← Book details Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 36

Sashe 3

Ni Da Aminiyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sopy kwance atsakar gida jikin wata 'yar bishiyar mangwaro dake tsakar gidansu,, hannunta rik'e da littafin English tana dubawa, dan exam tana gabatosu,, inna dake zirga zirga a tsakar gida dan k"ok'arin had'a abincin dare, ta kalli sopy safiyya ki tashi ki share tsakar gidannan kar magriba tayifa kina ganin rana tafara jaa.
To inna safiyya tafad'a tana mik'ewa, ta nannad'e tabarmar tafara sharar tsakar gidan,, tana cikin sharar malam ibrahim yay sallama da gudu sopy taje ta taryoshi,, baba sannu dazuwa.
Yauwa safiyan baba,, ya gidan?? Wlhy baba kafiya lao, to madalla.
Ta karb'i ledan hannunsa tana fad'in baba mika sayomin???
Yay dariya safiya way sai yaushe zakibar kwad'ayine kinfa girma,, inna tafito kichin tana masa sannu ya amsa cikin fara'a,, yaja kujera 'yar tsugunno yazauna,, inna takawo masa ruwansha.
Sopy tagama shara ta wanke hannunta, sannan tanufo babanta, baba tunda kaki fad'a min nibari naduba dakaina,, baba yay dariya to duba 'yar baba kankanace nasiyo miki saboda nasanki da son kankana,, ta d'auki ledar tana fad'in nagode babana mai sona.
Inna tace" malam ita kad'ai kasayoma kankarar Kenan? ?? Safiyya tace kai inna kina kishine???
Inna taimata 🖐🏻dak'uwa kinci gidanku nicema nake kishin dake ???
Malam ya mik'e yana musu dariya,, yad'au buta yayi alwala, ita kuma Sopy tazauna gyara kankana, dan tana fashin sallah.

Suna zaune atsakar gida suna cin abinci,, sopy tana gefe tana shan kankana,, inna tace" ni ina tawa kankanar?? Sopy tamik'e tana fad'in wlhy baba idan banbama inna kankanar nanba bazata barni nasha iskaba.
" inna tarik'e baki wayni yaushe safiyya ta rainani agidannan ne malam??? Malam ibrahim ya murmusa bawani raini,, aii ko kurama da 'ya'yanta take wasa a dawa,, itama tana tsokanarkine kaway.
Inna tace" kaidai kana goya mata baya ne kaway,, safiyya tai dariya baba kabarta ai kwanannan zan tafiyata gidan aunty Nafisa hutu saita dad'e bata ganniba,, damma uncle kabeer bashida mata da gidansa zan koma.........yaron dayay sallama yasa sopy yin shiru.
"" kai shamsu lfy ??sopy ta tanbaya,, shamsu yace wanine yace kizo awaje,, wani kuma?? Waye wani?? bashida suna ne??? Shamsu yace nibansan sunansaba amma agidan Alhaji Abubakar mai fata yake.
Baba yace"kaga yaro yitafiyar ka,, gata nan zuwa.
Sopy ta turo baki wlhy nikam baba banason fita tad'innan yau,, baba yace"" tobake kika zab'i mijinkiba da kanki maza tashi kije,, amma kar a zauna wannan doguwar hirar,, tun ana fad'ar gsky har akoma k'arya.
Sopy tace"to baba bari nak'are shan kankanata.
A'a tashikije idan kin dawo saikisha.
Dole tamik'e tatafi badan tasoba.

Inna ta kalli baba,, malam wlhy nidai dan kawai safiyya tanason yaron nan amma nikam bai kwanta min araiba,, banaso akai safiyya gidan nan mai tarin mata da 'ya'ya.
Baba yaja ajiyar zuciya,, hajara babu abinda zamu iyayi face addu'a,, dan neman zab'in ALLAH, ALLAH yazab'a mana abinda yafi alkairi.
"To amin malam"

Awaje kuwa sopy tana fita saita tararda Abdul tare da fareeda suna hira,, lamarin yayi matuk'ar bawa sopy mamaki,, amma saita danne tak'arada wajensu da sallama.
Atare suka amsa mata,, takalli fareeda,, ke sister amma ke 'yar rainin hankalice yanzu nan dama baki tafiba???? Fareeda tace" kibari kawai 'yar uwa wlhy mamace ta kwafsa min tahanani zuwa,, fushi nakeyi shiyyasa kikaga ban shigoba,, yanzuma nazo na ari wayan Abdul ne nakira aunty sadiya nafad'a mata abinda yahanani zuwa.

Sopy taja ajiyar zuciya mai k'arfi,, Abdul yay saurin kallonta gimbiyata miye matsalarki???? Babu komai habibina ykk?? Lfy lau nake gimbiyata.
Nan dai suka dasa hira harda fareeda,, dan tak'i tafiya.
Hakan baisa sopy ta zargi komai ba, dan zuciyarta a tsarkake take,, ta yarda da fareeda da Abdul, d'ari bisa d'ari.

Washe gari saiga aunty sadiya tazo gidansu fareeda,, nanta wuni,, saida mama tashiga sallah sannan aunty sadiya tabama fareeda abinda takawo mata,, tai mata bayani dalla dalla sai dai nima bansan mita bataba masu karatu dan sunshige k'uryar d'akine.
" kukasance tare dani danjin yanda zata kasance.....................✍🏻

💕Bily💕
💕💕Mrs Abdus'salam💕💕💕
💕I LOVE YOU MY FAN's💕💕
💕

[12/19, 7:24 PM] mrs bilkisu: 6~October ~2016

🔷🔹NI DA K'AWATA🔹🔷

NA BILKISA IBRAHIM💕

🔶🔸6⃣🔸🔶

................Yaud'in takasance asabar babu makaranta su sopy suna gida,, fareeda ce tadoso gidansu sopy hannunta rik'e da filet a rufe tashigo da sallama,, inna dake d'aki ta amsa mata,, tak'arasa d'akin inna ta gaisheta inna tace" yasu ladidin?? Lfy lao inna tamace na gaisheki wai anjima zata shigo kuje asibitin dubiyar nan.
"" A toshikenan babu damuwa saita zod'in,, kishiga safiyyan tana nan a d'akinta tana shirin tfy gidan hauwa'u,, nazatama tare zaku??? Eh dama tare zamuje to sai zanje gidan aunty sadiya nakai mata sak'o kinsan ita kuma bata zuwa gidan,, amma inna kai sak'on zan isketa acan d'in.
Ato shikenan ma,, itama d'in shirmene yake damunta kawai,, sadiya ba innarta bace??
Fareeda tayi murmushi bahaka bane inna laifin aunty sadiyarne aii,, tafad'a tana mik'ewa.

D'akin sopy ta shiga, sopy na zaune tana kwalliya fareeda ta zauna kusada ita 'yammata wannan irin kwalliya haka' saikace maishirin zuwa gasa??? Sopy ta harareta ke bakiga takibane??? Nitunda nake dake ma bantab'a ganin kinyi irin wannan gayunba wlhy????
"Fareeda ta tura mata filet d'in datazo dashi, tana fad'in shike nan kin rama.
Sopy ta bud'e filet d'in tana fad'in mikika kawo min??
Wlhy waynar filawace nayi dasafe,, to naga baki shigoba shiyyasa nabiyoki da ita.
Sopy tace" kin k'yauta kuwa dama tund'azu nakasa karyawa.
" saboda mi??
Wlhy bako mai kawai dai yaunatashi duk jikina babu dad'i ga gabana sai fad'uwa yakeyi. Fareeda tace tofa lfy dai""
Wlhy nima bansaniba 'yar uwa.
To ALLAH yatabbatar mana da alkairinsa,,, fareeda tafad'a.
"" sopy tace'' amin dai.

Tare suka fito kowacce tahau mota zuwa inda zata.
hauwa'u tatari 'yar uwarta da murana,, sopy tace" aunty ina Arfat yake?? Yana wajen kareema yarinyar makwaftan mu d'azunnan tazo ta d'aukeshi suka tafi.
" kai aunty wanan d'an yaron kika bari aka fita dashi da wannan safiyar?? To yazanyi auta yariga yasaba dasu,, tashigo kawo min abune yamak'ale mata. Toni dai ki aika akawo min yarona! Karki damu zata kawoshi,, wai yana ganki ke kad'ai ina K'AWAR taki fareeda???
"Itama tana nan zuwa taje gidan sadiyane takai sak'o zuwa anjima zata zo.
To shikenan ALLAH yakawo ta nitashima ki d'ora mana abincin rana,, dama d'inki zanyi.
Kefa kinji matsalarki mutum baya zuwa gidanki ya huta dayazo saikin manna masa aiki, tafad'a tana kumbura baki.
Aunty hauwa'u tace" kekuma gashi baki son aiki ko?? Haka zamu kaiwa Abdul d'in ke,, inma zaki dage kidage wannan gidan nasu mai tarin 'ya'ya da mata,, dan agidan za'a ajiyeki tunda dukkan matan yayyensa anan suke zaune.
Sopy ta tashi daga kwanciyar datayi,, to aishi yace" ba anan zamu zaunaba zai kama mana haya.
Aunty hauwa'u ta tab'e baki to ALLAH yasa hakane???
"Sopy tamik'e tana fad'in hakanema.
Miza'a dafa?? Aii inaga tuwon shinkafa za'ayi. Sopy tace" kai kukam kuda inna bakuda matsalar data wuce ta tuwo?? Aunty hauwa'u tai dariya,, toshi abban Arfat yakeson ci.
Nikam gsky bazanci tuwo daranaba,, zan dafa mana wani abu nida fareeda kafin tazo! Duk yanda kikayi cewar aunty hauwa'u.

Fareeda kam ta isa gidan aunty sadiya,, sadiya tabita da kallo lallai fareeda wannan irin kwalliya haka??? Duk ta tarar Abdul d'ince??? Fareeda tayi dariya auty sadiya ya rankine,?? kefa kikace na cake sosai.
" sadiya tace" gsk yane d'iyata, suka tafa nuna dariya.
Fareeda tace" yaya dai kin kammala girkin??
Aii komai ya kammala yanzu Abdul kawai zamu jira.
Fareeda tai wani ihu ALLAH yabar minke aunty na,, kina cikin aikina.
Sadiya tai dariya ALLAH yashir yaki fareeda,, yanzu dai ki kirashi dan muji yaushe zai iso??
"" to auntyna, fareeda takira Abdul yacemata aii gama shinan ahanyar zuwa,, tak'ara yimasa kwatancen layin?? Fareeda takuma yimasa kwatance sannan ta kashe wayar.

Sopy tagama abinci tazauna kusada aunty hauwa'u tana fad'in wash ALLAH yaudai saina sha maganin gajiya zan iya barci.
Aunty ta harareta way safiyya mikike son zamane?? Da dai keba raguwa bace wlhy.
Sopy tai dariya dama can dan ban gama sanin ciwon kaina baneba,, amma yanzu ina.
"" aunty tace" zaki gaya musu yarinya.
Kareema tai sallama hannunta d'auke da Arfat,, sopy ta karb'eshi da sauri tana fad'in oyoyo my son! Tai kissing d'in kumatunsa.
"" kareema ta gaisheta,, aunty hauwa'u tace kareema sannun ki! Kareema tai dariya kai aunty saikace wani aiki,, umma cema tace nakawoshi yasha nono amma ba kuka yakeba.
Aunty hauwa'u tace" aii nagode wlhy badankeba da Arfat bazai barni nayi d'inkin nanba,,, nibansan yanda zanyiba idan kinyi aure??? Kareema tafita da gudu wai kunya takeji,, su sopy sukasaka dariya.......................✍🏻

💕Bily💕
💕💕Mrs Abdus'salam💕💕💕
💕I LOVE YOU MY FAN's💕💕
💕
[12/19, 7:24 PM] mrs bilkisu: 7~October ~2016

🔷🔹NI DA K'AWATA 🔹🔷

NA BILKISA IBRAHIM💕

🔶🔸7⃣🔸🔶

..............Abdul ya iso yakira fareeda yay mata kwatancen inda yake,, suka aika wani yaro ya taho dashi zuwa k'ofar gidan,, amma sai yaja tunga yak'i shiga gidan,, fareeda tafito cikin dogon hijjab harda saka nik'af shi baima ganetaba dan haka yad'an ja gefe domin bata hanya,, tai masa sallama ya amsa yana binta da kallo,, tai dariya Abdul nicefa fareeda baka ganeniba ne??
Abdul yace"tofa wlhy ban ganekiba naga kinsaka nik'af nina zatama matar aurece!!
Fareeda tai dariya wlhy nice,, kashigo mana!!
A'a yaza ayi nashiga gidan mutane batareda izinin mai gidan ba???
Karka damu baya nan kuma yasan da zuwanka, kashigo kaway dan ALLAH.
sayda yay jim sannan yace" kina ganin babu matsala fareeda!
Babu wata matsala kamar yanda nagaya maka yasan da zuwanka,, kafinma katafi zai dawo gidan.
" to shike nan muje"
Har falon aunty sadiya suka kaishi yazauna yana shak'ar iskar fanka,, fareeda tafito zuwa tsakar gida ta iske aunty sadiya a kichin,, aunty sadiya tace" yaya dai yashigo?? Fareeda tace" yanama falonki zaune. Sukai dariya, sopy tacire nik'abi tad'au wata hoda a cikin leda ta kuma shafawa ta d' au kwalli tashafa,, aunty sadiya tamik'o mata turare ta fesa,, sannan tace" nayi my aunty??? Sadiya ta jinjina kai kinyi d'iyata komai yaji,, d'auki abinci kitafi nima zanzo mugaisa.
To shikenan auntyna fareeda tafad'a tana d'aukar tiren da kulolo ke kai.
Chapter 3 · 0% Book details