Sashe 26
Namijin Zuma Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bugun zuciyarta na kara kidima jikinta, se buga kanta takeyi a kasan tiles din dakin Sam ko zafin hakan bataji, abinda takeji a zuciyarta ya wuce tunanin duk Wani me tunani, se dealing number dinsa takeyi Kamar hauka Nan take tayi masa kira yafi kira dari biyar Amma duk a kashe. A bangaren Aeezad. tini jirgin Yan sanda dana sojoji sukama dajin saukar angulu, tako ina ma'aikata suka cika dajin tini Yan ta addan sun tsere. Bashir ne yasamu damar Kiran Wani abokin Aikinsu ya sanar dashi halin da suke fiki, kasancewar Aeezad ba karamin mutum bane a Nigeria, tini aka sanar da shuwagabannin sama, shine aka shiryo wadannan tawagar jirage guda biyu, motocin Yan sanda da sojoji Kam sunfi motoci hamsin. Nan wasu suka fada dajin domin dubo Yan ta addan Amma ina ai babu su babu dalilinsu. Yayinda tini aka dauki aeezad dake kwance kmr matacce aka sashi a cikin jirgi kana aka dauki Adamu na aka sashi a jirgin, a cikin jirgin harda chief of army, ba karamin kaunar Aeezad yakeyi ba sbda kokarinsa a hukumar sojojin, ganinsa kwance kmr ba Rai seda yayi kwallah,. "Jarumin maza.. Namijin fama..." Chief of army ya fadi Yana me kallon Aeezad a kwance tamkar matacce,kowa jikinsa ya sare gani sukeyi da wuya Aeezad ya rayu,dukda basu sanma a ina aka harbesa ba, kawai de jini se kwarara yakeyi a hannunsa jinin me dumbin yawa ya zuba daga jikinsa,hkn ne yasa suke tunanin da wuya Aeezad ya rayu sbda jinin daya zubar yayi yawa., har kwara Adamu ma yana iya rayuwa sede kafarsa da wuya ta moru. Cikin hanzari jirgin ya tashi sama aka nufa cikin garin Kano dashi domin Nan yafi musu saukin zuwa, direct babban asibiti aka nufa dashi, tini Yan jarida sun fara watsa labaran hakan a gidajen Redio da gidajen TV, domin tini Suma sun hallara dajin tin kafin a dauke Aeezad da adamu suka samu nasu rahotannin,, Nan da Nan Nigeria ta kideme da zallar tashin hankali, iyalansa dasukeda tabbacin a cikin sojojin dasuka rasa ransu akwai nasu suka hau koke koke. ** ** ** Dai-dai Alhaji sunusi dake zaune falonsa Yana kallon news wannan Labarin ya fado masa, aka nuna konewar motar sojojin sannan aka saka picture din Aeezad Dana adamu, cikin tashin hankali daddy ya tashi tsaye, sbda tini ya gane dansa ne tilo dayafi kauna a fadin duniyar Nan, ko daga bacci ya tashi ze gane d'ansa koda a cikin dubu dubu ne. "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!'' alhaji sunusi ya dauki salallami kusan sau uku a jere cikin ihu tamkar ze fasa falon nasa, ya jawo wayarsa ya fara kokarin neman number din shugaban sojojin nigeria, Yana Shirin kiransa yaga Kiran shugaban sojojin yashigo wayarsa. Nan gabansa ya yanke ya fadi Yana dagawa yace "Ina d'ana? Da gaske ne abinda ya faru da Aketa yad'awa a labarai..." Daddy ya fadi a rude yayinda yakeji kmr zeyi hauka dai-dai hajiya rafi'ah ta sakko daga upstairs cikin tashin hankali sbda karar dataji mijinta nayi, ta iso ta taddashi cikin tashin hnkli Yana waya. Nan shugaban sojojin ya tabbatar masa da abinda ya faru, ya sanar dashi yanzu suna babban asibitin dake cikin garin kano,. "Ka gayamin Dan Allah D'ana ya rasu ne?" Shine abinda daddy ya fadi yayinda idanuwansa tini suka kad'a sukayi jajawur. "Ka kwantar da hankalinka, be mutu ba..." Alhaji sunusi yace "Karya ne!! Karya ne!!" Ya fadi kmr zatautacce,jikinsa kawai ya basa d'ansa baya raye. Jin abinda yake cewa yasa rafi'ah shiga tashin hankali itama, Nan tashiga Fadin "meya faru wani d'an kake nufi? Bade Aeezad ba mijin y'ata... " Rafi'ah ta fadi cikin tashin hankali da rudewa. Katse wayar daddy yayi domin baya fahimtar me nacikin wayar ke fadi, cikin tashin hankali yashiga kokarin Kiran sakataransa bugu daya ya daga,. "Ase mana fly zuwa kano..." Yana fadar hkn cikin tashin hnkli ya katse wayar, ya ajiyeta gefe Nan kiran jama'ah ya fara shigowa wayar Ciki harda Kiran shugaban kasa, Nan take Alhaji -sunusi ya tabbatar da dagaske abinda idanuwansa suka gani ya samu tilon dansa. Rafi'ah dake tsaye se tambayarsa takeyi meya faru ya kasa mgna dukyabi ya fita a hayyacinsa, se zufa kawai yakeyi, duk sanyin AC dake falon baya ji a karshe ma zafi yaju AC na sakarwa,. Nan take kwallah ta wanke masa kunci, duk dauriyarsa seda kwallar suka subuce masa. Hankalin rafi'ah ya kara tashi ganin abinda bata taba gani ba a cikin idanuwan mijinta ba wato kwallah se yau, yanada dakiya da dauriya. "Meya faru Alhaji ko mutuwa Aeezad din yayi?'' ta tambaya a matukar rude. "Yan ta adda ne suka Kai masa hari, sun samu nasarar harbinsa,sun kashe kaf masu tsaronsa se mutane biyu ne suka tsira......" "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!'' hajiya rafi'ah ta dauki salati cikin gigita, tace "Bade ya mutu bade ko!?"cewar hajiya rafi'ah da hankalinta ya tashi Ainun Nan take yarta ta fado mata Rai watta take Egypt, rafi'ah ta tabbatar in yarta tasamu wannan labarin seta kusa hauka sbda kaunar datakewa Aeezad, uwa uba ma ita tunaninta karya mutu da wuri ya maida mata yarta Karamar bazawara. "Jeki Sako hijjabinki yanzu zamu tafi kano..." Alhaji sunusi ya fadi murya a rikice yayin daya kagu yaga d'ansa ko hnklinsa ze d'an nutsu. Ba bata lokaci hajiya rafi'ah ta Sako hijjabinta Alhaji sunusi dagashi se jallabiya ya fito harabar gidan, kaf ma'aikatan gidan duk sunyi jungum jungum domin sun gani a TV wasu kuma sun sauran. Ba bata time suka shiga mota dreva yajasu zuwa Airport, ba bata lokaci suka shiga jirgin ya daga zuwa garin Kano a jirgin ne Alhaji ya kira hafsat domin ya sanar da ita domin yaga bega kiranta ba, yasan da wuya inta sani. Aiko hafsat bata sani ba tanata Aiki, in tana Aiki Sam bata bi ta kan wayarta, tana aikin tanajin anata kiranta kiran dayake shigowa wayarta yafi kira dari biyu tanaso ta daga sbda Kiran yayi yawa ba a taba mata irinsa ba se kuma aikin yasha mata Kai, tana office ta rufe da key. seda hafsat taga kiran mahaifinta a kn wayar kana ta daga Nan ya shaida mata abinda ke faruwa,ya kare da fada mata suna hnyar zuwa garin kanonma yanzu. "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!!' itace kalmar dake fita daga bakin Aunty hafsat ta saka kuka, ta kasa mgna ma kawai se kukan tashin hnali ya kwace mata, Nan take ta fara ganin duniya na koma mata portrait. Batasan sadda ta cillar da wayar hannunta ba ta dauki car key dinta tana tafe tana tangal tangal tana kuka,ta fito daga office dinta, tini ma'aikata abokan aikinta suka shiga mata gaisuwa rasuwar kaninta, dansu a yadda sukaga Aeezad a TV sun sadakar ya mutu kawai. Jin yadda aketa mata gaisuwa ya kara daga mata hankali, wato AEEEZAD ma ya rasu kenan daddy boye mata yayi. Nan wani Jiri ya debeta saura kadan ta fadi Amma ta dake, ta fito ta nufa motarta, tana kokarin shiga dreva side, abokiyar aikinta halima ta karaso ta amshi car key din a hannun hafsat domin ta fuskanci in hafsat taja kanta a motar baze haifar da d'a me Ido ba. Side din me zaman banza halima takai hafsat ta zaunar da ita kana ta dawo side din me tuki tashiga taja motar zuwa gidan hafsat. Tinda suka taho a motar hafsat ta lumshe idanuwa se kwallah keta ziraro mata kalmar Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un! Ta kasa tsinkewa a kan harshen aunty hafsat, sosai halima ta tausayawa hafsat se natsiha take mata na duk me Rai mamacine ina ai hafsat ma batajin Sam me halima kece mata. A haka suka iso gidan, ko packing halima bata gama ba hafsat ta fita a motar tana tafe tana tangal-tangal har faduwa tayi ta tashi, a falo ta zube ta tsinci kanta da fashewa da Wani irin kuka me tsananin sautin kara, halima tashigo tashiga rarrashin hafsat. Nabeelah dake dakinta tana kwance har zuwa yanzu kasan tiles taci kuka ta kushi har muryarta ta disashe, kmr daga sama tajiyo kukan hafsat daga falon yayinda cikin kukan taji tanata fadin innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!. "Wani mummunar lamarin ya faru..." nabeelah ta fadi Cikin tashin hankali ta mike yayinda bata ganin gabanta ga idanuwanta a bude a zahiri Amma a kulle suke domin bata ganin komi se lalube kawai takeyi,da laluben tasamu ta fito daga dakin nata ta iso falon, se lokacin ta Dan fara ganin Aunty hafsat dake Tsugunne tana kuka yayinda halima keta Mata natsiha tana fadin "Kiyi hkri duk me Rai mamaci ne,muma duk lokacinmu muke jira..." Aunty hafsat na ganin nabeelah ta fito ta kara saka kuka tana ganinta taji tamkar Aeezad take gani a kwayoyin idanuwanta. "Meya faru Aunty hafsat? Waya rasu? Dan Allah waya rasu?'' shine abinda nabeelah ke fadi cikin kidimewa da rudewa . A fari da nabeelah ta fito aunty hafsat ta kalleta tasha ko tasan da rasuwar ne sbda yadda ta ganta duk a gigice alamu sun nuna taci kuka ta koshi,seda tayi mgna ne ta fahimci batasan komi ba. "Aunty nabeelah Aeezad ya rasu...Yan ta adda sun kashe manashi,, wayyo Allah na innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!'' sune kalaman dasuka fito daga bakin Aunty hafsat zuwa kunnuwan nabeelah. Wani irin disashewa kunnuwan nabeelah sukayi, Nan take portrait din datake gani suka dawo cikin idanuwanta, ji tayi kmr a mafarki, kmr zararriya tashiga girgiza Kai tana fadin ''Ya rasu? Ya rasu? Ya rasu? Wallahi karya ne be rasu ba, ynzu muka rabu dashi....wlhi be rasu ba karya kikemin Aunty hafsat..." Nabeelah ta fadi a matukar gigice cikin fitar hayyaci, bata tabajin kalmar data fi komi daci a zuciyarta da daga mata hnkali ba kmr wadda taji ynzu daga bakin Aunty hafsat, Adduarh takeyi Allah yasa bacci takeyi tana mafarkai, da tabbas inta tashi daga baccinnan bazata kara bacci ba harta komawa mahaliccinta, Wani irin Abu ne daci yazo ya tokare mata kahon zuciya. "Ba karya nake ba Aunty nabeelah...da gaske Aeezad ya rasu!'' cewar hafsat da tuni itama tayi loosing controlling, halima Kam tuni tadawo da natsiharta kan nabeelah domin ta kula nabeelah tafi hafsat fita a hayyacinta. "Wayyoh Allah na.... innalillahi wa'inna ilaihirraju'un! Wallahi da gaske ne Naji a jikina, Wani Abu ya sameshi...Naji a jikina,Naji a jikina! "" Nabeelah tashiga fadi cikin ihun fitar hayyaci, Kmr zata fasa falon da