Sashe 12
Nahuce Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Uncle ya fita bai nan tun safe, ta ji hakan a bakin Mu'allim, don haka ta jefa jakarta a bayan mota ta shiga ta tayar, Sahura ma ta shiga ta yi reverse ta durfafi get, maigadi ya bude musu za su fice sai ga Mubaraq na shigowa.
Ta dan dakata ta sauke glass ya ce, "Aunty unguwa za ku je ne? Mummy sun kusa isowa har da Uncle din mu da Junior, ya dawo daga Belarus kuma anan gidan zai fara sauka ya ga Junior".
Murmushi ta yi, ta ce, "Mubaraq ana kirana da gaggawa a asibiti, so I must go now, na yi wa Daddy text, ka gaya wa Aunty zan kira ta in na isa Abuja. A gaida min Junior da Uncle din mu, wani lokaci za mu hadu ai insha Allah".
Da haka suka yi sallama da Mubaraq ta ja motar da gudu suka hau kwalta. Da ta tabbatar ta yi nisa da Unguwar Sarki, ta hau titin fita garin Kaduna fintinkau, har wata ajiyar zuciyar samun kubuta ta saki.
Daidai lokacin da direban Habibu Mustapha Nahuche, ya karya kan motar su kirar Camero, onedoor, mai dauke da tambarin (NahucheHotels4) mai lambar jihar Lagos wadda a ciki ya dauko Habibu daga filin jirgin saman Kaduna ya shiga gidan Aunty Badiya, da yake suna waya shi da aunty da kamar mintuna biyar da isowar su yana cikin motar yana waya bai kai ga fitowa ba itama ta iso tare da nata direban, wanda ya daukota daga Gusau, Junior a gefen ta, Zarah a gidan gaban motar.
Yana kokarin parking Mu'allim na isko su da gudun gaske sabida jin dadin ganin Uncle Habibu, kusan watanni ukku kenan basu gan shi ba, shi ya bude bangaren (owners side) don Habibun ya fito, tun kafin direban sa ya gama parking, ya kuma karasa ya bude wa mahaifiyar sa tata motar. Yana yi musu oyoyo dukkan su.
Aunty Badiya ta fito tana mika, cikin tsabar gajiya tana, "Wash Allah!". Sabida gajiyar zaman mota tun daga Zamfara har Kaduna.
Mu'allim ya ce, "Welcome Uncle, welcome Junior". Tare da rungumo kyakkyawan dan uwan nasa Abdallah wanke hannu ka taba dan Habibu Nahuche. Wanda ke sanye cikin tsadaddun shirt da wando masu duhun kala samfurin (Dolce&Gabbana).
Junior ya na fitowa ya ce, "Yaya Mu'allim ina kwallona da na ba ka ajiya?"
Hararar sa Daddyn sa ya yi, ya ce, "Kwallo? Kwallo daga zuwan mu za ka fara ko Abdallah?"
"Afuwan Daddy, ka sani in ban yi kwallo ba bana jin dadi, ni so nake ma in na gama jarabawa ka kai ni Manchester inzamadan Manchester United".
Dariya Aunty ta yi, ta ce, "Karewar buga kwallo kenan, wallahi Baban Junior in ba mu yi da gaske ba Junior dan kwallo zai zama".
"Allah ya sauwaqe!".
In ji Habibu cikin takaici, a ran sa kuwa cewa ya yi, "Ranar da Alhuda-hudar uwar shi ta gan shi ya kare da zama dan kwallo da me zan mata tutiya da shi na cewa da na yi, zan fi ta iya kula da shi?
Suna takawa zuwa cikin gidan Mu'allim ke cewa,
"Aunty Rahinah ta tafi, ta ce in ta isa Abuja za ta yi miki waya, an kira ta on emergency a wajen aiki".
Kwakwalwar Habibu ta tsaya cak! Da aiki, kamar yadda ya dakata da tafiyar da yake yi. Sakamakon ambaton sunan Raheenah da Mu'allim ya yi, but he didn't take it further, and he did not show any reaction. Rahinah nawa ce a duniya kuma ba tun yau ba yake jin zancen ita wannan Aunty Raheenar a bakin su. Ya fahimci wata 'yar uwar su ce makusanciya ta bangaren mahaifin su.
Aunty ta ce cikin takaici, "Amma Rahina ba ta kyauta min ba, sai fa da na ce ta tsaya yau za su hadu da Junior". Takaicin ta daya ta so yau Raheenah da Habibu su hadu, ko Allah zai sa a dace su yi wa juna, don dai ta dade tana shaawar gwada wannan saar tata a ran ta, don a ganin ta Rahinah ba daya take da sauran mata da Habibu yake gudu ba, tafi karfin namiji yayi mata kallo daya.
Habibu ya yi gaba zuwa cikin gida ya bar su yana ta amsa wayoyin da ke shigo masa, bai saurari zancen da suke yi ba.
Bai tafi ba sai da Uncle Usman ya dawo, sun dade suna tattaunawa a falon Uncle a kan harkokin su. Suna cikin maganar sako ya shigowa Uncle daga Rahinah.
Uncle I'm so sorry, an kira ni on emergency ba zan iya jiran dawowar ka ba, yanzu har mun shiga Abuja, Uncle ba ni da amsa ga umarnin ka, I have no one, I have only myself". Rahinatun ka.
Murmushi ya yi, ya san da ma za ta gudun, amma kawai sai wani bakon tunani ya shigo kan sa, a lokacin da ya daga ido ya dubi Habibu da ke cin abinci a dining din falon sa.
-Wace ce uwar dan sa? Me ya sa ko zancen ta bai taba yi ba?
-Habibu ya rayu ne a Jamus, haka diyar sa Raheenah, Habibu na da Da Abdallah, Raheenah na da Da ita ma mai suna Abdallah, amma ko zancen dan ba ta yi. Habibu ba ya zancen tsohuwar matar sa, Raheenah ba ta zancen tsohon mijin ta. Ambasada ya ce mijin dan Zamfara ne...! Matar sa Badiya da kanin ta Habibu sun fito daga Zamfara ne...
A fili Uncle Usman ya ce, "Ya Jamilal Munzar! (Wato, Ya Mafi Kyawun Masu Gani) Ka taya ni duba al'amarin nan".
"Habibu!".
Ya kira sunansa da karfi, wanda hakan ya sa Habibu dakatawa da cin abincin sa, ya dago lumsassun idanun sa yana kallon Uncle cikin mamakin karfin tone din da ya kira sunan sa da shi, Uncle ya mike jikin sa har rawa yake, ya isa ga dining din. Ya ja kujera wadda ke fuskantar Habibu ya zauna.
"Ka gaya min sunan Babar Abdallah, da garin da ta fito".
Da wani irin mamaki yake duban mijin Yayar sa, wanda yake tamkar ubangida a gare shi. Duk wasu achievements din sa a rayuwa Usman Girei shi ne sila, don haka yana da matsayin da ya zarta na siriki kawai, yana kallon sa ne a matsayin Yayan sa da suka fito ciki daya kamar matar sa Badiya. Yana da wannan kimar. Ban da haka shi tun barin sa Jamus harshensa bai kara ambaton sunan Rahinah Omar ba... In ya ji mutum dan Adamawa ne ma ba ya tsayawa a inda yake, kada tsautsayi ya sa ya kasance ya san Raheenah Omar ya yi masa zancen ta.
Muryar sa na rawa ya ce, "Uncle Usman me za ka yi da sunan ta da garin ta? Ina fatan ba neman ta za ka je yi ba? I don't need her in my life anymore...!"
Girgiza masa kai Uncle yayi. "Ba neman ta zan je ba, ba kuma bikon ta zan maka ba, hakkin haihuwa zan ba ta in kai mata dan ta ta gan shi ta san yana raye, kada hakkin su ya kama ka.
Shekaru goma decade guda ka raba Uwa da Dan ta....
Yaa Subhanallah! Sai a yanzu Uncle Usman ya kara tabbatarwa yar sa Rahinarsa ce uwar Abdallah da ya tuna farkon bayyanar Rahinah gare su an gaya masa Habibu ya sato shi ne daga hannun ta yana dan shekara daya.
Kuma tabbas Junior ya zo hannun su ne bai fi shekara dayan ba, ina kwakwalwar su da lissafin su ya tafi tuntuni suka kasa gane hakan daga shi har Badiya?
"Ka gaya min sunanta na ce Habibu, da garin da ta fito".
Ya fada wannan karon cikin karyewar murya da karewar kuzari a jikin sa.
Cikin in'ina da magana daga kasan can makoshi ya ce.
"Rah...Rahinah Omar... Adamawa...!!!"
Uncle Usman ya tsura masa idanu, ya kasa cewa komai. Hawaye suka cicciko a idanun sa, hawayen da bai san na tausayin Habibu ne ko na tausayin Rahinah ba? Shekaru goma suna dakon soyayyar juna da kuma Da a tsakanin su? Habibu bai gane halin da Baban Musaddiq ke ciki ba, kuma bai san dalilin ganin cikowar hawaye a idanun sa ba, sai gani ya yi ya tashi daga wajen, ya dauki wayar sa da hanzari ya yi waje.
Mikewa ya yi don ya kasa ci gaba da cin abincin ya nufi sassan 'yar uwar sa. Tana falo ita da su Junior sun kunna kwallo (ball) suna kallo shi da Mu'allim sai iface-iface suke. Tambayar da Baban Musaddiq ya yi masa ta sa duk ya birkice, idanun sa sun kada, afterten years yau ya ambaci sunan ta.
Kuma ba a fatar baki kawai ya fada ba, ya fada ne tun daga karkashin zuciyar sa, wanda hakan ke bankado rufaffen gyambon yana kaikayi da son neman agaji. A yadda Aunty Badiya ta gan shi ya shigo falon sai ta ce da karfi.
"Junior, kashe kwallon nan ku tafi dakin ku, zan yi magana da Daddy".
Mu'allim ne ya kashe suka fita, Junior na cewa da Abban sa, "Don Allah kada ka je hotel ka kwana, ka zo mu yi sharing daki na". Amma ga mamakin Junior Daddyn nasa bai iya ya ce masa komai ba, which is very unusual Junior ya yi magana ya ki kula shi.
"Zai zo Junior, ka karkade masa shimfida". Inji Aunty.
Da murnar sa ya fita yana cewa, "Thank you Mummy. You know I love you ko? Ke da Daddy?"
Murmushi Aunty Badiya ta yi, ta ce, "I know Abdallah, and Mummy da Daddy loves you more".
Da haka ya fice yana tsalle.