← Book details Nahuce Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 16

Sashe 5

Nahuce Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Daddy Ambasada dan garin Bichi ne ta Jihar Kano, kowa ya san 'yan Bichi 'yan boko ne na ga-ni-kashe-ni. Gidan iyayensa har gobe yana garin Bichi, suna da family mai tsohon tarihi.
Sun sauka a Kano da daddare, daga filin jirgi wadanda suka zo tarensu kannen Ambasada ne su uku suka dauke su suka wuce dasu Bichi.
Kwanan su uku suna zaga dangi Yafendo da Nene na rabon tsaraba, suna kuma shan tambaya a kan bakuwar fuska Raheenah, cewa ta ke Daddy ke rikonta a Jamus, karatu ta zo. Sai da suka kwana hudu Yafendo ta kira Muqaddas kanin Daddy kuma cousin a gare shi, ta ce ya shirya mota gobe zai kai su Girei ita da Nene da Raheenah, Daddy Abuja zai wuce akwai taron da zai halarta na Ambasadodin Najeriya kafin nan da dawowar su daga Girei din.
Ambasada ya yi musu fatan alkhairi na Allah ya sa a dace ya kawo kudin fetir da na kashewa ya babbasu.
******

GIREI, ADAMAWA
T
afiyar su daga Bichi zuwa Adamawa ta basu wahala ba kadan ba. Musamman dake tafiyar mota ce zuwa Adamawa daga Kano. Sun jigata sun jijjiga wuni guda sur don ma motar lafiyayya ce.
Sai magriba suka shiga garin Girei, inda Yafendo ta ce Muqaddas ya tambayi gidan sarkin Fulanin Girei can za su je.
Raheenah sai rarraba ido kawai ta ke yi, tana jin wani irin nutsuwa da wani irin kwanciyar hankali na shigar ta, tun ma kafin a ce ga dangin Daadan ta. Kasar Girei da mutanen cikin ta kawai ta ke ta bi da kallo, irin feeling din da dan Adam ke ji lokaci na farko da ya taka fatherland din sa.

An kai su har gidan Sarkin Fulanin Girei mai ci a lokacin. Farin dattijo, siriri dan shafal da shi. Yana zaune a karkashin bishiyar darbejiya da ta yi wa kofar gidan sa rumfa. Suka sauko daga mota suka taka zuwa inda yake zaune, sai binsu yake da ido har suka karaso.
Tun daga nesa Raheenah ta kura wa siririn dattijon ido gaban ta na tsananta faduwa domin sosai yake kama da Dadarta.
"Jabbama-Jabbama (maraba-lale)". In ji Sarkin Fulani, su kuma suka tube takalman su suka karasa inda yake zaune a kan makekiyar tabarmar kaba, suka gaida shi ya amsa da madaukakiyar fara'a, sai kallon Raheenah yake yi da mamaki, domin da ganinta ka ga Sarkin fulani mai rasuwa, wato Umaru Modibbo. Fuskar ta sak ta jikoki sa dake cikin gida.
Yafendo ta kara gaishe shi, sannan ta gabatar da su daya bayan daya,
"Wannan sunanta Rahinatu, wannan Nene Balki, nikma Yafendo Mairama, mun taho tun daga Bichi ta jihar Kano don mu yi tambaya a kan tsohuwa (Rahin) da dan ta Modibbo Umaru Sarkin Fulani na nan Girei mai rasuwa shekaru kusan talatin da suka wuce.
Tunda na san shi ne a matsayin dan Rahin kuma sarkin fulanin Girei, shi ya sa kai tsaye na ce a nuna mana gidan sarkin Fulani mai ci a yanzu, wai an ce matambayi ba ya bata, hakane ko ba haka ne ba? Dadin dadawa muna da hoton ita marigayiya Rahin tare da mu".
Chapter 5 · 0% Book details