Sashe 8
Nahuce Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
"Habibu Mustapha Nahuce (Lucky), Young Nigerian Hotels Owner, the Proprietor of NAHUCE GROUP OF HOTELS, Excutive Director TRANSCORP HILTON, NIGERIA.......
(With so much interest) hadi da mamaki da dokantuwa, wani irin inquisitivity and curiousity, Raheenah ta ci gaba da surfing tana bin bayanan wadanda duk sun kunshi gwagwarmayar rayuwar Habibu ne, ta neman ilmi, ta fadi-tashi a Jamus, da ayyukan Hotels a gida Nigeria, saicurrent hotunansa wadanda suka kusan gusar da numfashinta.
Yana nan a handsome HABEEBUNsa, dan gayun nan wankakke, mai iya daukar wanka, mai iya sanya karin hula, kuma dan kwalisar shi yadda ta san shi a baya cikin birnin Cologne, sai wata 'yar kiba ta hutu da zaman naira a muhallin ta ya sabbaba kawai da ya kara, hadi da wani irin kwarjini da kamala wanda rikon addini ke haifarwa mutumin da ya rike addinin sa da gaskiya, ya kuma san ciwon kan sa (at approaching 40).
Numfashin Raheenah yayi balaguro na tsayin lokaci daga kirjin ta.
Ba ta iya ci gaba da karantawa ba, haka bata iya cigaba da kuma kallon hotunan tallbuildings din NAHUCHE HOTELS dake kasa ba ta kifa fuskar kwamfutar ba tare da ta kashe ta ba.
Numfashin ta na racing...cikin sassarfa, zuciyar ta na wani irin bugu cikin ragaita... So Habibu yana can kasar shi Nigeria yana progressingto such extent harya manta da ita. Ya manta an yi halitar ta. Mai wannan tarin achievements din ina zai tuna da wata halittar Allah mai suna RAHEENAH! Ya gama cimma komai na rayuwa, da duk wani buri da dan adam ke da shi, watakila ma har aure ya yi ya dau Dan ta Abdallah ya baiwa wata, in ba haka ba yaya zai yi da yaron???
Wannan tunani ya dugunzuma zuciyar Rahinah. Kishi da bakin ciki matsananci suka lullube ta. Kawai sai ta ji hawaye na saukar mata duk da ba na regret bane, na tunanin ya dau dan da ta sha wahalar dakon cikin sa wata tara da nakudar sa ya baiwa wata ne. Watan da ta ke da tabbacin ba zata rike mata Da sabida Allah ba sai don wannan dukiyar HOTELS da aka tara.
Ba ta san lokacin da ta sake kunna kwamfutar ba ta koma kan browser din ta ta rubuta 'HABIBU NAHUCE'S WIFE', amma kuma no result matched her search, ta yi sau ba adadi ba ta ga wata mace associated with him as a spouse ba, sai Daractoci da manajoji na hotels din shi, wadanda duk kabilu ne.
Wata nannauyar ajiyar zuciya ce ta kufcewa Raheenah, amma sai wata zuciyar ta ce,
"Kada ki yi saurin sauke numfashi Rahinah, watakila yana daga cikin mazan da ba sa exposing matan su a internet, ko da gani ma wadannan bayanan duka ba shi ya dora su ba, website ne na hotel din sa ya dora, ya kuma kunshi dukkan bayanan da suka shafe shi.
Da sauri ta soma binciken babban location na shedkwatar Nahuche Hotels, da kuma ainahin jihar da garin NAHUCHE yake, ba jimawa adireshin ya bayyana;
'ZAMFARA STATE, NIGERIA'.
Ta koma da baya ta jingina da allon gadon ta tana wani irin lumshe idon ta.
So Habibu dan Zamfara ne kenan all these while ba ta taba sani ba. Yau har karamar hukumar da garin Nahuce ke ciki sai da Rahinah ta binciko (aiki ya samu manyan mata) Ranar dai baki dayan ta ta zama ta DAN NAHUCHE jikan NAHUCHE ce a wajen Raheenah.....
Gabadaya ta birkice a searching din komai da ya dangace shi, sai da ta binciko komai concerning Young Nigerian Hotels Owner Habibu Mustapha Nahuche. Ba kuma da nufin za ta taba neman sa ba; she is only infatuated and truely in LOVE... ba tare da ita kanta ta san soyayyar gaskiya ke dawainiya da ita a daidai wannan lokacin ba.
Dankwalin kan ta yayi nasa wuri gashin kanta na fulanin usli duk ta hargitsa shi kamar yadda ta hargitsa zuciyar ta da tunanin ta.
Duhu na neman shigowa, har zuwa lokacin Raheenah na bisa kwamfuta ba tare da ta tuna da abincin rana ba. Wanda ta ce ma Nene in ta gama abinda take yi zata zo ta dauka.
Jin shiru har karfe shidda na yamma Rahinah bata fito ba sai Nene ta shigo mata da shi tana tambayar ko lafiya ba ta fito cin abinci ba gashi har an gama na dare? Idanun Nene Balki suka kai kan allon kwamfuta (screen) inda ta hango fuskar Habibun su ta cika screen din, da alama zooming hoton ta yi. Tana kara kallon kyakkyawar fuskar sa da kyau. Da sauri ta kife fuskar kwamfutar ba tare da ta kashe ta ba. Nene ta yi kamar ba ta gani ba, amma ta kusa sakin salati don mamaki, ta ajiye mata abincin da ta biyo ta da shi, ta ce.
"Ki daure ki ci abinci ki koshi, sai ki fi jin dadin tada tsumin tsohuwar soyayyah".
Raheenah ta yi maza ta rufe ido ruf! Tare da dora hannayen ta biyu a kai kamar ta ce, "wayyo Allah kasar ta tsage ta shige". Nene ta gani, ta gan ta da hoton Habibu cikin kwamfutar ta! Yau ina za ta sa kanta da wannan dingimemen abun kunya???
Nene ba ta tsaya sauraron borin kunyarta ba ta juya ta fice daga dakin. Ba ta kuma tsaya ko'ina ba sai falon Ambasada, ta labarta masa abin da ta gani a kwamfutar Raheenah yau. Mamaki kamar ya kashe ta.
Ambasada Shehu Bichi murmushi ya yi, ya ce,
"Shin ke Nene da can kin dauka wai ba ta sonshi ne? Ai ki bar bacin rai a lokacin da yake cin zuciyar diya mace. Sannan shi bacin rai (is mortal but love is inevitable). Amma kuma duk da hakan zuciyarta mai rauni ce a kan ta Da namiji. Bari ta gama karatun ki sha kallo, da kan ta za ta nemo shi duk inda yake.
A lokacin ne yake gaya mata shi ya san inda Habibu yake, (Habibu is now a successful business tycoon) a garin Zamfara, amma har gobe bai yi aure ba, me ye dalili? Wanda ke nufin uwar dan sa yake jira TA HUCE DAGA FUSHIN TA.
Ya kara da cewa, abin da ki ka ga tana yi yanzun, alamu ne na ta fara HUCEWA, sai mu ba su lokaci su duka, mu kuma bi su da kyakkyawar addu'a.
Amma a yadda na fahimta Habibu na da zuciya, soyayyah ba ta rufe masa ido ya kasa sarrafa kan sa.
Idan kin ga ya yarda ya maida Raheenah to fa sai dai idan ita da kanta ta neme shi, ta ba shi tabbacin amincewar ta a kan komawar ta dakin ta. Ya riga yayi zuciya da Raheenah. Yayin da ita kuma Rahinatu in kin lura akwai ta da ki-fadi (mawuyaci ne hakan ta kasance daga bangarenta)".
Nene ta dinga jinjina kai. Ta rasa abinda zata ce.
*****
COLOGNE, ALUMNI
A
yau ne jamiar Cologne ta kasar Jamus, jamia mai dadadden tarihi, ke bikin kammala karatun su Raheenah daga jami'ar wato (convocation ceremony). Duk inda ka duba dalibai ne daga kasashe daban-daban na duniya, tun daga Amurka, Birtaniya, Asia, Africa and Latin-America. Suna saye da bakar rigar kammalawa (convocation gown) da hular ilmi, farare sun cakude da bakake ba ka iya tantance nationality din kowannen su.
Dr. Raheenah Omar, ta fita da matsayin overall best student a department din ta (Otorhinolaryngology) ta karbi wannan kambu daga shugaban jami'ar Cologne. Ta karbi membership daga (AFHNS) wato (African Head and Neck Society) da kuma (ORLSON) wato (Otorhinolaryngocological Society of Nigeria).
Kamar yadda ta yi wa kasar ta alkawari, wannan ne lokacin dawowar ta gida bakidaya domin ta taimaka wa kasar ta ta amfana daga ilmin da ta tsaya mata ta yi.