← Book details Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 36

Sashe 11

Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

💞Assalamu alaikum. 💞
Gaisuwa dafatan alkairi, ina fatan wannan takardar zata sameki yayin da kike cikin nutsuwarki.
Ina buk'atar ganinki a office d'ina gobe idan ALLAH yakaimu, karkuma ki shanyani, ga kuma nomber na nanan, da daddare ki kirani ko kimin filashin, dan ina buk'atar ganin nomber d'inki.
💚kihuta lafiya💚
Youseef Hussain Ahmad Gurum. {Uncle G!!}.

Sopy ta d'an tab'e baki, lallai kam, saidai kayi hak'uri dan bazan iya aikata ko d'ayaba aciki, takai takardar wajen hancinta tashak'i k'amshi ta lumshe mayan idanunta.
Madina ta ce, "tofa kodai itama ta kamu ne??
Na ce, "to madina waye yasani, saidai mucigaba da kallon ikon ALLAH.
cigaba tayi da karatunta, amma lokaci2 takan kalli takardar tayi murmushi.

..yauma kamar yanda tasaba tashirya tsaf, cikin zani da riga na jan les, tasaka hijjabinta har k'asa, tad'auki jakkarta tafita, kai tsaye aji tanufa dan tanada lecture a dai dai wannan lokacin, bayan sungama karb'ar lecture d'in yawancin d'aliban suka firfito, itakam tana zaune abunta, saida taji zafi yafara isarta sannan ta tashi tafito, dan yau bataga 'yar kazaginnataba wato zaliha, gurin data saba zama tazo tazauna, amma yau ba karatu takeba, waya tad'akko tafa chatin da uncle kabeer, sai faman murmushi takeyi wanda yake k'ara k'awatar da k'yawun fukarta.
Uncle G!, dake tsaye ajikin wata bishiya yaja ajiyar zuciya tareda lumshe idanu, karfa yarinyar nan ta zautashi, dan wlhy jiya dak'yar ya iya barci, yadad'e yana jiran kiranta, amma har yay barci bata kiraba, yasan kuma takaranata letter d'insa amma tashareshi, tacigaba da harkokinta hankali kwance, shi gashi nan tabarsa cikin damuwa, dan wata irin soyayya yake mata mai tsanani, wadda yake ganin 'yammatan!! dasuke cewa suna sonshi!! tasu soyayyar ta k'aryace, ya rintse ido yabud'esu akanta, wani k'ayataccen murmushi tasaki wannada yasa kumatunta lotsowa, shima saiya murmusa.
Gaba d'aya yinin yau zaman jiranta yazauna yi, amma batazoba, gashi yau bashida lecture dasu, duk sanda aka kwankwasa k'ofar office d'insa saiyayi tsammanin itace, amma sai anshigo yaga sab'anin hakan, har zuwa yamma batazoba, ya tattara yafita shima cikin damuwa, dan yaso sugana.

Itakam sopy tana sane, amma ta share tacigaba da sabgogin gabanta, tun wajen k'arfe 3:30pm tagama lectures nata, amma tayi tafiyarta d'aki batareda tabi takan uncle G! ba, duk da tasan yana office yana jiranta, dan duk yau bata gansaba ma.

Yau tsawo kwana biyu da uncle G!, yabama sopy letter domin buk'ar ganinta, dakuma bata izinin kiransa a waya, amma bata aikata ko d'ayaba, dukda abin yana cikin ranta, amma ta danne ta nuna baidameta ba, yauma data kasance juma'a kuma bai shigo musu lecture ba, gashi tana shirin zuwa gida weekend, dan haka tashirya bayan gama lecture karfe 11:15am tayi tafiyarta, lokacinma uncle G! Bai shigo school d'inba.
Bayan shigowarsa yayta baza idanu dan son ganinta, amma ko alamarta bai ganiba, baimaga k'awartataba zaliha,, shikam baya son tanbaya, dan kar akawo masa raini, dole yahak'ura yabarma monday, dan yaci alwashi ranar monday kobata nemeshiba tofa shi zai nemeta, dan bazai iya rik'e sonta azuciyarsaba, batareda ya sanar da itaba, domin sonta yayma zuciyarsa baban kamu wanda babu yanda za ayi ya iya hak'urin rik'eshi, shima mota yashiga yanufi gida...................✍🏻

💕Bily💕
💕💕Mrs Abdus'salam💕💕💕
💕I LOVE YOU MY FAN's💕💕
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 21~October~2016

🔷🔹NI DA AMINIYATA🔹🔷

NA BILKISA IBRAHIM 💞

🔶🔸2⃣1⃣🔸🔶

...........safiyya ana gida anashan weekend, inna tayi farincikin ganin yanda sopy ta canja, tasaki jikinta sosai sai dai haryanzu tananan arame, dan bata k'ara k'ibaba.
Yanzu tarage yawan tunani, tafi maida hankali wajen karatunta, babama yaji dad'in ganinta sosai.
Taje tagaida maman su fareeda, harma tatayata wasu ayyukan, maman fareeda tanata k'ara lallashinta akan abinda yafaru, sopy ta ce, "wlhy mama ni yawuce awajena, dama can ALLAH yarubuta Abdul mijin fareeda ne, dan haka kudaina ganin laifinta, kud'auka wannan yana cikin k'addarar rayuwarmu ne kawai.
Mama ta ce, "hummm safiyya kenan ke dai mai hak'urice kawai!! Kuma insha ALLAH saikin sami miji nagari wanda yafi Abdullahi k'yawawan halaye, itakam mun barta da wayonta!!.
A'a mama dan ALLAH karkuce haka wlhy har yanzu ina k'aunar fareeda bana son iyayenmu suyi fushi da ita!!, dan ALLAH kuyafe mata!!.
Mama ta tsurama sopy idanu, tana matukar k'aunar yarinyar, saboda hak'urinta ga nutsuwa, lallai d'iyarta tayi asara, tunda har tarabuda safiyya bata koyi k'yawawan halaye daga garetaba.
Nan dai sukaita hirarsu har yamma.
Tayi k'ok'ari taje gidan aunty Nafisa da auty hauwa'u, har gidan aunty zainab yayar fareeda, nanama hak'uri tayita bata, sopy ta ce, " bakomai yawuce".
Ranar lahadi uncle kabeer yazo gidan dan shine zai maidata school, ya d'auketa sukaje yayo mata sayya ta kayan provision da Duk abunda zata buk'ata, 'yar gatan uncle kabeer kenan, har d'unkuna yaymata yasaya mata takalma da hijja bai, da yamma tashirya suka tafi, harda kukan rabuwa da inna da baba.
Amota uncle kabeer! ke tambayarta taje gidan fareeda!? ta ce,:"haba uncle ALLAH ya kiyaeye aii har abada bazanje gidan fareeda ba, saidai idan tazo anguwar magaisa amma bazanje gidantaba!!.
Uncle kabeer yay murmushi saboda kishi??? Tai saurin fad'in uncle aii ni! Har abada bazanyi kishi da fareeda ba, koda d'imma ina bak'in cikin sub'ucewarta daga garenine, da kuma abunda ta aikata saboda son zuciya, amma ni yanzu haka na yafe mata, sai dai kuma bazamu tab'a komawa kamar daba, dan yanzu banida aminiyar data wuce inna da baba, sai uncle kabeer da my auntys d'ina.
Uncle kabeer yay dariya to shikenan kema ALLAH yabaki miji nagari.
Sopy tasa hannu tarufe fuskarta saboda kunya.
Adai dai wannan lokacinne kuma suka iso cikin makarantar, yasamu guri yay parking, ya zaro waya bari nakira abokina yazo yataremu.
Sopy ta ce, "waini waye wannan abokin nakane uncle?? Ni tunda nazo school d'innan ban sanshiba.
Ya ce, "zaki gansa yanzu nan.

Cikin 'yan mintina ya iso, hankalin sopy yana kan waya tana chatin, uncle kabeer yabud'e motar yafito, suka rungume juna shida abokin nasa.
Kai abokina nazata makarantar nan zata zama gurin zuwanka fiye da haka, amma sainaga sab'anin haka, indai har bawani abu bane yakawoka ba, ba'a ganinka.
Uncle kabeer yay dariya karka damu indai nine yanzu zaka rink'a ganina sosai tunda my daughter d'ina tana school d'in!!.
Ya ce, "gsky ne, aii nima yakamata yau nasan wannan d'iyar tamu.
Uncle kabeer ya ce, "aii gata nan amota ma ita nakawo!!
Malamin yay dariya to ta fito, saimu k'arasa office ko?? Murnar ganinka tasa na manta a inda muke tsaye.
Uncle kabeer ya ce, "sopy tafito ga abokin nasa.
Da zumud'inta tafito kuwa, tayi turus tana kallon abokin na uncle kabeer,, ba wani bane illa uncle G!, shima kallonta yakeyi cikin wani yanayi mai wutar fassara,, uncle kabeer! Yay dariya to da alama kumma san juna kenan?.
Uncle G! Yay murmushi, ai d'aliba tace, kaga duk laifinkane kenan???. Uncle kabeer ya ce, "to, kayi hak'uri, ranar dana kawota ina sauri natafi wajen aikine wlhy.
Sopy ta daure ta ce, "uncle good evening!.
Ya ce, "ya weekend??
Ta ce, "ALHAMDULILLAHI.
MASHA ALLAH yafad'a yana kama hannun uncle kabeer!, abokina muje ciki ko.
Sopy ta ce, "uncle bari nakai kayan d'aki saina dawo muyi sallama, sannan kun gama.
Okey to shikenan babu damuwa, jeki kai, amma kisamu wasu sutayaki, dan kayan sunyi miki nauyi.
To uncle!.

Sopy takira zaliha awaya sukazo itada wata k'awar zalihar, suka tayata kwashe kayan, saidai gaba d'aya zuciyaryata cike take da tunanin dama uncle G! Shine abokin uncle kabeer??, k'in fita tayi har saida uncle kabeer ya kirata a waya sannan tafito.
Bayanda zatayi dole tanufi office d'in dan uncle kabeer ya ce, "tasameshi a can.
Ahankali ta tura k'ofar office d'in tashiga, office d'in sai tashin k'amshi yakeyi, uncle kabeer ya nuna mata kujerar dake kallonsa tazauna.
Ya ce, "kindai gama ko?? Ta d'aga kai alamar e, ya ce,"masha ALLAH, yagara zama to sopy! Ga abokina malam youseef tare mukai school d'innan dashi, amma dayake shi abincinsa anan yake, to gashi yana aiki anan, munsha gwagwarmayar rayuwa tare, komai namu tarene a school d'innan, gashinan duk abinda kike buk'ata to kizo wajensa ki karb'a, kokuma idan wani abu yashige miki duhu a b'angaren karatu, to kizo zai warware miki, domin wannan dakike gani kwarone, uncle yafad'a yana kallon uncle G!.
Uncle G! Yay dariya kaidai masherancine abokina har yanzu kana nan baka canjaba ko?
Uncle kabeer ya ce, "aii gsky ce, uncle kabeer yacigaba dafad'in abokina ga d'iyata wadda nafiji da ita acikin 'ya'yana, batada damuwa kamar yada nasanar maka, itama tanada kwakwalwar karatu, dan haka ka taimaka mini wajan cika mini kwakwalwarta da karatu.
Uncle G! yataso daga kwanciyar dayayi ajikin kujera, yad'an tsurama sopy idanu tai saurin janye idanunta daga kallon datake masa, yay d'an murmushi, babu damuwa abokina nakarb'a, ainima d'iyatace.
Sopy tana mamakin yanda taga uncle G! yanata fara'a yau, domin yau itace rana tafarko dataga murmushinsa, sannan duk d'agowar datayi saita kamashi yana kallonta.
Sun d'an dad'e suna hira, kafin uncle kabeer ya tafi, saida suka rakashi har wajen motarsa bayan ficewarsa daga cikin makarantar uncle G! Ya juyo yana kallon sopy, tai kasa da kai dan tasan batada gsky....................✍🏻

💕Bily💕
💕💕Mrs Abdus'salam💞💞💞
💞I LOVE YOU MY FAN's💞💞
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 22~October~2016

🔷🔹NI DA AMINIYATA!!! 🔹🔷

NA BILKISA IBRAHIM 💞

🔶🔸2⃣2⃣🔸🔶
Chapter 11 · 0% Book details