauna dai dai da tsarin halittarsa.
Dogone amma ba canba, amma tabbas baza'a kirashi gajereba,bak'ine amma mai haske, yanada manyan idanu farare tas, wad'anda saboda haskensu har akan iya ganinsu tacikin kwalbar dake idonsa👓, dan har wani k'yalli sukeyi, kumatunsa zagaye yake da bak'in gashi sid'ik wanda ake kira saje, hakama bakinsa zuwa gemunsa shima zagaye yake da bak'in gashin, kansa babu suma mai yawa dan da'alama yanayin aski saidai ba irin tal tal d'innanba, domin akwai gashi kwance akansa bak'i sid'ik yasha mai sai k'yalli yakeyi, yanada d'an jiki dankuwa baza'a kirashi siririba,amma jikinsa yay masa k'yau.
Yad'an juyo yana kallon su sopy dake waje, yaji ajikinsa tabbas ana kallonsa, sopy tayi saurin d'auke idonta daga kallonsa, shima saiya d'an tab'e baki yacigaba da bawa d'alibai darasi akan English domin shi malamin turancine.
Yagama lecture d'insa, harda yin test, yazo fita sopy tamatsa gefe tabashi hanya, ko kallon inda suke baiyiba ya wuce abinsa, d'aya acikin 'yammatan nan uku taja tsaki, kai wannan gay d'in akwai rainin hankali saikace d'an wani da wata.
Chapter 8 · 0% Book details