← Book details Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 36

Sashe 14

Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

............Safiyya! kam tunda uncle G! Yafita tashiga aji tazauna zuciyarta cike da tunani iri iri, koda zaliha! ta zauna kusada ita tana mata surutun data saba bata kulataba, saima ta d'akko wayarta tana catin da uncle kabeer.
Wani sak'o yashigo amma saitayi burus dashi, dan azatonta wanine ya d'auki nomber d'inta a group dan haka wasu keyi, musamman ma samari.
Shigowar wani malami yasa ta daina catin d'in, tanatsu domin d'aukar lecture.
Bayan fitarsa batada wata lecture sai k'arfe uku, dan haka tanufi library domin wani bincike.
Ta shak'i wani k'amshi wanda tabbas tasan mai shi, amma saita share tacigaba da karatunta, jin k'amshin ya yawaita agurin yasata juyowa domin tabbatar da zarginta.
Uncle G! Ne tsaye yana binciken wasu books saidai da alama bai gantaba, dan haka tak'ara k'asa da kai, bata buk'atar yaganta.
sai dai ta makaro, domin kuwa tunda ya shigo da ita yafara tozali, ya basar ne kawai yanuna bai gantaba.
Cikin takunsa na masu aji da gayu yanufo inda take zaune, hannu biyu yasa yadafe tebir d'in gabanta, tareda fad'in Assalamu alaiki?.
Da sauri tad'ago dan batai tsammanin zuwansa ba.
Ya ce, "bakijin sallama ??.
Cikin rawar murya ta amsa, ta d'ora da gaisheshi.
Yaja kujera ya zauna yana fad'in ya ykk?
Sopy taja numfashi tana fad'in lfy law.
Ya ce, "good".
Kafin yayi magana wayarsa ta hau k'ara alamun kira, ya cirota daga aljihun gaban rigarsa ya amsa.
Saida yagama wayarsa sannan yadawo da dubansa gareta, yayinda wasu d'alibai dake library d'in suke kallonsu.
Ya mik'e yana fad'in kisameni a office inaso muyi wata magana dake, domin inaso naje gida wannan week d'in akan maganar aurenmu!!.
Da sauri ta kalleshi, shima kallonta yakeyi, dan haka ta maida kanta k'asa, ya kwashi wasu takardunta data ajiye, ta daure ta ce, "uncle zanshiga lecture dasune fa.
Yatafi yana fad'in nasani idan kinzo saiki karb'a ina jiranki karki b'ata min lokaci.
Sopy ta dafe kai tana fad'in nashiga uku ni safiyya mutumin nan fa yafara shiga min hanci, yakamata na face shi, kanta ta maida ga karatu amma saita kasa karatun dole ta mik'e tafice, tadad'e tana tunanin zuwa office d'insa, dan gsky bataso azargeta akan yawan shiga office d'insa.
Wayarta ta hau wringing, tad'aga tana mita.
Muryar uncle G! Taji yana fad'in ina jiranki fa!!.
Kafin ta ce, "wani abu ya yanke wayar, ta dafe kai tana fad'in ya salam, dole ta daure ta nufi office d'in.
Ta kwankwasa, ya ce, "shigo mana, dan yasan ita ce!!.
Da sallama tashiga kanta ak'asa, yad'ago yana kallonta batareda ya ce komaiba.
Jin yayi shiru, ta ce, "gani!!."
Ya ce, "aii naganki, ya maida kansa kan abinda yakeyi.
Sopy tabishi da kallo cikin takaici, takardunta yake dubawa, taja k'aramin tsaki amma baiji ba, a zuciyarta ta ce, "kaidai kana son sakani cikin matsala, banason wani yazargeni wlhy.
Ya d'ago yana fad'in wai bazaki zaunaba ne??.
Ta ce, "nanma ya isa.
Ya ce, "okey nima bari nataso tunda yau tsayuwar kike sha'awa.
Kafin ta ce wani abu yataso, ya k'araso inda take tsaye, jingina yayi ajikin bango ya hard'e hannayen sa a k'irji, ya dasa mata fararen idanunsa manya masu yalwar gashi.
Ta k'ara k'asa da kanta dan ganin irin kallon k'urullar dayake mata, ya murmusa dan ganin yanda taketa sinne kai kamar wadda tayi k'arya, ya gyara tsayuwarsa, sopy!! Wai sai yaushe zaki kalli cikin idanuna ne, kunyarki tayi yawa fa.
Hannu tasa ta rufe fuskarta.
Yay dariya tareda fad'in okey to shikenan, dama inason nasar dake jiya da daddare naje gidanku!!.
Ta zaro idanu, gidanmu kuma??
Ya jin jina kai, e, gidanku, aii dama na ce, "miki bada wasa nazoba, yacigaba da fad'in, munyi magana da baba, nasar dashi komai nida kabeer, yakuma karb'eni fiye da zatona, yanzu haka yabani izinin turo iyayena! Sai dai ya ce, "bikinmu zaikai nanda watanni dan yanzu suna shirin bikin kabeer, amma bayan bikin kabeer da wata uku zuwa hud'u sai ayi namu.
Sopy ta zame ta zauna a k'asa, bayanta jingine da k'ofa.
Ya bita da kallon mamaki, ya daure ya ce, "yaya dai? Ko hakan bai mikibane??.
Ta d'an kalleshi, ta girgiza kai.
Ya ce, "to miye matsalarki??.
Ta ce, "babu, ta cigaba da fad'in nasan iyayena bazasu cutar daniba, dan haka na amince da duk abinda suka yanke, kuma zan yimusu biyayya.
Uncle G! Yaja ajiyar zuciya yana fad'in ALHAMDULILLAH!!, ya tsugnna a gabanta, ya ce, "karki damu safiyya!, kabeer ya sanar dani abinda yafaru dake a baya, tsakaninki da AMINIYARKI da kuma SAURAYINKI, to inaso ki manta da abunda yafaru a baya, ki gogeshi a arayuwarki, kid'auka yanzu zaki sake sabuwar rayuwane, ki yarda ni ne!! Zab'in alkairin da ALLAH yay miki, zan baki mamaki insha ALLAHU, Zan rik'e amanar da baba yabani taki kinji.
Yaja numfashi, gobe idan ALLAH yakaimu kabeer zaizo, zai sanar dake sauran bayani, ni kuma jibi idan ALLAH ya kaimu zanje nasanar da iyayena, ya mik'a mata farin hankici daketa tashin k'amshi, karb'i ki goge hawayenki dan banason su zuba k'asa.
Sopy ta karb'a dan ita bama tasan tana kukaba, saidai batasan kukan na miyeba?? Farinciki ko bak'incikin rabuwa da Abdul, tasan tabbas uncle G! Yafi Abdul komai kyau, ilimi, aji, da sauran abubuwa masu yawan gske, kud'i kawai mahaifin Abdul zai nunawa uncle G!, itakam bata d'auki kud'i wani abu mai muhimmanciba arayuwarta, dan itama talakace tib'is, tanada tabbacin samun nutsuwa a gidan talaka d'an uwanta.
Jitai uncle G! Yana fad'in to kukan ya isa haka, inko bahakaba zan lashe hawayen dasuka sake zubowa.
Hannu tasa tasa tarufe fuska tana dariya.
Shima dariyar yayi, "wai yau miyasaki makara ne??
Cikin sanyin murya ta ce, "karatun tarihinka mana.
Ya ce, "nice, hakan yayi nasan yanzu kinsan ni kowaye, ni talakane tib'is, sai dai rufin asirin ALLAH kawai, ina fata wannan bazai shafi auren muba ko??, Dan kinji wayeni dakuma inda nafito, kinji su waye family nawa, zaki iya neman k'arin bayani a wajen kabeer, dan yasan komai a kaina.
Tai murmushi to aii nima talakace, nasan kuma kasani, tunda kana tareda uncle kabeer.
Yad'an murmusa yana fad'in to shikenan ALLAH ya tabbatar mana da alkairi, amma daga yau idan kika k'ara makara a lecture d'ina tofa bayan horon hana shiga aji, akwai horo tsakanina dake, dan haka ki kiyaye, yafad'a yana mik'ewa.
Itama ta tashi tsaye, to bari na tafi.
Kai habadai tun yanzu, nifa ban gaji da ganinkiba!!.
Hannu tasa ta rufe fuska ta ce, "aii munkusa shiga lecture ne.
Yay dariya to sarkin kunya, ga kayanki can jeki d'auka.
Ahankali ta nufi tebir d'in sa, ta tattara takardunta ta kwaso zata juyo wayarsa ta hau wringing, ya ce, "taho min da phone d'ina!.
Saida ta d'an rissina sannan tabashi tay waje da sauri, dan batason yasake tsayar da ita.
Yay murmushi, yana binta da kallo...............[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 26~October~2016

🔷🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷

NA BILKISA IBRAHIM💞

🔶🔸2⃣6⃣🔸🔶

...........Tunda tabar office d'in tazama wata shiru shiru, gaba d'aya abin mamaki yake bata jitake tamkar amafarki, wai itace zata zama matar uncle G!, kai wannan lamari tamkar ba gsk bane, lallai ko bata son uncle G! tofa dolene ta aureshi, kodan ta k'ara nisanta kanta da Abdul, da fareeda, wasu hawaye suka zubo akan kumatunta, wlhy tana son fareeda, amma gashi fareeda tajawo abinda yanisantasu da juna, tana matuk'ar kewarta da son ganinta, takifa kanta saman tebir tana kuka.
Zaliha ta tab'ata, sopy lfy dai ko? Sopy tad'ago tana kallon zaliha, fuska share share da hawaye, ta ce, "babu komai wlhy zazzab'i nakeji".
Ayya sannu to kitashi na kaiki hostel mana.
Sopy ta girgiza kai ki bari mu gama lecture tunda saura d'aya.
Zaliha ta ce, "to shikenan", amma fa wata magana najiyo yanzu akanki!!.
Sopy ta ce, "akaina kuma zaliha??, wace irin magana kenan?.
Zaliha sarkin gulma ta gyara zama, wlhy wasu samari naji suna fad'in way soyayya kukeyi keda uncle G! Wai shiyyasa kikema samari girman kai, dan anga wai yabiki library d'azu.
Sopy ta k'urama zaliha idanu, kamar zata cinyeta, saida zaliha ta tatab'ata, sannan taja ajiyar zuciya, zaliha ta ce, "mi kuma kike tunani?
Sopy ta girgiza kai babu komai, amma ni k'arya suke min, dan kawai sunga yashiga library sai suce wajena yaje.
To aii wai bayan fitowarsa ke kuma kinje office d'insa!.
Sopy taja tsaki, ta ce, "kai magulmaci madai yaji haushi wlhy, to uncle G! Abokin uncle d'inanane tare sukai karatu a wannan makarantar, wannan itace dangan takar dake tsakaninmu, sai a daina gulmarmu aii, ta maida kanta ta kwanta.
Zaliha uwar gulma aka jinjina kai, kinsan ba kowane yasan hakaba, dan nima dabaki fad'aba ban saniba, dan wlhy nima nazata soyayya kukeyi, to ammafa kallon dayake miki irin na masoyane, idan fa yana lecture to gaba d'aya hankalinsa yana kanki, to kinga aii masu fad'a basuda laifi.
Banza sopy tayi mata, dan tasan zaliha magul maciyace tafad'a aji, ita ba k'ok'ariba sai iyayi da gwalli.
Ganin sopy ta shareta sai tatashi ta fita, wajen samarin ta nufa tazauna, suka shiga tambayarta zaliha tagaya miki, zaliha ta rik'e baki tana fad'in kukam magulmatane wlhy, idan ance maxa sun iya gulma ku musa mana, to ta ce, "wai abokin uncle d'intane.
Wani acikin samarin ya ce, "kai wlhy ban yardaba, k'arya ta fad'a miki, amma kicigaba da saka mata ido zaki hano gskyr maganar, zaliha tamik'e tana fad'in aiko saina gano bari naje dan za'ayi mana lecture yanzu.
Samarin suka shek'e da dariya, suna fad'i zaliha dama ke kina fahimtar karatune.
Zaliha ta hararesu tai gaba, dan tasan magana suka gaya mata.
Chapter 14 · 0% Book details