Sashe 3
Nahuce Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Yaron da ya riga ya shige zuciyar Dr. Badiyatu Nahuce farat daya, har fiye da son da takewa Habibu, ta kara rike shi sosai a jikin ta tana hararar Habibu, a lokaci guda tana mamakin irin karfin jinin sa. Yaro kamar Habibu yayi kakhi ya tofar, bai da maraba da shi a lokacin da yana kamar shi. Addu'a ta ke cikin ran ta Allah ya ba ta lafiya da tsawon ran kula da Abdallah, kamar, ko ma fiye da yana gaban mahaifiyar shi.
A washegari ta juya da Abdallah gidan ta a Kaduna.
******
Ba jimawa da dawowar sa ya yi registration na tafiya hidimar kasa. Aka tura shi Kwara State, ya tafi ya bar Abdallah hannun Yayar sa Aunty Badiya.
Haka yaro Abdallah ya rayu karkashin kulawar Kakar sa Hajiyar Nahuce da Yar mahaifin sa Dr. Badiyatu Mustapha Nahuce, suna zuwa Kaduna ta sanya shi a Kindergarten na (Kad-Poly) tare da diyar ta Zahrah, kullum sai ta sauke su sannan ta wuce aiki.
Sha biyun rana ta sa masinjanta ya dauko su, a can ofis din ta za su yi ta wasan su a gaban ta har ta gama abin da za ta yi su koma gida.
In aka yi hutu kuma ta kawo shi Zamfara ya yi hutu a hannun Hajiya Kaltume, sabida wayon yaron da kokarin sa a karatu da hikimar sa da saurin shiga rai a wajen malamai (double promotion) aka yi ta yi masa ya koma Nursery 3 daga Nursery 1. Sanan duk karshen zango shi yake zuwa na daya a aji, kuma sai ya dawo da prizes gida. Dr. Badiya (is highly proud of her son Abdallah) tana fada a koda yaushe. Yana tuna mata da kuruciyar Abban sa shima haka yake da yana kamar sa. Duk inda yayi karatu sai yayi tambari.
Zuwa wannan lokacin Abdallah ya manta da Raheenah, ya dauki Badiya a matsayin mahaifiyar sa. Hajiya Kaltume da yake kira "Granny kuma ya san Kakar sa ce wadda ta haifi mahaifin sa. Yana kara girma yana fahimtar alaqar sa da kowa.
Tsakanin shi da 'ya'yan Aunty Badiya ba za ka taba iya bambance wanne ne nata wanne ne na kanin ta Habib ba. Yayyen nasu Musaddiq, Mubaraq da Mu'allim suna kula da shi sosai shi da Zarah, don kuwa Uncle Habib (yadda suke kiran Habibu) ba su ajiye shi nan kusa ba, suna matukar son shi, sabida yadda yake nuna musu kauna shima duk lokacin da ya zo ganin Abdallah daga Kwara. Kaunar jini ce ta cakude da kauna ta musamman wadda suke yi wa Uncle Habibu, ta shafi dan sa Abdallah. Ko kuda in suna da iko ba zai sauka akan Abdallah ba.
A haka ya kammala NYSC, sai Aunty Badiya ta karbi takardun sa ta baiwa Baban Musaddiq ya tafi da su Abuja don nema masa aikin yi.
Kasancewar Baban Musaddiq babban ma'aikaci ne a Federal Ministry of Commerce and Industry wadanda Federal Govt. ke damawa da su a lokacin. Ga shi ya san manyan ma'aikata a can Abuja domin ya dade yana aiki, sai bai sha wahalar samar wa Habibu aiki ba tunda abu ne na wa ka sani, gashi da (qualifications) na Cologne University, ya samu aiki mai gwabi a babban Hotel din NICON NOGA, a lokacin shi ne hotel din da babu na biyun sa a Nigeria. Kuma fannin da Habibun ya karanta kenan wato (Hotel Administration).
Habib ya dade a Nicon - Noga, matsayi iri-iri a ya rike a cikin ta, daga karamin matsayi zuwa sama, promotion kan promotion akai-akai. Wani irin mutum ne shi mai nasibi akan duk abinda ya sa gaba. Ba don haka ba manyan mukaman da yake samu akai-akai a NICON cikin 'yan shekaru kalilan da bai isa ya same su a yan shekarun ba. Don akwai wadanda suka fi shi jimawa amma basu kawo matakin shi ba, abin kuma har da kwarewa da baiwa ta daban (exceptional talent) da Allah ya bashi.
A lokacin ne aka bude babban hotel din Najeriya watau TRANSCORP HILTON inda Habib da wasu daga cikin manyan ma'aikatan (Nicon - Noga) suka samu karin matsayin komawa (Transcorp - Hilton), inda Habeeb ya rike mukamin mataimakin manager, ba kananan kudi ke shigo masa ba domin kuwa a Nigeria gabadaya babu hotel din da ya kama kafar (Transcorp - Hilton) a birnin tarayyah.
Yawanci turawa, larabawa da sauran jajayen kunnuwa ke sauka a can idan suka zo Nigeria kan harkokin su, sai ko kusoshin kasar mu, da manyan 'yan kasuwanni, da ke yin conferences acan.
******
NAHUCHE HOTELS, ZAMFARA
I
dea din mallakar hotel nasa na kansa ta dade da ginuwa a ransa. A hankali yake saving, har ya tada tubalin ginin karamin gidan saukar baki 'guest inn' a kasar shi ta haihuwa wato ZAMFARA.
Da nan ya fara kamar da wasa, sai gashi Allah ya sa masa albarka da ilhama a ciki, ya fadada guest inn din ya maida shi babban hotel mai zaman kan sa a jihar ta Zamfara cikin Gusau.
Sabida yadda ba ya tsauwalawa ne da kuma kyawun hotel din gami da nagartar ma'aikatan sa ya sa ya yi attracting customers da masu kudin Zamfara nan da nan, inda ya fara da yi masa branch a birnin Tarayya, daga nan sai Lagos, inda can ne ya zamo (headquater) na (NAHUCHE GROUP OF HOTELS).
A cikin shekaru goma da dawowar sa daga kasar Jamus ya mallaki hotels manya-manya a duka manyan jihohin Najeriya. Ba ya wata sana'a sai wannan wadda ya karanta yake kuma da experience a kai, wato (Hotel Administration), ya san duk wata hanya ta bunkasa hotels (gidan saukar baki) a zamanance daga (Cologne) inda ya yi digirgiri da masta.
Daga nan ne kuma 'yammata suka ce salamu alaykum, ta hanyar budewa Habibu wutar so da kokon bara, kamar za su cinye shi danyen sa, ga kuruciya ga rufin asiri ta ko'ina ya samu, amma babu iyali.
Ga kyau na Zamfarawan usli tushen garin Nahuche. Ko marmarin aure ba ya yi, ba abinda baa cewa a kan sa a dalilin rashin aure, lokacin da sunan sa ya fara karade kafafan yada labarai a matsayin (Young Nigerian Hotels Owner) wasu ma sun ce neman maza ya hana shi aure.
Irin wadanan miyagun maganganu da aka soma yi a kan Habibu Nahuche suna dawowa kunnen Yayar sa Badiya, kasancewar ta mai taammali da mutane daban-daban, ta sha titsiye shi ta ce, sai ya gaya mata ko ba shi da lafiyar da zai iya aure ne?
A irin wadannan lokutan, Habib Nahuche, dariya yake yi sosai, ya cewa Badiya,
"Ba ni da lafiyar ki ka gan ni da Da na mai tsananin kama da ni?"
Sai Badiya ta ce cikin kankantar da murya,
"To Habibu ko dai da gaske kana deviating ne saboda bakin cikin Maman Abdallah ta ki ka?"
A wannan karon ma murmushi ya yi wanda Badiya ta kasa fassarawa, yayi kasa da kai, sannan nan da nan murmushin ya bace daga kan kyakkyawar fuskar shi, sabida wannan ba shine karo na farko da yaji hakan ba (ana masa mummunan zargi), ya ce cikin Bazamfariyar Hausar shi mai dadin sauraro;
"Wannan kuma ai tsakkanin bawa... da Ubbangijinsa ne".
*****
Zuwa yanzu kam Shafa'atu 'ya'yan ta biyar kenan, tana auren ta a Talata-Mafara.
Da farko ta gwada jiran sa kamar yadda Badiya ta kwadaitar da ita har ya gama NYSC ya samu aiki, amma tunda ya sa kafa a (Nicon - Noga) ba ta kara jin komai a kan sa ba. Bata kara jin duriyar Habibu ba. Zumunci ma ya yi rauni tsakanin iyayen su a dalilin hakan don iyayenta sun dauki laifin komai sun aza a kan Hajiyarsa, a ganinsu da ta takura masa da tuni ya auri Shafa'atu.
Ita kuwa Hajiya Kaltume kullum Allah ta ke kai wa kukanta a kan auren dan ta Habibu, shi kuma ta bar wa zabi. Baa shaidar dan yau, amma ita kam ta shaidi nata. Sabida yawan ibada da tsaida sallah yana hani dga aikata alfasha wanda kuma kowa ya san dabiun Habibu kenan, ga yawan azumin tadawwui. Ta dade da sanin akwai abinda ya kulle a zuciyar sa tun daga kan Maman Abdallah. Wadda ita tasa ya ki jinin mata. Duk ya hada su yayi musu kudin goro. Har ila yau, Hajiya Kaltume ta gama fahimtar ba ya son Shafa'atu, in ta takura masa ya aure ta zaa bata goma ne daya ba ta gyaru ba. A lalata zumunci kuma auren bazai dore ba. Sannan ta fahimci baya yin wani abu na banza duk da ba tare take da shi ba a yawancin lokuta amma ta fi kowa karantar sa, bata taba jin yana waya da 'yammata ba. Don ba wayar da ba ya iya amsawa a gaban ta.
Ta fahimci in ta takura masa ya auri Shafa'atuba zai kula da ita ba don kwata-kwata yanzu hankalinsa bai kan mata. A duniya abu uku ya sanya a gaba; (bautar Allah da neman kudi, sai rainon dansa Abdallah, Dan da Raheenah Omar ta haifa masa).