← Book details Nahuce Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 16

Sashe 1

Nahuce Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

(Daga Fushina)

2

Littafin

Sumayyah Abdulkadir
[email protected]

SADAUKARWA NE GA DUK MAKARANTA LITTAFAI NA A DUK INDA KUKE.

NA HUCHE 2!

Habibu Mustapha Nahuche ya sauka a filin jirgin saman Abuja daga Frankfurt ta kasar Jamus da misalin karfe shidda na safiyar Jumaah, yana rungume da dan sa Abdallah a kafadun sa na dama, wanda ke ta barci sadidan cikin gajiya tun suna cikin jirgi.
Kai in ka ga irin rikon tsantsenin da yayi ma dan na sa, gami da tsantsar kulawar da ya ke baiwa kankanin yaron, tsammani za ka yi cikin sa zai maida shi don tsananin So da kauna irin ta mahaifi. Mahaifin ma irin Habibu Nahuche wanda samun Uban da ke son dan sa kamar sa sai an tona. Har ila yau, tsatstsauran rikon da ya yi wa yaron, yana da nasaba da kasantuwar sa cikin fargaba da tsoron ko Raheenah za ta biyo bayan su afujajan kafin su kai ga sauka a kasar su ta haihuwa, Najeriya.
Duk da ya san hakan ba mai yiyuwa bane ba tare da shiri ba. Amma hanakalin sa bai kwanta ba har sai da ya gan shi a filin jirgin saman birnin tarayyah. Saboda yana da tabbacin abu daya: A yadda Raheenah ke son Dan ta, da yadda ta damu da kasancewa tare da shi ko barci bai taba raba su ba, da kuma yadda ya san ta wajen kafiya da naci akan abun data ke so, da bakin cikin shammatar da ya yi mata, ya tabbata za ta iya takowa ko da da rarrafe ne ko da akan gajimare ne tun daga Frankfurt, ta biyo bayan su ta cikin hazo don ta kwace dan ta Abdallah, shi ya sa bai je dauko Abdallah daga gidan Ambasada bama sai da ya kayyade ya kuma kintaci lokacin tashin jirgin su.

A yayin da jirgin ya karci kasa ya bar babban birnin Frankfurt din Jamus, sai ya ji tamkar ya nannade komai na Raheenah Omar daga zuciyar sa, tamkar yadda ake nade tabarma, ya baro shi a can. Ya cire ta kenan HAR ABADA daga rayuwar sa, ya hakura da ita, ko da ita ce autar mata a duniya, kamar yadda babu shi babu kara yin aure a duniya.

Raheenah Omar, ta kassara shi, ta raunata shi, ta ji masa ciwo mai muni a zuciya, bashi da sauran wata soyayya da zai iya baiwa wata diya mace, ta kashe duk wani burin sa a kan yaya mata (ko dama can bai da buri akan su, ita kadai Allah ya sallada zuciyar sa kan ta, ya jarrabce shi akan ta da mafi girman jarrabawa). Juya masa baya da ta yi da sulhun da ya nufa na alkhairi a gare su ya dauke duk wani farin ciki da walwalar sa, ta zagwanyar da farin cikin achievements din da ya dawo da su daga kasar Germany. Wato kwalayen sa guda biyu, masu daraja ta farko.

A kan ta ya san so, a kan ta ya fara so, haka a kan ta ya kare so, kamar yadda daga kan ta ya rufe SO. Ta tafi da dukkan (charming and amiable) Habibu Nahuche bata bar shi da ko guda ba cikin dabiun sa da halayen sa na baya.
Amma a matsayin sa na musulmi kuma haihuwar musulunci, ya san komai muqaddari ne daga Allah watakila Allah ya rubuta iya rayuwar auren da zai yi da Rahinah kenan ta kwanaki bakwai, watakila a rubutun kaddarar su; babu sauran zama a tsakanin su. Hakan ba zai sa ya kasa rayuwa a kasar haihuwar shi ba. Hakan ba zai hana shi godiyar Allah da ya bashi tsatso daga gare ta ba. Zai yi gammo ya dauki rayuwa a duk yadda ta zo masa, ba tare da Rahinah Omar a cikin ta ba.

Abin da zai sa a gaba yanzu shi ne: hanyoyin da zai bi ya maida kobo ya koma dari don tserewa bakin ciki da takaicin duniya, don samawa Abdallah kyakkyawan future, da kuma hanyar da zai bi wajen rainon gudan ran sa (ABDALLAH), zai yi duk yadda zai yi wajen ganin ya bashi rayuwar da ta dace da kowanne Da mai gatan UBA har ma da UWA (tunda Hajiya da Badiya na raye) da kuma ilmi mai inganci.
Ko a lahira ba ya fatan Allah ya sake hada shi ko a hanya da uwar Abdallah.. Infact, abinda ya lura a tare da Raheenah Omar; babu zuciyar imani ko kankani a cikin tsakiyar kirjin ta, babu compassion, babu love, babu affection, ita da sassakakken dutse basu da maraba. Taurin kai ko irin na mutanen farko, she has no love in her talk more of offering it to someone. To Idan so cuta ne. Hausawa suka ce hakuri ma magani ne!.
Zai hadiyi hakurin nan komin dacin sa, komin baurin sa, komin girman sa, zai kuma hada da addu'a da rokon Allah dare da rana kan ya fidda Rahinah da komai nata daga zuciyar sa da rayuwar sa bakidaya.

Daga Abuja shatar karamar mota ya dauka kai tsaye har garin su Zamfara, tun a wancan lokacin jihar Zamfara babu filin jirgi. Ya tsaya ya yi canjin kudin sa a Abuja daga Euros zuwa Naira, ya saya wa Abdallah abincin da zai rika ci a cikin mota har su isa Zamfara.
A lokacin Abdallah ya tashi daga barci sai faman kalle kalle yake na ganin sa a bakon wuri da bakin fuskoki, amma ko tari bai yi da sunan kuka ba, tunda dama ya saba da Baban sa sosai.
******

UNGUWAR KOFAR JANGE ZAMFARA STATE (GIDAN MARIGAYI ALH. MUSTAPHA BILYAMIN NAHUCHE)

Y
au unguwar kofar Jange cike take makil da matasa, ana ta hada-hadar siyasa, unguwar ta cakude da hargowar samari da 'yan jagaliyar siyasa masu yawo da fastocin 'yan takara suna musu kamfen. Don haka da kyar direban da ya dauko su ya samu hanya suka kutsa suka isa har kofar gidan da ake kira 'GIDAN NAHUCE'.

Duk inda suka gifta cikin unguwar tasu sai Habibu ya bi wurin da kallo (with nostalgia) da tsananin begen gida, yana mai tuno wani abu na dabdalar kuruciya da ya yi a wurin, shekaru bakwai kenan da barin sa gida idan har lissafin da yake yi daidai ne.
Yau ga shi ya dawo gida lafiya, amma ba shi kadai ba kamar yadda ya tafi, ya dawo ne tare da wani replica din sa (photocopy of Habib Nahuce). Wanda kaddara ta tanadar masa, ta kuma ba shi ba tare da ya tsara ba.
Yana godiya da wannan kaddara tasa da hannu bibbiyu, domin kyautar Da sukutum! Rahma ce daga Ubangijin Talikai. Wadda ba kowa Allah yak e baiwa ba.

Hajiyar Nahuce (kamar yadda kowa a dangi dama jamaar unguwar ke kiran ta) tana alwala da buta a gindin famfo lokacin da Habib ya yi sallama. Muryar sa ta dira a cikin kunnuwan ta kamar cikin mafarki.
Sai ta dakata daga wanke kafafun ta da ta ke yi, ta yi tsam! Da ran ta, tana son gasgata abin da ta ji. Kafin ta dago manyan idanun ta wadanda da gani ka san babu tambaya ita ce ta haifi Habibu Mustapha Nahuce. Alamun girma da ya soma kamata bai boye zahirin kamannin su ba na Rumawan Nahuche.
Bude baki ta yi cikin mamaki, da tuajjibi, don ko shekaranjiya sun yi waya dashi Habibun, amma bai ce mata yana tafe ba.
"Wa nake gani kamar Habibuna? Habibullahi?"
Duk yadda Da ya kai ga canjawa, cikin halin jin dadi ne ko akasinsa, to fa Uwa ba ta kasa gane abinta. Don haka komawar Habibu kyakkyawan Bajamushe kuma gogaggen bakin bature bai hana Uwarsa Hajiya Kaltume gane shi ba, daga kallo na farko da ta yi masa.
Har gabanta ya karaso ya sunkuya, cikin gajiya, sannan ba tare da ya ce komai ba ya mika mata Abdallah da ke hannunsa makale a kafadun sa. Amma sai Abdallah ya ki zuwa, ya makale sosai a jikin Baban nasa.
Jikin Hajiyar Nahuche ya hau rawa da makyarkyata.

"Ni Kaltume Nahuce! Habibullahi ina ka samo yaro mai kama da kai haka???"
Ba jikin ta kadai ba, hatta muryar ta Hajiya karkarwa take yi.
Magana ya shiga yi wa Abdullah da harshen German"Abdallah Sie istmeine Mutter, geh zuihr (she's my mother go to her)". Yaron ya make kafada cikin rashin yarda, tare da sake makalewa cike da tsoro da kyuya a jikin Abban sa.
Yara suka soma shigo da jakunkunan Habibu manya-manyan trollies. Haj. Kaltume gabadaya mamaki da tsoro ya hana ta kokarin karbar yaron da yake ta faman son ta karba.
Sai ta fara hawaye daga tsaye. Sakamakon abinda zuciyar ta ta hasaso ta kissimo mata.
"Sai ka fara gaya min ina ka samo shi tukunna zan karbe shi, Habibu Allah ya sa ba shegensa ka yi ba a can kasar masu jan kunne". Idanunta na zub da hawaye suna nuna tsananin kidima da fargabar da ta ke ciki.
Da sauri Habib ya hau girgiza mata kai. Shima nasa idnun suka kawo kwallah.

"Wannan ba rainon da ki ka yi min ba ne Hajiyata, ban taba yin zina ba, ban taba kusantar ta ba, tun ban san ma'anar ta ba kike nusar da ni illar ta, kuma har in mutu ba zan yi ba insha Allahu.
Ina baki hakuri Hajiyarmu, domin hakika na miki laifi, (na yi aure a Jamus ba da saninki ba)".
Dogon Salati Hajiyar Nahuce ta saki,
"Aure kamar ya ya?"
Habibu bai bata amsa ba, sai ya kara mika mata Abdallah, wannan karon ba musu ta sa hannayen ta biyu ta karba, tunda dai ta samu tabbacin ba shegen sa akai ba. Sannan kalmar aure ta gitta. Komai zai biyo baya a ganinta zai kasance da sauki.
Chapter 1 · 0% Book details