← Book details Nahuce Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 16

Sashe 2

Nahuce Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daki suka shiga, Habib ya shigo da jakunkunan sa, kafin ta yi komai flask ta jawo wanda dama ba ta rabo da kunun tsamiya a cikin sa, ta zuba a kofi ta saka dan suger ta motsa ta soma kokarin baiwa Abdallah.
Kasancewar Yafendo tana ba shi ya san kunu sosai, ya karba yana sha, ta dora shi a cinyoyinta tana rirriga shi, sannan ta maida hankalinta kacokam a kan Habibun, wani irin mabayyanin bacin rai kwance-kwance baro-baro a kan dattijuwar fuskarta.
"Yanzu Habibullahi wuyan ka har ya yi kaurin da za ka yi aure kan gaban kanka babu sanin kowa naka?
In Shafa'atu ce ba ka so ai ba sai ka yi haka zan san ba ka son ta ba, wane irin aure ni 'ya su sai ka ce wasan yara? Ina uwar dan da za ka dauko wannan dan tatsitsin yaron tun daga wata uwa duniya kai kadai?"
Habibu Nahuche, bai taba barin weakness din sa ya bayyana a gaban kowa ba, amma wannan UWA ce MAHAIFIYA ce, kafadar da kowanne dan Adam ke iya sauke damuwar sa babu haufin komai. Don haka sanda ya fara hawaye bai san sun zubo ba, dacin tuno kiyayyar Rahinah gare shi, sai da ya ji saukarsu a kan kundukukinsa, da damshinsu a kan fuskarsa.

"Na yi duk iya kokari na a kan ta so ni, ta zauna da ni mu raini dan nan da Allah ya bamu tare abu ya faskara. Ban san meye aibu na har haka ba da Rahinah ta ki ni. A karshe mun rabu, rabuwa ta har abada, ni kuma na dauke Dan ba da saninta ba, amma marikanta sun san na dauke shi".

Ya kwashe gaskiyar komai, har sanadin auren ba-zatan ya gaya mata, sai dai wani sirrin ai bai faduwa, balle sirrin aure. Ya tsaya ya kafe a kan Raheenah ba ta sonsa kawai, sabida ya aure ta baa hannun iyayen ta ba, yace aurensu kaddara ne kawai da rabo rantsatstse daga Allah.

Haj. Kaltume ta rasa abin da za ta ce, amma sai ta ji ya fi mata a kan a ce Habibu zina ya yi ya kawo mata yaron nan. Ta rungume Abdallah sosai a kirjinta, wanda zuwa lokacin ya samu barci yana sauke ajiyar zuciya.

A daren ranar ta kira Badiyya wadda ke aure a garin Kaduna, ta ce duk abin da ta ke ta bari gobe ta zo Zamfara maganar ta fi karfin waya.
Sannan ta sa almajiri ya share wa Habibu dakinsa, ya wanke masa toilet dinsa, sannan ya shigar masa da dukkan kayansa.
Girki na musamman ta yi musu, tuwon shinkafa da miyar taushe da naman saniya zuku-zuku a ciki, ta yarfa man shanu sannan ta hadawa Habibu kunun zaki kasancewar yana son shi sosai mutumin sa ne, amma na gasara ziryan ba na farau-farau ba.

Da dare ya yi Abdallah ya rikice kan bai kwana tare da Hajiya, sai Momin sa, don haka tare suka tafi dakin sa dake zaure yana ta rarrashin sa, sai da ya yi barci ya dauko shi ya maido wa Hajiyar shi.
Hajiya Kaltume tana sallahr dare kamar yadda yake a aladar ta, jefe-jefi tana juyawa tana kallon kyakkyawan yaron dake barci cikin nutsuwa a gefen ta mai tsananin kama da Habibu, tamkar Habibun a lokacin da yana kamar sa, kaunar yaron na dada shiga ran ta, a cikin kowacce sujjadah data yi tana yi masa addua Allah ya raya shi rayuwa mai tsayi da albarka.

Cikin wannan daren mai dimbin tarihi a rayuwar Habib da Raheenah. Dukkan su babu wanda ya runtsa. Ya fidda layinsa na kasar Jamus ya karairaya shi, ya taune shi ya zubar, ya saka MTN NG da ya saya a filin jirgin saman Abuja. Yana fatan yadda ya karairaya shi haka ya zubar, zuciyar sa ta karairaya Raheenah Omar ta zubar, da duk abinda ya shafe ta.

Amma ko da ya so yin barci, sai barci ya ce dauke ni inda ka ajiye ni. Shin ko yaya rayuwa za ta ci gaba musu shi da Abdallah? Shi maraicin matar da yake so daya da daya a duniya? Abdallah maraicin uwar da ya budi ido da ita?
Wata Tambaya ce mai wuyar amsawa farat daya, da ya kasa amsawa kan sa, ya ce bai son ta ma ya san wannan yaudarar kai ne. Raheenah Omar, ta shigo rayuwar sa da wani irin karfi, ta yi tasiri mai yawa a cikin ta cikin auren da bai gaza kwanaki bakwai ba. Tasirin da kafin ya yi nasarar cire ta kwata-kwata, shi ma ya san zai sha wuya, kuma abu ne da ba zai tabbata a lokaci guda ba.
But gradually, by trying to follow the path of reality; yana fatan canzuwar kaddararsu, yana fatan Raheena ta bar zuciyarsa ta sha iska haka, ta bar kwakwalwarsa ta sarara, ta bar gangar jikinsa da ruhin sa su huta. Ta bar sababbin abubuwa da suka fi ta muhimmanci su shigo.

Ba shi ya iya runtsawa ba sai da ya dawo masallacin Kofar Jange sallar asubahi, sannan ne barcin gajiyar da ya tara ta zaman jirgi da shirye shiryen dawowa da ya jima yana yi ta karkashin kasa suka taru suka danne shi bakidaya.
******

Kukan Abdallah ne ya tashe shi wajejen takwas na safe, ya karade gidan da kuka yana kiran ABBANSA da MOMIN SA... cikin harshen Jamusanci. Zuciyarsa ta yi wani irin karyewa, anya cikin hukuncin da ya yanke babu zalunci a ciki ga yaron da ma uwar kan ta?
Yanzu haka yaron zai tashi bai san mahaifiyarsa ba alhalin tana raye a kololuwar duniya?
Da tsananin mutuwar jiki ya fito tsakar gidan hannayensa zube cikin aljihu. Ya zubawa yaron ido daga bakin kofar shigowa cikin gidan. Idanun sa sun kada Abdallah na ganin sa ya taho da mugun gudu ya rungume shi, sannan ya soma gaya masa cikin harshen da yafi iyawa ya maida shi gun Mummyn sa, tashi Mummy din ba wannan ba, yana nufin Hajiyar sa.
Hajiya Kaltume ta fito daga daki tana ta mita.
"Dan nema rigimamme, sakaltacce, ni bana son shagwaba ko kadan, da alama gidan ku can sun gama sangarta ka, in ba haka ba ta ya ya gotai-gotai da kai za ka saki kashi daga tsaye? A ba ka foo ka ki hawa?"
Murmushi Habib ya yi, shima ya san da gaske gidan Ambassada sun sakalta Abdallah, ya karaso inda ta ke yana dauke da Abdallahn.
"Ke da maigidan naki za mu gan ku a rana, Maman shi pampers ta ke saka mishi ba ta dora shi a wani foo".
Hajiyar Nahuce ta ce, "Au? Tunda irin 'ya'yan Badiya ne, to ba zan iya ba, ta zo ta dauki abin ta (Badiyar), su ma haka ta sangarta su da kin hawa foo, yaro dan shekara biyar sai ya saki kashi cikin auduga, mu ba haka iyayen mu suka raine mu ba, to ni ba zan iya wankin kashi a cikin pampers ba da girman yaro da komai".

Karshe Habibu ya je ya siyo pampers gari guda ya kawo mata, yana rokon ta kan ta lallaba Abdallah, a hankali zai koyi hawa foo din. Shi zai dinga yi masa tsarkin ya fidda pampers din. Hajiya sai ta ji su duka sun bata tausayi.

Sai wajen la'asar Aunty Badiyya ta iso daga Kaduna, Aunty Badiya ba ta kama da Habeebu sam, bazaka ce ma cikin su daya ba, don ita mahaifin su sak ta dauko, fara ce ita Barumiyar Nahuce, sabanin Habeeb da yake wankan tarwada.
Aunty Badiya 'yar boko ce sosai, domin kuwa (PHD holder) ce. A wannan lokacin ita ce mataimakiyar Provost ta (Kad-Poly), yayin da mijin ta babban ma'aikaci ne a Abuja, sabida aikinta ta ke zaune a Kaduna sai karshen mako yake zuwar musu.
Yaran Aunty Badiya hudu ne duk maza ta karshen ce kawai mace, Zarah, wadda ba ta fi sa'ar Abdallah ba.

Zuwan Badiya gida da ganin kanin ta da ta yi da Da, da labarin da ta tsinkaya daga bakin mahaifiyar su ya bata mata rai ba kadan ba.
Ta yi fadan kamar ta yi ya ya! A karshe ta ce, "Allah ya kara da ba ta son naka, Allah ya kara karawa, yanzu ai sai ka hakura ka zo ka auri mai son ka (tana nufin yar uwar sa Shafa'atu)".
Ita babban bacin ran ta yadda ya boye musu maganar auren nasa a Jamus, kamar wani wanda bashi da kowa, amma Hajiya Kaltume da ta ga fadan Badiya ya yi yawa, duk hakurin da Habibu ke ta bata ta ki sauraron sa, sai ta ce
"Maman Zarah, hakuri za ki yi mana, laifi kam ya riga ya yi sai dai tunda ya bada hakuri kuma ya ce ya yi ne don ya ceci kansa daga aikata zina a can, ai ina ga wannan ya isa hujjah, ni tuni na dauki kaddara.
Yaro Allah ya raya mana shi, Ya sa Mahaddacin Alqur'ani ne".
Badiya ta ce "Hakuri na daya ne Habibu ya auri Shafa'atu, ban ce ta rike masa yaro ba, ni zan hada da na waje na in rike, amma auren sa da Shafa'atu ya zama tilas".
Habib da yake neman a yafe masa, ba abinda ba zai yi ba a lokacin. Ya ce da Yayar sa Badiyya "ki bari na gama NYSC sannan a yi maganar auren, ni yanzu da ba ni da abin yi, da me zan yi auren?"
Badiyya ta ce, "A can Jamus da me ka yi auren? Cewa nake karatu kake a inda baka da kowa ma? Balle anan da mu zamu rike maka matar. Ka yi auren ka dandani dadin sa da rashin dadin sa ne zaa kyale ka ka ci gaba da zama a haka?
In dai Shafa'atu ce ba bakuwar zafi ba ce, za ta iya zama a gidan nan tare da Hajiyar mu, sai a gyara muku sassan Baba".
Mikewa ya yi daga gurin yana kakkabe rigar sa, har da kunkuni kamar kuturu yana fadin.
"Ke za ki dinga ciyar min da matar? An ce miki a Jamus ko kai dalibi ne kana rasa aikin yi da zai rike iyali? Nan kuwa fa? Ai ki ji da kan ki kawai Yaya Badiya, ki kyale ni in nemi kobo. In gwaninta za ki min, kawai ki kular min da Abdallah".
Chapter 2 · 0% Book details