Sashe 42
Namijin Zuma Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
gimbiya me mulkar farar zuciya Zaks yayi mgnr da Aunty nabeelah, bayan ya kula da aiken hararar da nabeelah ta masa, nabeelah da Aeezad ne kawai suka fahimci me zaks ke nufi amma big hajiya bata fahimci komi ba, a zatonta shakiyyancine kawai irin na zaks, suka shige cikin dakin big hajiya da nabeelah. Aeezad ya kalli Zaks yace Kai zanci kutmar ubanka fa in kana hadawa da iyalina a iskancinka Zaks yayi dariya yace da girman kujerarka dawisu me mulkin mallaka,,,sannu Mijin mommy kuma mahaifin mommy kuma mahaifiyar mommy, sannu waliyyin mommy shugaban yan iskan duniya, me ciki bakwai Aeezad ya kwashe da dariya hadi da watsoma zaks wani gangariyar ashariya, Zaks ya kwashe da dariya. Aeezad ya mike yana dariya ya kalli Zaks yace Dan iska, kaje ka Kira doctor yazo yasamin drip Dina na yau na farajin hannun namin zafi yanzu Zaks ya mike hadi dacewa okay yana fadin hkn ya fice , Aeezad ya nufa cikin dakin. Ranar gabaki daya nabeelah batayi bacci ba, Zaks nan ya kwana a falo, ita kam ko rintsi batai ba, kafin Safiya tayi ta kara fice wa a hayyacinta har Rama tayi, ita banzan jikine da ita, tashin hankalin awa biyu ka seya ramar da ita, ba wani jikine da ita ba kayane na Alatu kawai gareta tako ina , irin kayan da dole in namiji ya ganta hankalinsa ya tashi, ko mace ta kalleta seta tabbatar nabeelah macece ta bugawa a jarida macece wadda ta Riga ta Kama kasa tanada komi da namiji ke bukata a jikin mace. Washe gari da safe Zaks ya bar asibitin zuwa karfe sha biyu hauwa u tazo, da manyan baskets masu dauke da manyan warmers , abinci ta kawo musu kusan kala biyar da farfesu nau i daban-daban kala uku, sannan da drink kala uku shima. Dole nabeelah tayi feeding Aeezad badan tanaso ba, hauwa u na ankare da nabeelah tin zuwanta ta fuskanci tanada damuwa ba haka ta barta ba jiya Gashi bataga alamar wayar da Alhaji sadin ya bata ba, daman hauwa u tasan za a rina hakan. Bayan nabeelah ta gama bawa Aeezad abincin hauwa u tayi dabara taja nabeelah waje,. Kawata Meya Faru daga jiya zuwa yau kinyi fige-fige hauwa u ta tambayi nabeelah bayan sun fito wajen sun kefe gun wata bishiya. Nabeelah tace bakomai.. hauwa u ta tsareta da tambaya, badan nabeelah taso ba se dan bata da yadda zatayi yasa ta kwashe komi ta sanar da Hauwa un, bata boye mata komi ba. Tabdijan!! Hauwa u ta fadi tana me jinjina lamarin ita kanta jinta take kmr a mafarki. Kaddara hauwa u ta fadi a bayyane se kallon nabeelah takeyi. Wlhi aurennan be dauru ba, tinda ba amincewa ta yayi Auren yaudara dani, kawai danni ba kowa bace zemin haka, dan Ina aiki a kasansu nabeelah ta fadi Tana sharar kwallah. Hauwa u tace Wallahi kawata Aure ya dauru sede kiyi hkri bade an tara shaidu ba , kuma kmr yadda kikace, har kinji komi a kunnenki sannan A masallacin sultan Bello , masallacin da babban masallaci ne, bazeyu ayi yaudara a dakin Allah ba, wallahi Aure ya dauru, ke da kanki ma kinsani, tinda kinada zurfin karatu a koyarwar Addinin musulunci, dande kawai tashin hankali baze barki ki fahimci hakan bane kawai kiyi hkri Aunty nabeelah komi kaddara ce, ki duba kiga mazan dasuka dinga nemanki kikaqi Aurensu, wannan fa duk a cikin zanen kaddararki ce, Ubangiji ya riga yace Aeezad ne ze aureki nabeelah ta kara fashewa da kuka tana fadin Wallahi be isa ba, wlhi ban yarda da wannan Auren ba, musulunci bece ayi zalinci ba na raine shi da hannuna in auresa in me dashi, wlhi nafi karfin aurensa, karya ne be Aureni ba, ban amince ba nabeelah ta fadi Tana me kuka kmr ranta ze fita, ta dinga sharewa da gefen hijjabinta. Hauwa u ta dinga bata baki dan ta kula bata hayyacinta, tadinga rarrashinta, ita kanta hauwa u tashin hankalin datake ciki baze misaltuba tabbas A wannan Lagon Aeezad yayi gaggawa kuma bema nabeelah adalci ba, shide kawai yabi San zuciyarsa ne da San ransa, a wata siffar kuma hauwa u ta dauki hakan kaddara ce, kuma duk bawa be isa ya kaucewa kaddararsa ba, amma fa akwai babban wasa a gaba, akwai kalu bale masu yawa, hauwa u ce kawai tasan meke kasan ranta ta tabbatar akwai babbar matsala. Ranar ma Haka hauwa u ta wuni asibitin har dare kana nabeelah ta rakota waje , nanma hakuri da ban baki hadi da natseeha akan yadda da kaddara hauwa u tayitama nabeelah kmr yadda de ta wuni Tana mata natsihar, kawai nabeelah jinta takeyi amma batajin kome za a mata a duniya zata amince da Auren Aeezad a kanta, yaudara kawai ta maida hakan. Hauwa u ta hau napep ta wuce a zuciyarta tana jinjina lamarin ita kanta abun ya bata tsoro nabeelah ta koma Cikin asibitin Tana kwallah Tana sharewa gabaki daya ta gaji ma da kasar kawai so takeyi taje kasarsu taga mamanta ko zata samu samu sassaucin abinda ke ranta. After 2days tini hawwa u ta koma katsina. gabaki daya nabeelah taki sakin jikinta kullum se kuka kawai ko bacci bata samu tayi, big hajiya duk Tasha tausayin ne ke dawainiya da ita har yanzu se natsiha take mata kan tayi hakuri ta cire hkn a ranta. Hankalin Aeezad kam kaf a tashe yake, daya kalleta se hankalinsa ya tashi ganin kukan da take tayi, ga shadin yatsunsa na Marin daya mata har yanzu be baje ba a kan fuskarta, se bata hkri yakeyi yana lallaba, hajiya nashiga toilet seya taso daga inda yake ya iso inda take dan yanzu tadena zama kusa dashi Sam kullum tana rakube a lungu, yayi ta bata hakuri amma Sam taki hakura, ko saurarensa ma bataji, a kwana biyun harshi kansa gogan ya rame, Marin dayayi mata ne kadai yake nadamarsa amma Sam be nadamar Aurenta da yayi, yasan aurenta da yayi ne yasata a damuwar da take ciki, shi kam daya kalleta se yaji ddh,. Ko abinci se hajiya tayi da kyar nabeelah keci. A satin Alhaji Sunusi da hajiya rafi ah sukaxo hadi da aunty hafsat, jirgi daya suka biyo sukaxo ganin jikin aeezad din. Kallo daya Aunty hafsat tayima nabeelah ta tabbatar Tana Cikin damuwa me tsanani, haka hajiya rafi ah ma kallo daya ta mata ta fahimci tana da damuwa dadih ya rufe hajiya rafi ah , Gashi ta fuskanci kwata-kwata nabeelah bata ta Aeezad yanzu kobi ta kansa ma batayi, farin ciki goma da ashirin ya kashe hajiya rafi ah, ita a zatonta Aikinta ne yaci a kan nabeelah , komawarta katsina tini ta Kai sunan nabeelah gun bokanta tace a raba nabeelah da Aeezad inma asiri tama Aeezad din a karyashi boka yace an gama. Toh zaton hajiya aikin ne yaci a kan nabeelah. Tini Hajiyah ta fita waje ta kira yarta dake Egypt , tanaso ta dawo amma uwar ta hana itade hankalinta na kan mijinta uwarta kuma tace bazata dawo ba seta gama hado mata kan kayayyakinta kana ta dawo. Hajiya rafi ah ta shaidawa na eema yadda taga nabeelah ta koma duk ta lalace sannan bata ma ta Aeezad din farin ciki ya lullube na eema ta jinninawa uwarta a fagen tsubbu. Sunfi awa hudu suna waya ta zallar makirci da mugunta kawai, na eema ta shaidawa uwarta ita kawai so takeyi a gayawa boka yasa nabeelah ta bar garin a mata kurciya kuma kar tasake Waiwayowa kasar ma gabaki daya, sannan bataso taje kasarsu sbda Aeezad yasan har gidansu kawai so takeyi ta nufa wata kasar daba wanda yasanta. Me kikeci na baka na zuba wannan aikinma za a yishi a hnkli, kede ki bari in gama natsar da sabon shagona in saitasa yadda ya kamata Cewar hajiya rafi ah datayi mgnr bayan taji abinda yarta ta gama Zayyanowa itama ta jima tana San ayima nabeelah hakan, sede ta fuskanci Tana mata amfani, duk karshen week in zasuyi meeting ita da kawayenta nabeelah ce karfin aikin gidan, duk Saturday da Sunday a gidan hajiya rafiah takeyi. Yawwa hajiya mommy Allah ya barminke, inasan Aeezad banasan abinda zesa nasamu cikas dashi a zaman mu tare,,, hajiya rafi ah tace Karki damu, in baki manta ba ai har aurenki dashi rabi a kan asirine, rabi nede yake sanki amma sauran ai duk asirin da ake masa ne yayi tasiri a kansa, ke dabadan sihiri ba kin isa ki dinga masa yawo da Aure, yaron da ubansa ma tsoronsa yakeji, ni kaina wlhi tsoronsa nakeji,,,,komi na rayuwarki zeta tafiya yadda kikeso yata ki kwantar da hankalinki Cewar hajiya rafi ah nan hnklin na eema ya kuma kwanciya, seda suka kara awanni biyu suna waya kana sukayi sallahma hajiya rafi ah ta koma ciki. Da daddare hajiya rafi ah ta nufa hotel dan ita tace bazata iya kwanan asibiti ba, Alhaji Sunusi ya kaita har hotel din datakeso, kanashi ya dawo asibitin shi ze iya kwana tinda abun ya kamasa dole. tinda sukaxo nabeelah ta Koma kwana falo, Aeezad fa hnkli ya tashi, ya saba daya motsa ya ganta , Gashi ta koma falo, dukse yabi ya shiga damuwa, gabaki daya hafsat na Ankare dasu, Tin zuwansu a ranar aunty hafsat ta tambayi nabeelah meke damunta aunty nabeelah tace bakomai, hafsat tayi tambayar duniyarnan amma nabeelah tace bakomai, dole hafsat ta kyaleta amma tasan tabbas nabeelah na Cikin damuwa. Kwanansu Alhaji biyu Shida matarsa hajiya rafi ah suka koma garin katsina, suka bar aunty hafsat wadda ta dauki hutun Aiki sbda ta taya nabeelah jinyar Aeezad Dan tasan Nabeelah ce ke whla big hajiya bata da katafus, ita kanta kaya ce balle tayi jinyar wani, wanka ne kawai take Taya Aeezad din yayi sbda hannunsa daya da bashi aiki har yanzu sbda ba karamin matsala k ashinsa na guiwa yasamu ba , dauri aka masa kusan na uku yanzu. After 2days da tafiyar su Alhaji sunusi da hajiya rafi ah,. Asibiti ya rage da nabeelah da big hajiya da Aunty hafsat, ba karamin Jin dadin zuwan aunty hafsat nabeelah tayi ba, sbda Rabin kula da Aeezad din duk yadawo hannun aunty hafsat, shi kam Aeezad beji dadih ba Sam , shifa bemaji dadinma zuwan Aunty