← Book details Nahuce Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 16

Sashe 15

Nahuce Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Habibu Mustapha Bilyamin Nahuche, ya fito daga motar hotel dinsa yana taku majestically, zuwa cikin gidan Aunty Badiya.
Musaddiq ne ya fara taren sa a bakin kofar shiga falon, da runguma mai karfi yana fadin.
"Welcome Uncle Habib!"
Muryar Musaddiq ce ta fiddo Aunty daga kicin, murmushi fal bakinta ta ce, "Ban zaci za ka sauka haka da wuri ba. Musaddiq ka je ka taho da su Abdallah".
Musaddiq ya ce, "Aunty da kin kyale Abdallah sai Uncle ya ci abinci ya huta, yana zuwa zai ishe shi da zance da dumi ba comma ba full-stop".
Aunty ta ce, "Sai kuma Uncle din ya ce maka bai son ya cika shi da dumin? C'mmon je ka dauko su maza gidan Anty Hassu".
Habibu na jin su amma rabi-da-rabi don hankalin sa ya tafi ga wayar da yake ta amsawa akai-akai.
Kafin dawowar Musaddiq Uncle ya dawo, ita kuma Aunty da mai aikin ta ba su zauna ba sun dukufa shirya abinci bisa makekiyar darduma da aka shimfida a falon Uncle. Fita goma ko shiga goma za ta yi sai ta kalli Habibu ta yi murmushi, ba abin da ta ke tsananin so irin ganin reaction din da zai nuna idan ya ga Raheenah yau a gidan ta. Ko za a kashe ta ta san Raheenah ce ta farko, kuma ta karshe a zuciyar Habibun, ko da kuwa su duka a yau sun nuna musu ba su taba sanin juna ba.
Uncle Usman ya bi Aunty kicin ya ce, "Tana ina ne?"
Aunty ta yi dariya ta ce, "Tunda ta zo, tana daki a kwance ba ta fito ba, kamar wadda aka yi wa duka".
Uncle ya girgiza kai ya ce, "Bari in je in yi serving din sa abinci ya ci, idan ya gan ta ba zai iya cin abinci ba, ga shi ban san yadda kowannen su zai karbi dan uwan sa ba".
Ya juya ya fito, ita kuma Aunty ta hau kiran Musaddiq a waya don ta ji ko sun taho?
Uncle da kan sa ya zuba ma Habibu duk abin da Aunty ta dafa a kan plate guda yana ta jan shi da zance yana loda abincin a kan faranti har sai da Habib ya ce, "Abincin nan ya yi min yawa fa!".
Uncle Usman ya ce, "So nake ka tada komada daga wannan ramar taka, kai kenan kullum kamar a bushe ka fadi?"
Murmushi ya yi, ya ce, "Yaya dan Adam zai yi kiba alhalin rayuwar sa ba ta taba hutawa ba? Kullum cikin kujuba-kujubar nema yake, sannan babu iyali a gefe wadanda taimakon su zai sa ya yi kibar?"
Baban Musaddiq ya ce cikin halin ko'in kula,
"I can relate, I see".
Sannan ya tura masa plate din abincin gaban sa. Bayan ya aza cokali da fork akai.
Gab da zai gama cin abincin Abdallah da Zarah suka shigo, Abdallah ya yi kan sa da mugun gudu yana,
"Daddy na, oyoyo!"Ya rike shi sosai cikin jikin sa tamkar zai maida shi cikin sa yana sunsunar sa, ya ce, "Junior, me ka ke ci haka? Ni girman ka tsoro yake ba ni".
Dariya Abdallah ya yi daidai lokacin da Aunty ta shigo, ta ce, "Junior, je ka dakin Zarah za ka ga bakuwa tana barci, ka taso ta, ka ce ta zo in ji Daddy ya dawo".
Da gudu Abdallah ya fita don shi yaro ne mai bin umarni, yana fadin, "Daddy kada fa ka je ko ina, yanzu zan dawo".
Aunty ta zauna gefen Habibu tana yanka mishi apple, Daddy kuma na diban sa da zance.
Barci ta ke sosai, lokacin da Abdallah ya shiga dakin. Yatsun kafarta ya hau ja yana fadi da karfi, "Bakuwa ki taso ki zo in ji Maman mu, Daddy ya dawo".

Kamar a mafarki 'yar siririyar muryar yaron ta ke ratsa kunnuwan Rahinah Omar. Jin muryar ta yi tamkar busar sarewa cikin kunnuwan ta, ga shi sai kara maimaitawa yake yi. A hankali ta ke bude fararen idanun ta, wadanda barci ya sa suka canza launi tana kallon kyakkyawan yaron. Har idanun ta suka gama washewa sosai a kan sa.
The cute face looks so familiar... and the feelings for him is not a strange feeling. Abin nufi ji ta yi ba yau ya ginu a zuciyar ta ba. Wani daddadden feeling ne wanda babu irin sa (maternal love) irin wanda kowacce uwa ke da shi a kan dan ta, walau ta san shi ko ba ta san shi ba.
Amma a halin da ake ciki, Rahinah Omar ta ji kaunar yaron ne kawai a ranta ba tare da ta san daga ina kaunar ta keto ta fito daga karkashin zuciyarta ba.
Murmushi ta yi masa, sannan ta yunkura ta tashi daga kwanciyar ta sa hannu ta yafito shi. Matsowa ya yi gaban ta ya tsaya, a kintacenta zai yi shekaru goma, amma ba ta taba ganinshi cikin gidan ba, don haka tunaninta ya ba ta shi ne Junior da suke yawan ambata. Hannu ta sa a kan lallausar sumar kansa ta ce, "Kai ne Junior?"
Gyada mata kai ya yi, sannan ya juya zai fice.
Raheenah sai ta samu kanta da cewa cikin rawar murya,
"Junior ya ya sunanka na gaskiya?"
Sai da ya kai bakin kofa zai fice ya juyo ya ce, "Sunana Abdallah Habibu Nahuche!!"
"ABDALLAH NAHUCHE!!!
Rahinah ta maimaita a fili. A ina ta taba sanin wannan sunan?
Tamkar wadda aka fizga a zuciya ko kuwa aka tsikara sai ta samu kan ta da mikewa wuf! Ta bi bayan sa ko kallabin ta ba ta tsaya daurawa ba.
Dakin Aunty Badiya ta fara zuwa, babu kowa! Da sauri ta fito zuwa inda ta jiyo tashin muryoyin jama'ar gidan, wato falon Daddy.
Nan ta tadda su complete family yadda sukan zauna koyaushe. Amma a kusa da Aunty a tall, giant, handsomeman, ya bata baya, wanda duk hayaniyar da ke tashi a falon babu tashin muryar sa. It's either kamar bai falon, ko kuma akwai abin da yake yi da ya hana shi magana. Waya ce a hannunsa yana daddannawa, sallamar Rahinah Omar ta sanya shi wani irin dagowa in a slow motion.
Ita kuma ba tare da ta lura da shi ba ta nufi inda Junior yake can gefen Musaddiq yana ta zuba masa zance. Tamkar wadda ake controlling da remote haka ta nufi gurin yaron absentmindedly ta tsugun na a gaban sa, tafin kafarsa ta kama tana son tantance abin da ke cin ta a zucci.
Tawwadar Allahn data ke son gani tana nan a kan babban yatsar kafar sa, sai girma da fadi da ta kara.
"ABDALLAH!"
Habibu ya fada da karfi tamkar ya ga wani abun da zai cutar masa da Da. Irin tsugunnon da ta yi a gaban yaron, irin sa ta yi a gaban Ambasada Shehu Bichi tana rokon sa ya karbar mata 'yancin ta daga hannun sa. Bafullatanar mai yawan sumar kai, da hasken fatar da ko a cikin farare ita fara ce lamba daya tsugunne gaban dan sa, wadda cikin kowanne hali ba zai kasa gane ta ba, image din kyakkyawar fuskar ta ba zai taba gushewa daga zuciya da kwakwalwar sa ba.
Balle ma cikin shekaru goman da suka gabata, canjin da Rahinah Omar ta samu na halitta ba wani mai yawa ba ne. Canji ne kawai irin wanda nauyin shekaru ke haifarwa diya mace ba tare da ya canza appearance na kuruciyar ta ba. She is still that ravishing, glowing and sparkling lady fiye da yadda ya baro ta a Germany.
Sai ma wata 'yar kiba-kiba da ta kara mai nuna sukuni, wadata da kwanciyar hankalin da ta ke ciki.
Kiran da Babansa ya yi masa haka da karfi ya firgita shi, don haka da sauri ya kwace kafar sa daga hannun Rahinah ya nufi baban sa yana buya a bayan sa.
"Daddy boye ni, ni ma ban santa ba".

Ya yi daidai da lokacin da Rahinah ta juyo ta sauke ragaitattun idanunta a kan Habibu Nahuce, wanda ke kallonta babu ko kiftawa. Her Ex- Habibu ne! wanda ko mutuwa ta yi ta dawo ba za ta kasa gane shi ba, balle dan da ke tsakaninsu.
Kallon-kallo aka shiga yi tsakanin Habibu Nahuche da Rahinah Omar, kallon da ke rewinding duka incidents din shekarun can baya a Jamus, abubuwa da yawa da suka gabata na gilmawa a idanun su.
Chapter 15 · 0% Book details