← Book details Nahuce Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 16

Sashe 16

Nahuce Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

A take Rahinah ta soma ja da baya cikin tsoro da kidima. Tsoron da ya haifar mata da karkarwar jiki da ta zuciya, amma ga Habibun, ba zan iya cewa ba.
Domin kuwa bayan idanun sa sun farfado daga shock din ganin ta a inda bai taba tsammani ba, wato a gidan Yayar sa, ya kara yi mata kallo na biyu, kallon da ya tattaro duk wani kundi da ya lullube a karkashin zuciyar sa. Ya bude shafukan sa filla-filla, shafukan tun shigowar Raheenah cikin rayuwar sa, and the roles she played in shattering it (da rawar da ta taka wajen yagalgala ta).
Eh, ya kira shigowar ta cikin rayuwar sa ba komai ba sai kacaccala ta (shattering dinta intopieces) tunda har yau ga shi nan a gantale bisa titi yana ragaita babu iyali, in an kuma bi salsala wannan bafullatanar ita ce sila.
Domin kuwa soyayyar ta ce har gobe ke azabtar da shi ko na second daya bai taba hutawa ba. The marital physical relationship din da ya wanzu tsakanin su, will forever remain green a zuciya, gangar jiki da kwakwalwar sa, wanda ya dusar da hasken duka sauran mata daga idanun sa yake musu kallon ba bambancin da nasa jinsin, sai ita kadai ce mace a idanunsa.
Ba zai gaji da cewa ba Rahinah Omar ta tafi da dukkan farin cikin sa, sannan dawowar ta a yau ya san yana nufin abubuwa da dama in bai yi wa tufkar hanci ba.
Tunda ita tamkar mala'ikar daukar rai ta ke, ba ta zuwa ta tafi, ba tare da ta kashe zuciyar mutum ba. Ta zame masa tauraruwa mai wutsiya ganin ki ba ALHERI ba. Yana cikin tattala 'yar ragowar rayuwar sa da ta riga ta kashe ya samu control din ta a yanzu, shi ne kuma ta dawo cikin rayuwar sa ta inda bai zata ba.
A wannan karon, a wannan lokacin, a wannan 'yan dakikan, Habibu Nahuche, ya kudiri aniyar yaki da dawowar Rahinah Omar cikin rayuwar sa. Ba zai bari ta sake yin galaba a kan sa ba. Ko da wacce ta zo zai tarbe ta kyakkyawar tarba irin ta yakin ceton rai.
Ko da ma can ya san tana existing a garin Abuja matsayin cikakkiyar otorlaryngologist din National Hospital da NIZAMIYE. Yadda aka yi ta zo gidan Yayar sa ne bai sani ba, watakila wani ya gaya mata ga inda dan ta yake shi ne ta zo, za kuwa ta sha mamaki in ya ce mamaki, yana nufin mamaki mai gigita kwanyar diya mace. Domin daga yau Abdallah zai bar gidan Badiya.
Hannu ya sa ya janyo Abdallah da ke faman buya a bayan sa, ya yi masa kyakkyawar mafaka a kirjin sa, ya rungume shi sosai idanun shi a lumshe.
"Don't be afraid Abdallah, I'm here with you babu mai taba ka sai ruwan sama".
Daga nan ya mike tsaye rike da hannun yaron, kyakkyawan kallo na biyu wannan Rahinah Omar ba ta samu daga gare shi ba,
"Maza Abdallah debo kayan ka tafiya za mu yi".
Daga Aunty Badiya har Daddy bin sa suka yi da kallo kallo na mamaki. Domin ba haka suka yi zato ba. Yayin da Dr. Raheenah ta sunkuyar da kai, hawaye fal idanun ta. (Between happiness and excitedness) ba ta san wanne ta ke dulmiyewa a cikin sa ba. Abdallahnta... her only son Abdallah... after a decade, yau shi ne tsaye a gaban ta gidan Uncle din ta.
To ta ina ya zo? Wannan na nufin... shi ne Junior din, dan kanin Aunty Badiya... wannan na nufin Habibu Nahuche... shi ne kanin Aunty Badiya. Ta wani irin lumshe idanun ta a hankali, tsigar jikinta na tashi, ko kafin ta farfado daga shidewar wucin gadin da ta tafi babu Habibu babu dan sa Abdallah a falon.
Ta ina za ta bari Abdallah ya sake kubuce mata A KARO NA BIYU? Ai ko yakin duniya na biyu (World War II) za su yi ita da Habibu wannan karon sai ya ba ta dan ta.
Da gudu-gudu ta bi bayan su tana kiran sunan "ABDALLAH". Yayin da jamaar falon duka suka bi su da kallo. Ba ta cimmasu ba sai a harabar gidan yana kokarin saka katuwar jakar kayan Abdallah a bayan jibgegiyar motar da ke ajiye a ma'adanar motoci.
Sai ta rasa kwarin gwiwar karasawa gare su, sabida kallon dibar karen mahaukaciyar da Habibu ya yi mata, ta tsaya daga bakin kofar shiga falon Daddy Usman tana kallon su kawai suna shiga mota, kaunar Dan ta na kara bunkasa a zuciyar ta kwatankwacin ta ranar da ya zo duniya, hanyoyin da zata bi ta karbi Abdallah ta take tunani, koda hakan shine struggle na karshe da zata gudanar a rayuwar ta. Daga nan har supremecourt! Wato kotun daga ke sai Allah ya isa!!!

Ganin sa da ta yi yau matsayin kanin Aunty Badiya matar Baban ta, ta san Allah ke nufin farawar sababbin alamura da dama a gare su, wadanda a iya kintacen ta da tsinkayen ta bata hango farkon su balle karshen su ba. Na baya duk shimfida ne, wato wanda ya faru a Jamus, yanzu ne zasu fara ta babu dadi ita da dan mutanen Nahuche. Domin ko sama da kasa zata hade sai ya bata dan ta. Abu daya ta sani shine (maintaining self-esteem) din ta yanzu ta fara, ko da soyayyar ita ce ajalin ta, amma tana da right din ta na rikon Abdallah wanda addini da shariah suka bata har sai ya balaga ya zaba tsakanin ita da shi.
Idan a da bata da gata shi yasa yake walagigi da ita da dan ta yadda yake so to a yanzu tana da gata kamar koma fiye da kowa. Sannan ta tsaya da kafafun ta ta wuce wargin kowanne da namiji. Don haka ita da Habibu a je zuwa..wai mahaukaci ya hau kura

SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI KE CEWA, MU KARASA LABARIN "NAHUCHE. (DAGA FUSHI NA) A LITTAFI NA 3 NAN BA DA JIMAWA BA INSHA ALLAHU.
20/2/2022
Chapter 16 · 0% Book details