← Book details Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 36

Sashe 24

Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

............Washe gari dak'yar sopy ta iya b'an b'are jikinta daga na uncle G!, dan tunda sukayi sallahr asuba suka koma suka kwanta, takula zaifara wani takale2, gashi yau zai koma aiki, tasamu dai dak'yar yabarta tashiga kichin ta had'a musu break, tana cikin gyaran falo fareeda ta fito, Sopy tayi burus da ita taci gaba da aikinta.
Fareeda ta daure ta ce, "mizan tayaki dashi sopy?.
Batareda ta kalletaba ta ce, "kibarshi kawai nama kusa gamawa.
Fareeda ta dage saita taya sopy aiki, Sopy ta ce, "kije ki kwanta kinsanfa bakida lafiya, fareeda tad'anyi murmushi mai ciwo ta ce, "Sopy kenan!!; karki damu da lafiyata dan nikaina batada amfani agareni, dan haka ki kawo natayaki kedai.
Sai asannan sopy ta kalli fareeda dake hawaye, saikuma jikin sopy yay sanyi, ta tabbata har yanzu tana k'yaunar fareeda, kawai b'acin raine yahana son tasiri dakuma danneshi datakeyi.
Fareeda ta surkushe agaban sopy tana zubar da hawaye, ta ce, "dan ALLAH Sopy ki yafe min, wlhy nayi nadamar abinda na aikata, rud'in shaid'anne kawai ya kaini ga aikata kuskure mafi girma ga Aminiyata 'yar uwata, dakuma iyayena, kuyimin kowanne irin hukunci, indai zaku huce, ki daina fushi dani plz, ta rushe da kuka mai ban tausayi.
Sopy ta kauda kai itama tana hawaye, sunkai tsawon minti uku kowa yana kuka, sannan sopy ta d'ago fareeda ta rungumeta suka cigaba da kuka ahaka, uncle G yana tsaye yana kallonsu cikin tausayi, lallai yasan gurinnan ana k'aunar juna, shaid'anne kawai yashiga tsakanin aminan juna, har yay tasirin b'ata tsakaninsu, ganin kukan nasu bamai k'arewa bane yasa shi yin tafi, da sauri suka juyo suna kallonsa, yay murmushi mai k'ayatarwa, tareda fad'in lallai yau ranace mai tarin farinciki da tarihi, na godema ALLAH dayasa muku hak'iri azukatanku.
Su duka murmushi suke, farida tai surin dafe kujera danjin jiri yana d'ibarta, da sauri sopy ta ruk'ota tana tambayar lfy??.
Fareeda ta ce, "kainane, uncle G ! Ya ce, "ki kaita d'aki ta kwanta, to sopy tafad'a tana rik'eda fareeda, uncle G! yabisu da kallo yana murmushi.
D'aki yakoma ya kwanta dan dasauran safiya, sopy kuma taci gaba da aikinta, bayan tagama tanufi d'aki danyin wanka, amma saita tarar fareeda ta gyara d'akin tsaf, sopy ta ce, "kai fareeda keda nace kizo ki kwanta ashe kina nan kina aiki.
Fareeda tad'anyi murmushi kawai, wanka sopy tashiga ta tsantsara kwalliya cikin siket da riga na material tayi k'yau sosai, ta ce, "fareeda kema yakamata kiyi wankan dan kiji k'arfin jikinki, saiki fito muyi break, fareeda ta ce, "to.
D'akin uncle G! tanufa, yana kwance d'ai d'ai yana barcinsa, sopy ta kalleshi tana murmushi, lallaima mutuminnan kamanta yau zakaje aiki ko?, saman gadon ta hau, tad'an jamasa hanci, ya d'an motsa, tashiga shafa kumatunsa da saje yakwanta luf luf na bak'in gashi, ahankali ya bud'e idanunsa, ta nuna masa agogonsa data d'aukko a durowar gefen gado, ya ware ido sosai dan ganin lokaci, ya mik'e yana fad'in sopyna nakusa makara fa.
Sopy tayi dariya tana fad'in ato hutun nan yasa kafara mantawa da makaranta, ya juyo yana kallonta, ya matso daf da ita murya kasa2 ya ce, "ba hutune yasani mantawa da makatantaba aii.
Sopy ta lumshe ido ta bud'e ta ce, "to, miye?, yad'an rungumota gefen jikinsa ya ce, "sopyna ce ta shayar dani zuma mai d'an d'ano, harna manta da kowa da komai.
Safiyya ta kwace jikinta tana dariya, ta ce, "uncle nidai babu ruwana ga ruwan wankanka can a bayi, bayi yanufa yana murmushi, saida yaje bakin k'ofar yajuyo yana kallonta.
Ta ce, "miya faru kuma??, ya d'an marairaice fuska ya ce, "baza'a taimaka amin wankanba.
Sopy ta zaro ido waje tana fad'in rufani kasayani, yanufota yana fad'in to bari na rufaki na sayaki, da gudu tafita tana dariya, shima bayin yashiga yana dariya.

A gurguje yayi break dan yakusa makara, har wajen mota sopy ta rakoshi, ya kalli motar da mamaki dan ganin an gogeta tsaf, ya ce, "Sopyna sannu da k'ok'ari, amma yaushe kikayi aikin nan??.
Tayi murmushi ta ce, "da safen nan uncle, ya jawota jikinsa ya rungume tsam tareda sumbatar kumatunta, ya ce, "lallai nayi dace da samun mace tagari k'yak'yk'yawa mai hankali, ALLAH yay miki albarka sopyna, yabamu 'ya'ya nagari masu irin halayen nan naki.
Tayi murmushi tareda fad'in aikafini halaye masu k'yau, nafison 'ya'yanmu subiyoka tafad'a tana rufe fuska dan kunya🙈.
Uncle G! Yay murmushi ya ce, "sarkin kunya, ni bari nawuce dan karna makara dayawa.
Ta ce, "to ALLAH ya tsare ya kiyayeminkai!!, ka gaida min da mutane.
Ya ce, "amin, tareda mata hararar wasa ya ce, "ninema d'an aikenki??.
Ta ce, "A'a nina isa na aiki my sir d'ina, kuma sarkina.
Yay dariya, idan nadawo zaki gayamin waye sir d'in aii.
Sopy tashige gida tana dariya, shima yaja motar yatafi yana dariya, da k'ara jin yarinyar a zuciyarsa..................✍🏻

💞Bily💞
💞💞Mrs Abdus'salam💞💞💞
💞I LOVE YOU MY FAN's💞💞
[12/19, 7:26 PM] mrs bilkisu: 7~November~2016

🔷🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷

NA BILKISA IBRAHIM💞

🔶🔸4⃣4⃣🔸🔶

............fareeda dake lab'e tana kallonsu sopy takoma da sauri tazauna danganin sopy tanufo palon tana dariya.
Sopy tashigo da sallama, fareeda taisaurin kauda komai azuciyarta ta amsa cikin fara'a, sopy ta ce, "tashi muyi break ko 'yar uwa, fareeda ta ce, "to, suna break suna hira sama2, dan yanzu babu wani sabo tsakaninsu, kunsan idan karabu dazama da mutum hakan yana faruwa, bare idan sab'ani yashiga tsakaninku.
Bayan sun gama break sopy tanufi d'akin uncle G! domin gyarawa, fareeda! ta k'urama hoton uncle G! dake palon idanu, wani kuma shida Sopy! suna murmushi, a zuciyarta ta ce, "sopy kedai kullum mai sa'a ce, inama ace............. ..., 😳nad'an zaro ido ina fad'in fareeda!! inama ace mi?????????????????.😏😏😏

Amakaranta kuwa tunda uncle G! yay fakin d'alibai sukayo caa akansa, ya fito daga motar fuskarsa cike da fara'a, sukansu d'aliban fara'ar tasa tabasu mamaki, nan dai suka shiga gaisheshi da k'ara tayasa murnar aurensa.
Shima gidiya yayita musu da halartar d'aurin aurensa dasukayi, dakuma tanbayarsu karatunsu.
Sukace komai nomal amma sunyi missing nasa sosai, shima ya ce, "yayi missing nasu.
Wata ta ce, "uncle G! ina amarya safiyya!!?, saida yad'an murmusa sannan ya ce, "tana gida nabarota, wata ta ce, "bazata dawo school baneba??, ya ce, "zata dawo amma saita k'ara hutawa, gaba d'aya gurin suka sa dariya, shima yayi gaba yana dariyar.
A office ma bata sake zaniba, dan d'alibaine sukaita yimasa cincirindon taya murna harda malamai 'yan uwansa, wasuma gulma takawosu acikin d'aliban.
Dak'yar ya samu kansa zuwa sha biyu yashiga lecture, saidai gaba d'aya kewar sopy saita isheshi, ya kalli gurin zamanta yaga kamar zaiganta yanzu, sukansu wasu d'aliban sun harbo jirginsa, dan duk sanda ya kalli gurin daya fara ganinta saiya yi murmushi, dahaka dai yagama musu lecture d'in yafito, suka shiga gulmarsa akan kallon gurin zaman sopy dayayi tayi.
Daga nan wani ajin yaje yagabatar da lecture, sai karfe biyar na yamma yanufo gida, cikin zumud'in son ganin sopy.
Chapter 24 · 0% Book details