Sashe 14
Nahuce Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
"Ina so ki ba ni hankalin ki".
Baban Musaddiq ya ce da Aunty Badiya.
Ta gyara zaman ta tare da tattara masa kafatanin hankalin ta. Baban Musaddiq tun jiya ta ke ganin shi upset, ga waya akai-akai shi da wadanda ba ta san ko su waye ba, abu kadan ya dau waya ya fice ya gama magana sannan ya dawo, abin da ba halin sa ba, babu wayar da ba ya iya amsawa a gaban ta a baya.
Yanzun dai Nene Balki ce ta ba wa Ambasada shawarar ya kamata Badiya ta san komai, kuma a gidan ta ya kamata Habib ya ga Rahinah ba a Abuja ba, tunda a can Junior yake. Ba ta ga amfanin kin sanar da Badiya da wuri ba.
Shi kuma Ambasada ya gaya mata cewa, Badiya tana kullace da tsohuwar matar Habibu a kan ita ta hana dan uwan ta aure, da yadda ba ta taba neman ta ga dan da ta haifa ba inji Uncle Usman, Nene ta ce,
"Akwai fahimta da kyakkyawar mu'amala tsakanin Rahinah da matar kawun nata, insha Allah komai zai zo da sauki".
Don haka shawarar Nene Balki Uncle Usman ya bi yanzu. Ya ce,
"Maman Junior I have something special for you, mene ne zai zama tukwici na?"
Murmushi Dr. Badiya ta yi, ta ce, "Duk abin da ka ke so shi zan ba ka Daddy".
Ya ce, "Shin wace ce babar Abdallah ne, kuma a ina ta ke?"
Nan da nan Aunty Badiya ta canza fuska kamar ba ita ke ta fara'a yanzun ba, ta ce, "Daddy da zan ganta Allah kadai zai raba ni da matar nan, na tabbata surkullen su na fulani ta yi wa Habibu ya kasa yin aure.
Ban san ta ba, ko sunanta ban taba tambayar sa ba, sabida ba ni da wata alaka da ita. Yaron da ta haifa ta yasar, babu ko waiwaye ga shi nan Allah ya raya shi.
Ita kuma Allah ya yi mana shari'a da ita a lahira".
Uncle sai ya kama dariya, ya ce, "Wato fulani surkulle gare mu? Kuma 'yan Nahuche ai fulanin ne in miki kirarin garin ku Zamfara GALMA UWAR RUFI, ko ba ku son mutum ba ku hwadi. Ke kam ba ki yi galmar ba kin hwadi ba ki son matar Habibu, ga shi kuma ta zame miki dole, sai ki dau na Annabawa ki soma tunanin hanyar sulhunta su, tunda kuwa ba kowa ba ce 'yar ki ce Dr. Raheenah".
Kusan za a ce Aunty Badiya shidewar wucin gadin razana ta yi, sabida ta san Baban Musaddiq ba ya yin joke shi kai tsaye yake fadar komai. Ta kura masa ido ta kasa daukewa, shi kuwa sai lumshe mata ido yake yana gyada mata kai cikin ba ta tabbacin maganar sa. Da kyar Aunty Badiya ta iya cewa,
"Wace Dr. Rahinar?"
Shi kuma bai bata lokaci ba ya ce, "Ya ta Raheenah".
Ya kwashe labarin komai ya gaya mata, sak! yadda Ambasada ya labarta masa.
"Idan Ubangiji ya lullube al'amari, babu dan Adam din da ya isa ya bankado shi, sai a lokacin da Ya nufa. Don haka ki sauke duk wasu makaman yakin ki a kan Maman Abdallah mu taru mu taimaki yaran nan su koma auren su, don zan iya yi miki rantsuwa kan cewa soyayyar juna ta hana su aure.
"Yanzu me ye abin yi? Da me zan iya taimakawa?"
cewar Badiya cikin mutuwar jiki.
Uncle Usman ya gyara zama. Tiryan-tiryan suka soma tsarawa.
******
"Kin kyauta Rahina, ni da ma na san kafin in dawo za ki gudu, to duk abin da ki ke yi ki bari ki zo karshen satin nan, I'msure ba kya aiki asabar da lahadi, Sarkin Fulani ma ya ce ki biya ku gaisa idan kin zo".
Raheenah ta marairaice murya abin tausayi, ta ce, "Uncle, bana son zancen aure, don Allah Uncle ka kyale ni, idan ka takura zan iya kamuwa da depression, I have a lot to do I can't put myself in any relationship... Zan iya rike kaina Uncle, don Allah kada ka sake yi min zancen aure".
Murmushi Uncle ya yi, ya ce, "Na yi alkawari ba zan sake ba, za ki zo din? Weve planned a get together dinner na kammala karatun Musaddiq".
A hankali ta ce, "Insha Allahu zan zo Uncle, tunda ka yi alkawari".
Murmushi ya yi yana kallon matar sa Badiya.
"Finally, ta amince za ta zo din".
"To Allah ya sa shi ma ya yarda ya zo don ka san shi kamar tsuntsu yake, yanzu haka sai ka ji ya bar Lagos din ma".
Ta fada tana dialling number din Habibu Nahuche.
Har ta yi karar ta ta gama bai dauka ba. Tana kokarin sake kira sakon sa ya shigo.
"In a meeting, call later".
Murmushi ta yi, ta tura masa nata sakon.
Call me da zarar ka fito".
Yana fitowa din kuwa ya kira ta.
"Ya ya ku ke Aunty, ya Abdallah?"
"Sarki mai Abdallah, ni boarding zan kai shi in huta kallon kwallo. Za ka iya zuwa karshen satin nan? Baban Musaddiq ke gayyatar ka get together dinner iya mu i'mu na gama degree din Musaddiq and zaa yi hotuna da bidiyo don tarihi, don haka presence dinka is very vital".
Habibu ya yi dan murmushi, zumunci da 'yar uwar sa ba ya hada shi da komai, don ba shi da wanda ya fita a duniya bayan mahaifiyar su. Ya ce, duk muhimancin uzrurrukan sa yana bari sabida hidimar Aunty Badiya da iyalin ta.
"Zan yi squeezing time don ina da muhimman abubuwa a gabana a weekend din nan".
"A bar komai a zo mana, in babu kai abin ba zai yi armashi ba".
"I know Maman Abdallah". Da haka suka yi sallama.
Kusan a tare Habibu Nahuche da Raheenah Omar suka shigo garin Kaduna, shi a jirgi daga Lagos, ita a motar ta daga Abuja. Sahura na gefen ta tana zuba mata hira, amma ga mamakin ta ta kasa ce mata komai. Yau jin kan ta ta ke kamar an dinke mata baki, an cire dukkan kuzarin ta. Ba ta san hakikanin abin da ke damunta ba.
Raheenah ta riga Habibu isowa gidan Uncle, kuma kai tsaye sai ta wuce dakin ta na gidan ta kwanta, don duk yaran gidan Aunty ta kwashe su ta kai su gidan aminiyar ta a Malali, ta ce sai takwas na dare za ta turo a dauko su. Musaddiq ne kawai a gidan, don haka bayan sun gaisa da Aunty ta ce ba ta jin dadi, kwanciya za ta yi kamin Uncle ya shigo gida. Da ma kuma tana hutun sallah.
Ba a fi awa guda da kwanciyar Rahinah ba Habibu ya iso, karkashin rakiyar ma'aikatan Nahuce Hotel na garin Kaduna, wadanda suka dauko shi daga filin jirgi. Motoci uku jibga-jibga kamar su fashe don koshi da sheki, kowacce dauke da logo na NAHUCE GROUP OF HOTELS. Sanye yake cikin black-greyGerman-Suit wadda ta fiddo zahirin ilhama da cikar zatin sa, kwarjininsa ya fiddo zahirin matashin miloniya mai tashe, HABIBU MUSTAPHA NAHUCHE wanda kallo daya za ka yi masa ka tabbatar Allah ya gama yi masa kowacce irin ni'imar rayuwa.
Kallo daya ba zai gamsar da idon ka a kan HABIBU NAHUCHE ba, ba tare da marmarin ka yi masa kallo na biyu ba. Idaniya ba sa taba gajiyawa da kallon sa sabida wani sassanyan sirrantaccen kyau da haiba da Allah ya yi masa.
"The successful business tycoon of Zamfara".
Kamar yadda kafafen yada labarai ke kiran sa.