Sashe 32
Namijin Zuma Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
aunty hafsat ma duk sunzo,, dangin mahaifiyarsa ma sunzo ciki harda Aunty fatima kwananta uku kana ta koma niger. gana daddy Su kullum a hanyar zuwa suke, kullum packing space din asibitin cike da tamfatsa-tamfatsa din motoci, Kai dagani zakasan wabi kusa na kwance a asibitin. hatta Zaks ba a barshi a baya ba kullum Yana asibitin, Yana jinya shima dasa Ido ga Aeezad da Aunty nabeelah, tini Zaks ya fahimci karatun kwayoyin idanuwanta Aeezad. kowa na iya bakin kokarinsa daddy Kam ya kasa ya tsare, duk abubuwan da kowa ke masa na kulawa Aeezad baya ganin na kowa inba na Aunty nabeelah ba, ko bude Ido yayi, yaga be ganta ba hankalinsa yafi na kowa tashi, kullum tana gefensa ita ke basa abincin safe da rana da dare, bacci kawai ke raba Aeezad da nabeelah daddy ke kwana tare dashi,ita Kuma su kwana falo ita da Aunty hafsat, da sauran Al'ummah,. Gimbiya hajiya rafi'ah da na'eema Kam har yanzu hotel suke kwana, se Wani faman ciccijewa hajiya rafi'ah keyi , magana Daya biyu in Alhaji sunusi ya mata seta gaso masa magana cikin mutane ita Sam ko a jikinta, sede Alhaji sunusi yayi Shiru kawai ya kalleta ta biyoshi da harara, ta tanadar masa rashin mutumci ruwa-ruwa, kawai jira takeyi Su koma katsina ya zama ita dashi kawai , duka ne kawai bazata masa ba,Duk abinda danginsa da uwarsa suka mata a kansa zata fanshe domin shine marainin wayaunta. Tini mutane sun fara watsewa asibtin ba kmr a fari ba, Aunty hafsat ta koma katsina sbda yaranta data baro da Aikinta, ganin jikin nasa da sauki yasata tafiya, asibiti ya rage daga Aunty nabeelah, se Zaks and Alhaji sunusi da hajiya bilkisu da hajiya rafi'ah da na'eema,gabaki daya Rafi'ah tagaji da zaman asibitin wai a haka ma bata wuni asibitin, in suka kwana a hotel din dasuke kwana sesu Kai karfe biyu kana suzo asibitin, gabaki daya hajiya rafi'ah ta kosa ta koma katsina ta duba kasuwancinta, gashi na'eema ta baro mata dukiya a Egypt ta kosa su koma katsina na'eema ta nufa Egypt ta dubo mata uwar dukiyarta dake can ta sarin rigugguna. Yau Aeezad ya nemi Transfer zuwa Asibitin 44 dake kaduna, saboda Sam bayason zama a asibitin Aminu kanon sannan bayason komawa katsina saboda wata manufa dake ransa. Karfe shida na yamma zaune suke dukkaninsu a dakin da Aeezad din yake, yanzu ana barin kowa a cikin dakin sbda jikin nasa da sauki, sede kullum ana masa Allurorin saboda matsalar hannunsa. "Kaida na'eema zaku kadunan gobe kou da big hajiya ? Su zasuyi jinyarka..." Cewar Alhaji Sunusi dake zaune Yana facing Aeezad, jin abinda yace yasa Aeezad hade Rai ya saci kallon fuskar AUNTY nabeelah wadda ke kasa zaune kan carpet. "Wace na'eema??' hajiya rafi'ah ta amshe cikin tsiwa tana kallon mijinta dayayi maganar fuskarta dauke da buhu buhun rashin mutunci. "Wace na'eema kika sani bayan matarsa,,, ke kiji tambayar rashin tarbiya..." Cewar hajiya bilkisu data amshe maganar, Alhaji sunusi de yayi Shiru bece komi ba. Yatsina fuska hajiya rafi'ah tayi ta kalli hajiya bilkisu ta watsar kana tace "gaskiya bazata iya jinya ba, saboda itama ba lafiya ce da ita ba neman me jinyarta takeyi ynzu haka, ita inama zata iya wahalar jinya...." Na'eema tayi saurin amshewa da "Aah mommy zan iya wallahi..." hajiya rafi'ah ta gwabeta dacewa "Ke dallah gafara can ,a gidan ubanki zaki iya, kina fama da uban jiki kamar jakar kauye, tayaya zaki iya Wani jinya? Wannan kibar taki ta asara ke kanki ai neman me jinyarki kikeyi, kina motsi da kyar kmr mesa ta hadiye mutum... bazata iya ba wlhi sede ke hajiyar da danginku kuyi jinyar jikan naki, in rashin mutumci ne kowa ma ya iyasa ai..." ta karashe mgnr tana kallon hajiya bilkisu a wulakance. Wani irin bacin rai kalaman Rafiah ya haifarwa da Alhaji sunusi a zuciya, shi ya rasa gane kan gadon me rafi'ah take nufi ne, ada be gane ba Amma yanzu ya gane akwai kiyayyar jininsa a jinin rafi'ah, mamaki da zallar madarar bakin ciki suka kuma cika Alhaji Sunusi, ya kure hajiya rafi'ah da idanuwansa dake cike da bacin ranta dande beda yadda zeyi ne kawai, zamansu a asibitin Nan shi kadai yasan yawan bakin cikinta daya kunsa, gashi yau wai itace kecewa na'eema bazata iya jinyar jininsa ba, Aiko ba aure a tsananin na'eema da Aeezad a tunanin Alhaji sunusi na'eema me jinyar d'ansa ne, kai bama Na'eema ba, ko ita hajiya rafi'ah yaci ace ta tsaya tayi jinyar jininsa meye be mata ba a rayuwa, kaf danginta shine gatansu, cinsu suturar su duk a hannunsa yake, uwa uba ya rike mata yarta ya bata kulawa ta isilamiyya da boko, ya bata tarbiya ya bata komi take bukata a duniya fin yaran Daya haifa da cikinsa abinda yayima na'eema wlhi ko Aeezad mafi soyuwa a ransa bemasa ba. "Hmmm mutum kenan butulu, a maka rana ka tura mutun dare me tsananin duhu...insha Allahu a barmin shi ni kadai na isa zanyi jinyarsa babu abinda ze gagareni na godewa Allah ma da nake raye, insha Allah ba abinda ze gagareni Saniya bata gazawa da k'ahonta...." Cewar hajiya bilkisu dataketa mamakin hali irin na Rafi'ah ita tako ina ba inda za ace Kwara a halinta, ga rashin wayau, ga rashin kunya ga rashin tarbiya, ga uwa uba jahilci, babban abinda yafi damun hajiya rafi'ah shine rashin wayau, ga rashin iya magana Amma ita a ganinta tafi kowa iya magana,. Se yau hajiya bilkisu ta kara tabbatar da hajiya rafi'ah wawiya ce, sbda yadda ta Hana na'eema jinyar mijinta alhalin ita yarinyar tanaso tayi jinyar mijinta,. A bangaren Aeezad Sam Ko a jikinsa shi sema dadih dayaji, shi kadai yasan dalilin jin dadinsa, kawai hakan dasukayi ya masa dai-dai. Zakariyya wato Zaks ya zubawa hajiya rafi'ah Ido a ransa Yana Kara jinjinawa rashin mutunci irin na hajiya rafi'ah da rashin wayau. "Tashi mu tafi Dan ubanki daddawa uwar miji Nan kina ganin irin cin mutumcin da Akamin a family dinnan, har dukana karamin yaro yasoyi ammma ba a masa komi ba, a haka sbda bakisan darajar uwarki ba kike cewa zaki zauna Kiyi jinyarsa bayan a kansa, Nan ba irin zagin da ba ayimin ba,..." Cewar hajiya rafi'ah datayi mgnr byn ta tashi tsaye ta hambari na'eema da maganganganu dole na'eema ta tashi tana turo baki a zahiri wlhi tafiso tayi jinyar mijinta da kanta saboda bata kaunar taga Nabeelah na rabar mata miji. Kaf kowa na dakin ya zubowa Hajiya rafi'ah Ido da na'eema nabeelah Kam a ranta se kara mamakin hajiya rafi'ah takeyi ganin yadda ko a asibiti ma bata sassautawa mugun hali irin nata ba, hakan ya bawa nabeelah tabbacin da wuya hajiya rafi'ah ta shiryu kila seta jita a kabari. Hajiya bilkisu ta jefi rafi'ah da harara kawai takiyin mgna sbda intayi mgnar abun baze musu kyau ba, Sam shi Aeezad beyi mamakin komi ba yasan hajiyar Rafi'ah ba hankali ne da ita ba zata aikata fin hakanma. "Kai kuma gobe inka shirya mu tafi gida toh kase mana fly da wuri kaji na gaya maka..." Tayi mgnr da Alhaji sunusi kamar Wani d'anta. "Toh shikenan..." Alhajin sunusi ya fadi jiki na rawa, inda sabo duk sun saba gani ita kanta hajiya bilkisu ba sabon Abu bane a gunta ,tini tasan aikin asiri ne, domin inba asiri wane mutum, Adduarh ce kawai maganin wannann matsifa na hajiya rafi'ah. zaks Kam Sabon abun ya zamar masa Dan haka ya saki baki kawai Abu kamar acting din film, ba value taki ina. Hajiya rafi'ah na gama fadar hakan ta juya ta fice a dakin da wata matsiyaciyar bag a hammatarta Tasha danyar shadda da mayafi Sam ko swag dinma bata iyaba, har yanzu ruwan bariki be saki hajiya rafi'ah ne, suka fice a dakin yayinda hannu na'eema ke cikin nata, bayan sun fito daga dakin na'eema ta kwace hannunta daga cikin na hajiyar Rafi'ah tana fadin. "Ke komi sekinyi abinda be kamata ba hajiya mommy,,,," "Dan Uwarki da ubanki me nayi dabe dace ba? Shigiya se kibar banza da hofi ba wayau yanci na kwantar miki Amma kike neman min rashin kunyarki da kika saba Yar iska kawai mara tarbiya..." Na'eema ta kara hade lukutar fuskarnan tata wadda ke cike da uwar namomi me tattare da tarin lagwad'ar kitse da kyar Ake ganin kwayoyin idanuwanta sbda azabar kibarta tace "Wani yanci kenan Mommy? Ko kuma de kinaso ki kasheni da raina ba ta hanyar sanya kusanci tsakanin Aeezad dina da waccan ballagazar me Idanuwan karuwai Nabeelah..." "Dallah gafara can, sakarai, Kinga matsalar rashin wayau kou? Inta samu kusanci dashi se ayi y'ay'a?"' cewar hajiya rafi'ah. "Se ya fara santa mana mommy, bakiga yadda yaketa nannan da ita ba kamar ya maidata ciki fa hajiya mommy wlhi ji nakeyi daman inada hali in kashe ta Tsinanniya ta tsufa a gida ta kasa auruwa sbda karuwanfi..." Na'eema ta karashe mgnr a zafafe kishin nabeelah a zuciyarta kmr ze faso ya fito fili. Kallon banza hajiya rafi'ah tabita dashi kana tace "ta yaro kyau take bata karko... Ke yanzu a zatonki a duniyar Nan akwai macen dazata iya Gwafzawa dake a fagenki da AEEEZAD, na miki alqawari har abadan ke kadai zaki rayu da Aeezad, keda kishiya sede ta waje..." "ta waje kuma mommy? Wace irin ta waje? Niko ta wajemma ai banso..." cewar na'eema data amshe a zafafe, bakin kishi nacinta. "ai keda ta wajenma har abadan, ke kadai zakiyita shawagi a gidan Aeezad , ki kwantar da hankalinki diyata..." "Hankalina baze kwanta ba saboda nabeelah, hajiya mommy abinda Aeezad keyima tsinanniyar me kod'adadiyar fatarnan, wlhi mommy bnsanta kwata-kwata.." cewar na'eema. "Ai ita bata isa Aeezad ya mata Wani duba ba, bayan name masa hidima, mema zeyi da ita, bayan ita ta renesa, ke wannan fa dagani ta girmeni ma kawai Dan kyau ne da ita,,, sannan inaga asirine ta masa na amsar kudi kinsan su yan niger dinnan da asirin tsiya ga kwad'ayin kudi, can uwarta zata bugo mata asiri sbda su samu rabonsu, Insha Allahu shima asirin sena karyasa,wuyarta de in koma katsina....." (haka Ake mana sharrirrika ace mana masu asiri , ace mana masu mallake miji, ace mana Yan iska, insha Allahu se Allah ya saka mana) Nan na'eema ta danji zuciyarta