Sashe 13
Nahuce Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Habibu ya zauna gefen Yayar sa, tamkar wanda ya dauki azumin rashin magana. Aunty Badiya ta ce, "Tsakani da Allah Habibu me ye reality na rashin auren ka? Habibu ko dai ka zama ba namiji ba ne bayan haihuwar Junior da ka yi?"
Duk halin da yake ciki sai da Dr. Badiya ta ba shi dariya. Ta gefen ido ya kalle ta ya yi murmushi, ya ce, "Auren ne kawai bana ra'ayi, tunda kuma ina azumin litinin da alhamis ina iya rike kaina. Stop all these silly thoughts. Yau ki ce wannan, gobe ki ce wannan.
Badiya ta yarfar da kai gefe, ta ce, "Tsakani na da Maman Abdallah Allah ya isa! Ita ta ki zama da kai, sannan ta hana ka auren kowa. Wa ma ya sani ko asirin su irin na fulani ta yi maka?"
Mikewa ya yi yana dan murmushi kafin ya ce da Yayar sa Badiya.
"Ai ita ba ta so na ma ko kadan, balle ta yi min asiri. Masu yin asirin ina ce sai suna son zama da mutum suke yin sa? Ba ta taba so na ba, kuma har abada ba za ta so ni ba".
Yana fadin hakan ya doshi kofa ba tare da ya juyo ba, kada Aunty Badiya ta ga kwayar idanun sa, ta hango weakness din da ya bakunce su.
"Gobe ba zan biyo ta nan ba, daga Hotel zan wuce Lagos".
Badiya ta yi masa Allah ya kiyaye hanya, ya wuce ba tare da ya kara waiwayowa ba, ya bar ta da hannu bisa haba.
A harabar gidan ya ga Baban Musaddiq zaune bisa fararen kujeru yana waya, ga yadda ya bada nutsuwar sa kacokam ga wayar za ka fahimci waya ce mai muhimmanci yake yi. Habibu na dosowa ya kashe ta, ba tare da ya gama ko ya yi sallama ba.
"Baban Musaddiq zan wuce masauki, gobe zan wuce Lagos, ba zan shiga Abuja ba sai upper week".
Baban Musaddiq sai kallon sa yake kamar yau ya soma ganin sa yana kissima abubuwa masu yawa a cikin ran sa.
Ashe surukin sa ne... Ashe shi da Badiya har jini sun hada... Ashe shi ya sa yake matukar son ABDALLAH... Abubuwa da yawa yake kissimawa wadanda sai a yanzu suka samu damar dawowa suna warware kan su, yana kara mamakin ta yadda har ya kai tsayin wannan lokacin bai gane din ba.
Hannu kawai ya iya mika wa Habibun, ba tare da ya ce komai ba suka yi musabaha ya wuce zuwa motar sa. Ya shiga ya tayar da kan sa don ya sallami Solomon tun dazu, Baban Musaddiq bai bar wajen ba sai da Habibu ya fita daga get gabadaya.
Wayar da Uncle Usman ya fito waje yana yi, ba da kowa yake yi ba da Ambasada Shehu ne. Har kuka ya yi a cikin wayar, a lokacin da yake gaya masa ashe Habibu shi ne mijin Raheenah ba su taba ganewa ba?
Murmushi Ambasada ya yi, murmushi mai sauti kafin ya ce.
"Finally kai ma ka gano da kan ka kenan, kamar yadda na dade da ganewa. Da ma na ce ba zan gaya maka ba ne sai ranar da ka gano don kan ka...".
Nan aka dauko tsohon tarihi, Ambasada ya warware wa Uncle Usman rikicin auren su a Jamus kaf! Ya kare zancen sa da cewa.
"Har gobe daga ni har Nene Bilki da kawar ta Yafendo, babu wanda ya san hakikanin laifin da Habibu ya yi mata. Bata taba fada ba. Which means tana sirran ta sirrin sa. Amma kuma tana fushi da shi, ban yarda rashin so ne ba, kada ka takura sai ka ji, don tsakanin mace da miji sai Allah.
Yanzu neman hanyar sulhunta su za mu yi, in ba haka ba ina mai tabbatar maka Habibu da Rahinah za su yi furfura a kan su ba tare da sun yi aure ba".
Uncle Usman da Ambasada suka ci gaba da kulla mai yiwuwa a tsakaninsu su biyu ba da sanin Aunty Badiya ba, haka ba da sanin Habib da Rahinah ba, sun aje kwanaki uku masu zuwa za su hadu su je Girei su samu Sarkin Fulani a san ta yadda za a shawo kan al'amarin. Bayan nan, sun yanke tabbas za su hada Habibu da Rahinah a gidan Uncle Usman ba tare da sanin kowannen su ba, don su ga irin reaction din kowannen su.
Don a cewar Ambasada Rahinah ta HUCE daga fushin ta tuntuni, ki-fadin ta ne ba zai bari ta nemi Habibu ba. Shi kuma Uncle ya musanta da cewa har yanzu ba ta huce ba, don ko jiya da ya matsa mata da zancen aure, kuka ta yi masa. Ta kuma gudu. Ba za su gane hakikanin abin da ke zukatan su ba har sai sun hada su sun ga juna unexpectedly.
Abin da dattijan biyu ba su sani ba shi ne, daga Habibu har Rahinah babu wanda bai san garin da dan uwan sa ke rayuwa ba... Babu wanda bai san duk wani taku na dan uwan sa ba. Babu wanda bai san ci gaba da nasarorin dan uwan sa ba. Abin da ba su sani ba shi ne, alakar da ke tsakanin su, wadda Badiya da Uncle Usman suka hada, wato kasancewar Habibu kanin matar Uncle din ta, da kasancewar Rahinah diya ta halali ga ubandakin sa, kuma sirikinsa Baban Musaddiq Alh. Usman Girei.
******
Sarkin Fulani ya gama jin duk abin da ke akwai, ya yi kabbara takbir da tahlili cikin jinjina kudurar Ubangiji. A karshe ga bayanin da ya yi musu, a matsayin sa na babba, wanda dukkan su ya fi su shekaru da tsinkaye.
"Bana bayan shawarar ku, ta a maida musu aure ba da sani da amincewar su ba. Kada ku manta Rahinatu na a matsayin bazawara ne a halin yanzu, addini ya ba ta damar zaben mijin aure. Alhamdulillahi tunda saki daya ne a tsakanin su, abin da za ku yi yanzu shi ne, ku yi kokari su hadu da juna, ta ga dan ta ta san shi ne. Ya gan ta, ta ganshi su san alakar zumuncin da ke tsakanin su.
Daga nan ku bar komai a hannun su, ni na gaya muku za su sulhunta kan su. A wannan lokacin addu'a ce tsakanin ku da su ba tirsasawa ba".
Daga Uncle har Ambasada sun yi na'am da shawarar Sarkin Fulanin Girei.
******
Ta fito daga bedroom dinta a shirye tsaf, likita mai aji, rike da 'yan mukullayen motar ta ta tadda Sahura a falo tana kallo, ta ce, "Sahura, yau in na fita sai Allah, don haka kada ki yi girki da ni, ki yi daidai cikin ki, za mu yi dashen dodon kunne har biyu (cochlear implant transplantation) a Nizamiye, don haka sai kin gan ni kawai".
Sahura ta ce, "Allah ya yi jagora, Allah ya bada sa'a uwar daki na, Allah ya bada ladan ceton kunnuwan al'umma".
Dariya ta yi ta wuce ta fita tana karanto addu'ar fita daga gida.