Sashe 4
Nahuce Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ita kan ta Dr. Badiya ba karamin gata ta ke samu a wurin Habibu ba, duk da kasancewarta mai albashi mai tsoka nata na kanta itama, to balle kuma mahaifiyarsa da Dansa. Wadanda duk abin da ya samo nasu ne, a cewar sa su yake nemawa. Duk fadi-tashin sa a rayuwa sabida su ne. Sau uku a jere Haj. Kaltume da Badiya na tafiya aikin Hajji duk shekara.
Tuni ya buge gidan su an zuba gini na zamani na gani na fada, kai ka ce gidan wani minista ne ba gidan tsohuwa Kaltume matar marigayi Bilyamin Nahuce ba, duk fadin unguwar Kofar Jange babu gida mai fasali da zubin zamani da ya kai kwatankwacin GIDAN NAHUCE.
Ga maaikata rututu Habibu ya zuba mata. Kullum zaka sameta zaune a tankareren falon ta akan kilishi mai taushi tana lazumi tana ibadah, don a cewar ta su kadai suka rage mata yanzu, sai ko ganin auren Habibullahi. Hajiyar Nahuche ta zama wanke goma ka tsoma biyar. Jawur da ita, tsafta da naira sun kama jikin ta. Ga hasken rikon addini. Gidan ta kullum cike da yan cin arziki daga jamaar unguwa dana garin su Nahuche.
Daga baya Hajiya Kaltume ta soma karbar tayin hotunan 'yammata da ake kawo mata daga Nahuche da Bungudu, sannan yayan masu da shi anan Zamfara da iyayensu ke son hada auren 'ya'yansu da Lucky Habibu Nahuce duk haka ake kawowa Hajiyar Nahuche. Eh, wasu kan kira shi 'Lucky' sabida kafin ka samu mutum mai sa'a a kan duk abin da ya sa gaba kamar Habibu Mustapha za a dade.
Komai ya sanyawa hannu na harkokin sa sai ya zama kamar magic sai ka ga ya bunkasa ya shahara ya yi albarka cikin dan lokaci. Wannan kuma albarkar bakin UWA ne da addu'o'inta da ba sa yankewa a gare shi. Kullum Haj. Kaltume a kan dugaduganta take kwana sallah, kuma duk yawancin addu'o'in ta akan Habibu ne.
Nasarar rayuwa, kariya daga sharrin Shaidan, albarka a dukiyar sa, da mata tagari (wadda zata kaunace shi saboda Allah ba don dukiyar sa ba) su ne abubuwan da kullum take roka masa.
Hotunan 'yammata iri-iri 'ya'yan manya a garin Zamfara da garin Bungudu da Nahuce an sha kawo wa Hajiya Kaltume, amma a duk lokacin da ta dumfari Habibu da su ko dubawa ba ya yi zai ce,
"Ki yi hakuri Hajiyata, ni na riga na gama aure a duniya". In ta takura masa kan sai ya duba kuma sai ya fara mata yan kanan kwallah, da dole zata mayar dasu inda ta dauko cikin mutuwar jiki. In ya so tsokanar ta kuma sai yace.
Hajiya kada ki damu akwai (hurul eeni a aljannah, inshaAllahu).
Bata taba daukar maganar sa a bakin komai ba, face lokaci ne bai yi ba, in lokacin yayi shi da kan sa zai kawo mata matar da yake so, bacin ran uwar Abdallah (Rahinah) ta yi amanna da cewa shi ke walagigi da shi har zuwa lokacin. Ya ke ganin don ita ta ki shi, ba zai samu mai kaunar sa ba. Ko kuwa an ce ita ce autar mata da za'a debewa sauran mata tsammani a kan ta??? A bisa wannan dalilin Hajiyar Nahuche ta ji ta fara tsanar wannan Rahinah duk da bata taba ganin ta ba ko a hoto.
******
MUTANEN JAMUS (BAYAN BARIN HABIBU FRANKFURT).
Tun daga lokacin da Habibu ya dauke mata Abdallah, rayuwa bata kara komawa yadda ta ke a baya ba ga Raheenah Omar. Sauran kadan ta zama depressed wato ciwon damuwa ya kama ta. Ita kadai sai ka same ta a dakinta tana magana cikin safah da marwah, karatu ta daina fahimtarsa kwata-kwata, zuwa makarantar tana yi ne kawai bisa tursasawar Nene da Ambasada Shehu, amma ta kasa concentrating a kan komai. Komai ya fice mata a ka. Hatta kasar Jamus bakidayan ta.
A jarrabawar karshen zangon da suka yi Ambasada Bichi bai ji dadin sakamakon Raheenah ba ko miskla zarrah; ta fadi courses har biyar. Don haka ya kira ta falonsa don su yi magana ta Uba da Da.
"Rahinatuh. Ina son sanin hakikanin abinda ke damun ki? Akalla in ban miki maganin sa ba a matsayina na Uba zan baki shawara wadda nake ganin ta dace. Wannan wane irin mummunan sakamako ne nake gani haka?"
Raheenah ta share zufar da ta jika goshinta, cikin rauni da karaya ta ke wa Baban ta Ambasada magana. Ba tare da ta san maanar abinda take furtawa ba.
"Ni kai na Daddy (ban san hakikanin abin da ke damuna ba), rayuwar ce kawai na gaji da ita. Na fi so in mutu in huta. Ji nake kamar ni kadai na yi saura a duniya, kamar rayuwata ta zo karshe.........
Kamar babu wani sauran farin ciki da zan cimma a karshen ta, kamar duniya ta ta kare. Ji nake kamar wani tsuntsu ko kuma shaho ya zo daga sama ya tattare dukkan farin ciki na da burika na ya tashi sama firrr! Da su".
Wani irin murmushi Ambasada Shehu ya yi, irin nasu na manya da suka karanci halayyr dan adam, kafin ya ce,
"Kuma wannan TSUNTSU ko SHAHO ba kowa ba ne, HABIBU ne!!!.
He ran away with all your hopes and happiness... (ba tare da sanin ki ba ya tafi da dukkan fata da farin cikin ki).
Habibun da ki ke gujemawa da gangan, amma ruhin ki da zuciyar ki na tare da shi da Dan da ki ka haifa masa..
It's either two options; ko dai ki yi hankuri ki ba wa zuciyar ki abin da ta ke so don samun farin ciki da kwanciyar hankali, ko kuma ki ci gaba da horar da kan ki da kan ki a bisa kuskuren ki.
Allah Ubangiji mai afuwa ne, Annabi (S.A.W) mai afuwa ne. Allah Ubangiji kuma yana son masu afuwa.
Amma Rahinatu ke kin ce ba za ki yi afuwa ga Habibu ba a kan kankanin laifin da ya yi miki. Wanda ku kadai kuka san abin ku. Don haka sai ki koya wa zuciyarki juriyar rashin su, in har kina nan a kan bakanki, ki fuskanci rayuwar da ke fuskantar ki.
Kina da babban aiki a gaban ki wanda ba ya son damuwa da rudani (karatun ta). A matsayi na na Baban ki, shawarar da zan ba ki ita ce ki koma addu'a, idan rabuwar ki da Uban dan ki ita ce mafi alkhairi, Allah ya ba ki zuciyar dangana.
Idan dawowar su cikin rayuwar ki shi ne alkhairi Allah ya sanyaya miki zuciya su dawo cikin rayuwar ki ba da jimawa ba".
Raheenah ko kadan ba ta son yarda da abin da Ambasada ke fadi, wai- wai wai Habeebu ne tsuntsun da ya tashi da farin cikin ta. Za ta fi yarda in ya ce rashin dan ta Abdallah! Don haka ba ta ce komai ba, amma tana can tana kokawa da zuciyar ta a kan shin abin da Daddy Amb. ke fadi shi ne hakikanin damuwar ta ko kuwa?
Wato rashin Habibu Nahuce???
Idan kuwa shi ne zuciya ba ta yi mata adalci ba, domin Habeeb bai bar wani (green momeries) ba cikin rayuwar ta da ya cancanci ta bishi da kewa, sai (black memories and black episodes...) wadanda da su ne kullum take kallon sa, suka kuma sa ta kasa bashi gurbin masoyi, wane irin rashin adalci na zuciya ne zai sa rashin sa ya dagula lissafin ta har haka, ya hana ta ci gaba da harkokin rayuwar ta?
Daga wannan ranar Raheenah ta yi aniyar fighting da zuciyar ta, mai neman kai ta ta baro, har sai ta manta da Habibu da Dan sa, dan da bata taba zaton ma za ta so ba har sai bayan da ta haife shi. Wannan wani kudiri ne da ta ke fatan Allah ya ba ta nasara da iko a kan sa, wato gusar da duk wani burbushi da Habibu ya bari cikin rayuwar ta.
Daga wannan ranar, Rahinah Omar ta maida hankali a karatunta, don in ba karatun ba wa za ta kama? Ranar da babu su Ambasada? Habibu ko sunan garinsu ba ta sani ba, balle inda ya fito, bare ta sa ran watarana za ta je ta kwato danta.
Abin da ta sani a kansa kawai shi ne dan kasarta Nigeria ne.
Bayan wannan bata san komai akan sa ba. Sannan Nigeria kasa ce ba gari ba.
Da sabon zango ya zagayo. Ta sake maimaita takardun da ta fadi, kuma cikin ikon Allah ta haye wannan karon. Da taimakon nasihohin Yafendo, Ambasada da lallashin Nene Balki.
*******
Ana gab da hutun summer Ambasada ya karbi passport din ta ya hada da nasu don yi musu shirin zuwa Nigeria hutu, kamar yadda suke yi duk karshen shekara.
Ta shiga dakin Yafendo a wani dare, sai ta tadda ita tana daure kaya. Tsibi-tsibi tana daurewa tana ajiyewa kamar in ta tafi ba za ta dawo ba. Raheenah ta ce,
"Yafendo? Wannan kaya ina za ki kai su haka? Ai sai ki karar mana da kilo"
Yafendo ta ce, "Duk tsaraba ce da na ke tarawa tsayin shekara guda ta mutanen Bichi. Sannan ke ma na yi sayayya ta musamman don ki kai wa 'yan uwanki in Allah ya sada mu da su".
Wani dadi ya ratsa Raheenah, sai ta ji tamkar Dadanta ce a tare da ita. Allah ya sa wadanda Yafendo ke hasashe su kasance su ne dangin nata. Da duk wasu matsaloli da damuwoyi sun karasa zama tarihi a gare ta. Habibu ya je ya dafa dansa ya cinye.
A washegari ita ma ta hada nata kayan, amma ba ta dauki sun fi kala bakwai ba. Don Daddy ya ce ita sati daya za ta yi ta dawo ita da Safeenah don ba ya so gidan ya zauna babu kowa. Safeenah kuma ba ta son zaman Bichi ko kadan, a cewarta zafi ke damunta.