← Book details Nahuce Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 16

Sashe 10

Nahuce Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Raheenah na dakin tiyata, fitowar ta kenan ta samu kira daga bakuwar lamba. Sai da ta zauna bisa kujerar ofishin ta ta warware nadin mayafin da ke kanta, sannan ta bi bayan kiran.
Muryar wa za ta ji? NENE! Sannan lambar ta kasar Nigeria ce.
Wata zabura da Raheenah ta yi daga kujerar ta tana kiran sunan "Nene!" Sai da ta bai wa Nene Balki dariya, ta ce,
"Finally, ga mu a Abuja, kuka ya kare ko?"
Hawayen farin ciki suka zubowa Raheenah, da ma kewarsu da kadaici sun addabe ta musamman da ta fara samun saukin ayyukan da ke gaban ta. Sannan ba ta da kowa a Abuja bayan Uncle Usman, shi kuma ba haduwa suke ba sai idan ta samu lokaci ta je ofis din sa ko shi ya zo nata.
Don haka dawowar iyalin Ambasada Shehu Abuja ba karamin kwanciyar hankali ya kara wa Dr. Raheehah ba. A ranar a gidan Nene suka kwana dakin Yafendo ita da Sahura ana ta hirar yaushe gamo.
Daga wannan lokacin ne kuma rayuwar Raheenatu ta dauki sabon direction. Rayuwa ce ta 'yanci ta ke ciki wadda kowanne mai ilmin boko ita yake yi wa buri, ga aiki, ga gida ga albashi ga motar kan ta, ga kuma rayuwar Abuja. Don haka abu daya ya rage mata shi ne mahadin rayuwar diya mace, wato mijin aure. Mazan da har gobe ta kasa daga ido ta yi musu kallon maza, sai muna-maza, domin kowa ya zo gare ta da kalmar so ji ta ke tamkar ya daba mata mashi a kahon zuci, bai kai ba, bai isa ba. Wanda ta ke binnewa da gangan a karkashin ran ta, shi kadai ne namiji a idanunta a zahiri da badini, dan Hajiyar Nahuce (Habibu).
Ta zama infatuated a kan Habibu kwarai, ta ci gaba da follow up a kan duk wani takunsa na rayuwa, da halin da yake ciki. Duk wasu nasarorin sa na rayuwa a kan kunnen ta, Amma ta yanke shawarar never to look for him ever! A wurin ta kaddara ta riga ta gama playing game din ta, tsakanin ta da Habibu Nahuche. Amma ta rasa dalilin da ya sa har gobe ta kasa daina bibiyar halin da yake ciki.
Shin da gaske ne kaddarar ta gama playing game din ta a tsakanin su???
Ta tambayi kan ta a ranar da ta ji (live programme) din sa da British Broadcasting Corporation wato gidan rediyon BBC Hausa. Ta kashe rediyon ta koma jikin taga ta tsaya standstill tana kallon harabar gidan ta wanda shuke-shuken korran ciyayi suka yi wa kawanya. Abdallah ko yanzu in ya gan ta zai iya shaida ta? Ko ya taba gaya masa yana da uwa a duniya? Ko kuwa bacin ran ta ya sa bai taba gaya masa ba? Habibu kadai ya san duka amsoshin wadannan tambayoyin.
******

Yau juma'a ba ta da aiki sosai a ofis don haka ta yanke shawarar tattara komai nata ta wuce Maitama wajen su Nene ta kare ranar yau tare da su. Ta kira Sahura a waya ta ce, kada ta dafa abinci da ita ta wuce wajen su Yafendo sai dare za ta dawo.
Rahina na tuki cikin nutsuwa kamar yadda ta saba, lokacin da direban sa Yohan dan kabilar Igala ya shararo motar su a guje kirar 'Discussion Contineous' saura kadan ya goga mata. Da sauri ta dauke kan motar ta tana mai Allah wadai da halin wasu direbobin, shi ko Yohan Ubangidan sa ke azalzalarsa a kan ya yi sauri, saura mintuna goma sha biyar meeting din zai halarta a Transcorp Hilton.
Amma me? Motar da ta kauce musu is a glimpse of her Fulani face. That magical beauty of her's, wanda cikin kowanne hali ba zai kasa shaidawa ba. Cikin hali na mafarki ko ido biyu ba zai taba mancewa da kamannin Raheenah Omar ba. Waiwaye wani abu ne da ba ya yi sam, amma yau ya yi waiwaye har ba adadi kamar wuyan sa ya karye amma motar ta bace masa. Abu daya ya gane, motar fara ce sol! Kirar kia picanto, kuma yana da tabbaci a kan-kan sa (self-assurance) na ko da ba ta bace masa ba, ba zai bi bayan ta ba. To ya bi ta yace mata me? Ko ya yi mata me?
Ta bar shi da tabo a zuciya, it's a deep wound that can never be healed, watakila har sai ranar da Raheenah Omar ta nemi KOME zuwa auren su da kan ta da bakin ta.
Wanda kuma yake da tabbacin abu ne mai matukar wuya a kafiya da taurin kai irin nata da ya dade da fahimta.
Wannan na nufin ta dawo Nigeria...
Wannan na nufin she's progressing without him, shi da dan sa ta ba su baya, ta manta da su kwata-kwata.
A duk lokacin da ya tuna Raheenah, fada yake da zuciyar sa ta ci gaba da yin tauri, kada ta karaya, kada weakness din ta ya bayyana. Amma yau fa? Raheenah ya gani ba hotonta ba, her humble self bayan wucewar shekaru goma, which is hard for him to control himself domin kuwa ko meeting din da yake gaggawar zuwa har aka yi aka gama bai tsinci komai a ciki ba.

Ta iso gidan Nene wajejen karfe sha daya na rana. Da Ahlan ta soma cin karo suna wasan kwallon kwando da abokan sa a harabar gidan. Ya baro abokan nasa ya zo ya bude mata kofa yana fadin, "Yayata tafi ta kowa, Yayata likitar da babu kamar ta'.
Dariya ta yi suka rankaya zuwa ciki.
Nene na kicin tana girki lokacin da suka shigo. Ta kama mata suka karasa komai, suna aikin Nene ta ke gaya mata Yafendo ba ta jin dadi tun jiya.
"An je asibiti?" Ta tambaya cikin damuwa.
Ba yadda Daddy bai yi ba dazu su tafi asibiti ta ki, wai in mutuwa ce a bar ta ta mutu a cikin dakin ta. Ba ta son zakule-zakule, Raheenah sai ta bar komai ta nufi dakin Yafendo.
A kwance ta same ta tana lazimi ta tsaya daga bakin kofa ta ce, "Yafendo me ya same ki?"
Yafendo ta sauke idanun ta da suka kada sabida zafin zazzabi, ta ce,
"Ya ki 'yar albarka, da ma yanzu zan ce wa Ahlan ya danno min ke a waya, ki zo ki ba ni magani, bana son zuwa asibiti a yi ta jagwalgwala ni".
Ai kuwa sosai Rahinah ta bincike ta, ta kuma ba ta treatment din da ya kamata, domin ta fahimci zazzabin typhoid ke son kamata, har allura ta yi mata wadda ta aika Ahlan ya sayo.
Zuwa la'asar Yafendo ta ji dadin jikin ta sosai, sai suka koma hira, Yafendo ta ce,
"A yi magana cibi ya zama kari, amma bari Baban naki ya shigo".
Raheenah ba ta gane me Yafendo ke nufi ba sai da Daddy ya dawo, ya kuma shigo don ya duba jikin Yafendon, nan ya ga Raheenah ya fadada fara'ar fuskar sa, yana fadin, "Lale-maraba, da manyan otorlaryngologists".
Yafendo ta ce, "Ai gara da ka zo, da ma yanzu zan ce ta latso min kai. Shigo ka zauna, magana za mu yi ta gaskiya ni da ku".
Ambasada ya samu wuri gefen Yafendo ya zauna, ita kuma sai ta fara magana cikin tsananin damuwa.
"Yanzu saboda Allah haka za ku zuba wa Rahinatu ido ta kare rayuwar ta babu aure? Talatin ta ke nema fa rabin sittin ba ashirin ba. Ni ban ce lallai sai ta koma wa Baban Abdullahi ba, tunda wannan shi ta ga zai fishshe ta, amma ta fidda miji ta yi aure ko wane ne tunda ta ki komen mai kaunar ta da gaskiya.
Amma wallahi ku yi a hankali daga ku har ita, kada bokon ku ya kai ku wutar jahannama".
Shi kam Ambasada murmushi kawai yake yi domin a yau din nan ya gano wani muhimmin al'amari, wato Yayar Habibu Nahuche Uncle din Rahinah Alhaji Usman Girei ke aure. Ya gane hakan ne daga hirar da suka yi da Uncle Usman yau a ofishin sa, inda yake gaya masa ai NAHUCHE HOTELS na kanin maidakin sa ne Badiya, lokacin da aka nuno sabon ginin NAHUCHE HOTEL da ya yi launching a jihar Rivers (PortHercourt) a talbijin din da ke cikin ofishin a gaban su lokacin da suke hirar. Shi kuma Ambasada bai gaya wa Uncle komai a kan sanin da ya yi masa yana dalibi ba, ko girman alakar da ke akwai a tsakanin su yanzu. Shi Uncle Usman din da Habibun (wato surakuta). Ya bar wa Allah ikon Sa ya ci gaba da yin hukuncin Sa a kan Rahinah da Habibu Nahuche, don ya gane ba karshen kaddarar su kenan ba, tunda har wannan babbar alaka ta sake bayyana kan ta a tsakanin su.
Chapter 10 · 0% Book details