← Book details Namijin Zuma Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 82

Sashe 77

Namijin Zuma Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bar falon, ya nufa side din da doctor haphis yake ya isar da sako kana yaja motarsa yabar gidan. bajimawa Aeezad yayi wankan ya fito duk jikinsa ba ddh kmr an zare masa laka, ya shirya cikin kananun kaya marasa nauyi riga da wando iya guiwa kalar sky blue, yayi sallar azahar kana ya sakko falon kasa inda tini doctor ke jiransa hannunsa rike da charbi yana lazimi se zuba kamshi yakeyi, fuskannan tasa tayi fayau da ita. doctor ya gaidasa ya amsa, ya zauna kan kujerar 3ctr doctor ya duba hannun ya masa allura a baya ya koma ya kwanta kan kujerar 3ctr din idanuwansa na kan TV Amma zuciyarsa na kan mommy, da yanzu suna tare, tunawa yashiga jiya war haka yana tare da ita. "Ubangijine ya jarabceni da wannan azababben SON.." Aeezad ya fadi a ransa. doctor ya masa Allah sawake Sam be amsa ba sbda bejisaba, yanacan duniyar tunanin mommy. ftini doctor ya fice a falon da kayan aikinsa a hannu, a farfajiyar gidan yaga Hajiya naeema wadda ke tafe cikin isa sanye take da jallabiya nude color skin dinta na hutu se walwali yakeyi. Doctor haphis ya gaidata sbda yasan itace matar Aeezad din, sama sama ta amsa ta nufa part din Aeezad shi kuma doctor ya nufa part din da aka basa, yana tafe yana mamakin halin naeema tin tini in yana gaidata seta dinga amsawa da kyar, tin zuwansa gidan da 2days yaganta a gidan, wato ranar dasukaje gun bokan gidan hajiya mommy ta kwana har kwanaki biyu, tana gidan Alhaji sunusi ya gaya mata Aeezad ya kebance kansa sbda Yana bukatar hutu, Sam na'eema bata yadda da hutun da yaje yiba sbda baya daukar wayarta, Kuma gaskiya ba hk yake mata ba, ko a Wani hali yake yana daukar wayarta, daman ta tabajin kishin-kishin mijinta ya taba ajiye karuwa to Tasha gun karuwar yaje yanzu ma, Amma tayi shiru da bakinta seta tabbatar seta gayama hajiya mommy a dauki mataki, gabaki daya ma ya chanza mata, dace ada ne inya ganta jikinsa har rawa yakeyi yacita, Amma yanzu shiru,. Ta window dinta taga dawowarsa gidan yanzu. Ayi hkri da typing error. Saadatubintuabdullahi 38... Bakinta dauke Da Sallahma tashigo Falon nasa, danshi ka'idace ba a shigo masa falo ba ayi sallahma Ba. a fari ta fara wannan iskancin seda ya taka mata burki shine ta shiga taitayinta. Kwance ta gansa idanuwansa rufe, tasan ba bacci yake ba, ta karasa kujerar dake facing wadda yake kwance ta zauna, tayi crossing legs. Cikin isa ta gaidasa Hadi da tambayarsa ya jiki. Sam beji.a shigowarta ba sbda Yanacan duniyar tunani. "Ina wuni,,, ya karfin jikin?" Naeema ta sake maimaitawa da d'an karfi, ganin kmr ma besan tashigo ba. Aeezad yayi firgigit Hadi da dawowa hayyacinsa ya bude sexy luf-luf eyes dinsa kyar a kanta, tunani yashigayi ma wai yaushe tashigo Falonsa?. ''tunnanin me kakeyi har haka?" Na'eema ta tambayesa fuska dauke da azababben kishi, tana azabar San mijinta, ita duk tunaninta, tunanin wata karuwar yakeyi. Yaji me tace Amma Sam be bata amsa ba, saboda yasan tunaninta baze dauki abinda yake tunani ba, Koya gaya mata bazata dauka ba, illa iyaka ma ya tarwatsa mata brain, ta fadi ta mutu. Gyara kwanciyarsa yayi a kan kujerar dayake kwance, still manyan idanuwansa masu kama Dana bacci-bacci suna kan na'eema, ji yakeyi a ransa inama ace nabeelah ce zaune inda na'eema take zaune, dase yajawota jikinsa yayi kissing dinta, gabaki daya kewarta ta ishesa kmr ba yanzu suka rabu ba,ji yakeyi kmr ya shekara dubu be ganta ba, gaskiya shida kansa yasan yana azabar San mommy, musammanma yanzu daya shiga gindi yayi gwatso yaji azababben dadih iya dadih, se son da yake mata da martabarta suka kara ninkin-ma-ninkin a kwayoyin idanuwansa, shifa yanzu baya ganin naeema a mace, ba na'eema ba duk matan duniya yanzu be ganinsu a mace, gabaki daya mommy ta riga ta cika ko ina na sassan zuciyarsa da gwanjinsa da komi nata. Ganin ya mata shiru ya hasala na'eema ranta ya Kuma baci zuciyarta ta harzuka da azababben kishinsa, tasan shi miskiline daman tin can Amma gaskiya a yanzu abubuwan nasa sunyi yawa, kallon da yake mata yanzu ada ba irinsa yake mata ba,. Cikin tsiwa Na'eema tace "duk kabi ka chanzamin tin tini, kawai ina daurewa ne, ina Kuma kallanka ne kawai, sekace ba auren soyayya mukayi ba nida Kai,, Baka kallona da daraja sbda ka fad'a soyayya da karuwa, duba fa yanzu nashigo baka sani ba sbda kana tunanin wata banza ballagaza karuwar ti-t..." Bata samu damar karasa kalamanta ba saboda uwar tsawar daya daka mata. "Ke dallah rufemin baki,!! Sha-sha-sha, ni kike dangan tawa da karuwa saboda baki da hankali baki da tunani bakisan inda Ke Miki ciwo ba? Yaushe raini yashigo tsakanina dake har haka? To ahir dinki Dani, kinsanni Kmr yunwar cikinki nafi karfin raini a gurin y'a mace, Ke in kinada hankali harkin isa kizo kiyimin wata mgnrki ta hauka ranar da aka dawo Dani daga asibiti kika fita kika bar gidannan ba tare da izinina ba, ke duk abubuwan da kikeyi ban miki mgna ba seni kikema mgnr banza, kike dangan tani da karuwa, Sbda bakida daraja baki da tarbiya ni kike dangan tawa da karuwa, tin wuri ki kiyayeni kinji na gaya miki in ba haka ba wlhi zan bata miki rayuwarki gabaki daya!!," Ya karashe da muryar gargad'i. Na'eema ta saki baki ganin wai yau itace Aeezad kema tsawa da gaya mata maganganu kamar Daman Yana jiranta, Harda cemata sha-sha-sha. "Yau harni Na'eema kakema tsawa? Kawai saboda ka hadu da karuwa Ta dauke maka hankali?" Ta sake fadi cikin tsiwa da rashin tarbiya da rashin kunya. Tashi zaune yayi ganin tana Neman ta bata masa Rai, kalmar karuwannan na bata masa rai,,..''Tashi ki fitarmin a part tin ban miki abinda zakiyi Dana sani saninaba,!!!,,," ya fadi cikin tsawa Hadi da nuna mata kofar fita,. Mamakinsa ya daskarar da na'eema a inda take zaune, zuciyarta se dukan uku uku takeyi, wai yau itace Aeezad ke kora a part dinsa, mutumin dake rokonta Allah annabi tazo part dinsa yacita ada Amma yau ita yake kora? mamakinsa mara iyaka yayi wankan tsarki ya kuma rufe mata zuciya, be taba wulakantata ba duk abubuwan da take masa Se yau, idanuwanta suka cicciko da kwallar tashin hnkli Amma ta hadiye sbda bataso tayi kwallah a gabansa gudun karta zubarma da kanta mutumci. "Yauni kake kora a part dinka,? Sbda ka hadu da wata karuwa, wata Tsinanniy..." Mikewa aeezad yayi ganin tana neman bata masa mood shi Kuma Kawai so yakeyi ya zauna shi kadai yayi tunanin mommy yafi masa ganin na'eema dadih. Batare dayace komi ba yabar falon zuwa upstairs Nan ya barta tana sambatun kishi, mikewa tayi ta bar falon a guje ta nufa part dinta, tana Isa falonta ta zube kan kujera ta fashe da kuka, duk ta gigice sbda azababben kishi, tana kaunar mijinta sosai, gani takeyi kawai karuwa yasamu shiyasa yaketa chanza mata,koda hakan ya faru ma tasan harda lefinta sbda tafiye-tafiyen da takeyi, tin Yana dokinta yanzu ta kulama yadena dokinta, Kuma duk lefin hajiya mommy ne, Amma ba halin ta fadi. bayan taci kuka ta koshi tajawo wayarta ta kira hajiya mommy, bugu biyu wayar tayi ta daga , taji yarta na kuka Nan hnklinta ya tashi tashiga tambayarta meya faru? Na'eema ta kwashe duk abinda ya wanzu tsakaninta da Aeezad ta gaya mata. Hajiya mommy ta numfasa tace "haba biri yayi kama da mutum,,,toh wlhi ke kinfi karfin wulakanci, ashe bamusan inda bakin zaren yake ba, mun dauki hakkin nabeelah, daman daga baya nayi tunani gaskiya aeezad me zeyi da wata nabeelah, tsohon gindi, Can wata Yar asirin yasamu Ashe ta mallakesa, haba biri yayi kama da mutum,...ba Wanda ze daga miki hnkli yata ki kwantar da hankalinki zuwa gobe mu shiga cikin daura can gun bokana na kan ruwah..." Na'eema na kuka tace toh sukayi sallahma ta ajiye wayar taci gaba da kukan, tabbas da ace zatayi Ido biyu da wadda ta dauke mata hankalin miji, babu abinda ze hana ta nakasata ta yadda bazata moruba. Direct bedroom dinsa ya nufa bayan ya hayo upstairs din. Zuciyarsa fal haushi da takaicin na'eema Sam besan na'eema bata da hankali ha se yau. Yaja k'wafa, kana ya isa kan bed dinsa ya kwanta befi 3mnt da kwanciya ba yayi zumbur ya tashi zaune, ya nufa bedside ya daukko wayarsa ya nemi lambar mommy ya kira ,bata daga ba har kira uku, ya katse ya kira Aunty hafsat wadda ke zaune har yanzu a falon tana jinjina lamarin Aeezad da nabeelah, big hajiya Kam tinda tashiga dakin bata fito ba, tana can ta tasa abun duniya a gaba se kasafi takeyi, harda kudin da zaks yace ze kawo masa dukda batasan nawa bane Amma se kasaftasu takeyi sbda azabar San zuciyar dake dawainiya da big hajiya. Ringing biyu wayar aunty hafsat wadda ke falon jone a charge, ta tashi ta isa ga wayar tata, taga sunan Aeezad, cire wayar tayi a charge kana ta daga wayar ta kara a kunnenta na dama. Daga cikin wayar Aeezad yace ''Ya mommyna take?" Aunty hafsat tace "Ai tana daki bata fito ba tinda kuka bar gidan..." "Ki dubomin ita pls,,, a bata abinci sbda batajin ddh Kuma tanajin yunwa...'' aunty hafsat tace ''Toh .." lamarin nata Kara daure mata kai. "Kije ki dubata ynzu inajinki bazan kashe wayar ba,,,"cewar Aeezad. Aunty hafsat tasake cewa toh...kana ta nufa dakin aunty nabeelah, kwance ta ganta tayi baje bajee ta cire hijjabin jikinta, sanye take da rigar mara nauyi lemon green,. Bayan Aeezad ya fita a dakin a daddafe ta iya wanka, tayi sallar azahar ta chanza rigar jallabiyar Aeezad dake jikinta zuwa rigar jikinta ta ynzu lemon green, tana kwanciya bacci ya kwasheta ga sanyin AC na ratsata,. A yadda take sauke numfashi ya tabbatar ma da Aunty hafsat baccin takeyi sosai Kuma me nauyi. "Kagana Bacci takeyi..." Aunty hafsat tasanar da Aeezad ta cikin wayar. "Bacci kuma? Amma tana lafiya de kou,?" Ya tambaya muryarsa dauke da rikicin SO da kaunar mommynsa,. Aunty hafsat tace "toh gaskiya bansaniba tanade bacci naga Kuma baccin ya dauketa sosai..." Sam aeezad be gamsu ba kawai so yakeyi yaganta danya tabbatar Kuma idanuwansa
Chapter 77 · 0% Book details