← Book details Matan Asokoro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 25

Sashe 9

Matan Asokoro Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

yadan kwashe da dariyanshi irin na boss sanan yace "yar talaka zaka auro wacce zaka batada kudi tadinga binka irin matan nan da idan kayi fushi har kuka zasu dinga maka suna rokonka karufa musu asiri, ance kudi baya sayan komi billahillazi abokina karyane, kudi nasiyan komi na duniyan nan saidai in mutum baisan ta yanda ake siyaba" suka kwasheda dariyan iskanci, cikeda takaici Baba Khalid yace "can you believe it Attajiri waini zanjema yarinyar nan tacemin ita bazata bayarba sabida tai rashin lafiya bance mata yajiki ba, ni namayi yaji bazan komaba" dasauri Attajiri yace "ohoho, banda abunta irinmu bamu tambayan mata komi yooo ita tama isa ai saidai suyi rashin lafiyan sanan suzo sucemana sunji sauki Baby nagode da kuladani, kuma bazaka komaba katashi komawa gidan nan saidai ka koma da amarya, inda ninekai mata biyu zan kara alokaci daya, daya bazawara wacce mijinta ya danna mata saki, tayanda tana auranka zata darajaka tasan aurenta nada auren wahala tayi sanan tabiyu kuma ka auro yarinya danya sharaf, kabula abunka kaci ana maka godiya iyaye na zuwa maula, kuma kanuna musu duk wacce tamaka hauka danna mata saki zakayi ka koreta daga gidan nan fess zakaga ana kappa kappa dakai, sanan dukansu agidan nan zaka zubasu wlh kanayi kana gumama Hassana tasan cewa kaiba nawasa baneba" wani irin kwashewa sukayi da dariya bana wasaba, da kyar suka tsayarda dariyan Baban Khalid yace "to yanzu yaya za'ayi zanyi managing mata guda biyu a lokaci daya kuwa? Sanan gakuma Hassana su uku kenan" "kai waketa wani maganing kai manager ne? Suyi managing kansu dai kai kazuba musu kudi kayi gaba abunka" dasauri yace "itakuma Hassana nasan yanda zanyida ita wlh zata ganewa hayazaki saitasan tayi kuskure abinda tamin" "correct yanzu kai magana Gwamnati amman da ka tsaya kana wani magana kaman wani wawa" murmushi yayi sosai yace "to yanzu dai yaya zamuyi banda wacce nakeso" dasauri yace "kai! Wake maganan wani wacce akeso anan wurin? Yanzu dai akwai wata mata danagani a office dinka, mai zuwa muku shara da mopping" dasauri yace "Mrs Saudatu" dasauri yace "yes ita kaga matarnan akwai kayan harka ajikinta kuma bakacemin mijinta yamutu ba?" Dasauri yace "yes mijinta yamutu, tanada yara uku though wai basa tareda ita suna family mijin ni tausayi ma tabani nabata aikin sabida yaran" dasauri yace "to itace bazawaran dazaka aura, worker dinka ce dagudu zata yarda and kabata kudi dajin dadi she go craze follow u, banda haka kanuna mata bakasan auren yadauki lokaci zaka mata komi na kayan daki, kawai tafadama nawa takeso sadaki azo adaura aure bakason bata lokaci period zakaga jikinta yafara rawa, kafin auren ma kana kiranta office fara da bata...
Inkika karanta batare dakin biyaba zaki biyani ranan dabaki dashi, this book is not a free book, pls support me.

Wuraren 12 yakai office direbanshi yafito yabudemai baya yafito yana sanye cikin suit yayi kyau, security guard nahangoshi yabudemai kofa ya shiga, anan reception yaga wata mata zaune da Hijabinta ash color ajikinta dayadan kunne takusada gefen wuya, black beauty ce itama kyakkyawa abinta kana ganinta kasan ba yarinya bace zata iyayin 39 kokuma 40yrs haka, saidai batada jiki kaman Hassana, ita siririya ce, tana ganinshi harwani ijiyan zuciya tasauke tana addu'a Allah yasa ba laifi tayiba wanan da sakatare yace "Oga yakira yace tajirashi karta tafi, batare daya kalleta ba ko amsa gaisuwansu yawuce sama sanan yabude katafaren office dinshi dayake a gyare yashiga tareda zama a chair, saida yabata kusan 15min dudda babu abinda yake sanan yadauki wayar office yakira sakatare yace "aturomai ita" ijiye wayan sakatare yayi ya kalleta yace "Sir is ready to see you now" gyadamaikai tayi ahankali sanan ta tashi itama tai sama saida tai knocking kofar aka bata izinin shigowa sanan ta shiga ahankali tareda kofa yana zaune yakafeta da idanu, sanan yanuna mata daya daga cikin kujerun dake gaban desk dinshi yace "sit" karasowa tayi tazauna gabanta nafaduwa tama kasa magana batasan anything dazaisa tarasa this her work dan ana biyanta da kyau dashi take saima yaranta da mahaifiyarta yan abubuwan daba'a rasaba, anatse cikeda tsoro tace "yallabai gani nan Allah dai yasa bawani laifin nayiba, ance kana nemana duk tsoro yakamani" murmushi yasakin mata ahankali saikuma yagyara zama yadaura hannunshi kan table yace "niba yaro bane, sanan kema ba yarinya bace, so I would like to skip all the talk and cut to the chase" dasauri ta gyadamaikai har lokacin gabanta nafaduwa, sanan anatse yace "aurenki nakeso nayi Saudat, ni bana harkan yara ko harkan iskanci, kinmin inaso na aureki na killaceki agidana a inuwata, all abinda kawai nake bukata itace yardanki da amincewanki, banson kiyi tunanin kaza kaza kaza ko abubuwan dazaki kawo gidana kokuma wani abu, nariga nasan kewacece, nasan karfinki saisa zandaukemiki duk wani nauyin kayan daki dawace tsiyace ke kawai kadai zaki shigo gidana, sanan bansan wanan hayaniyan bikin da sauransu niba yaro bane, sonake dazaran kin yarda kawai a daura aure dayar walima nazo nadaukeki nakaiki dakinki" yanakaiwa nan yay shiru yana kallonta kaman yanda take kallonshi in a total shock, saikuma tadaura hannunta akan kirji tace "Yallabai ni? Kodai mistake kayi? Ninefa Mrs Saudat mai shara da wanke bayi da mopping a kampaninka" gyadamata kai yayi yace "kwarai kuwa nasan kece, kuma kedin yanzu nake kokarin namaidake matar mai kampanin gabaki daya" yay maganan yana kallonta yana murmushi yace "by the way bazan takuraki ba, zan baki dagayau zuwa gobe dan banison bata lokaci kiyi tunani, idan kin yarda ayi, gobe war haka ina jiran amsa" gyadamai kai tayi tama kasa magana still, saikuma ahankali tatashi zata juya yace "tsaya" juyowa tayi takalleshi wasu code ya danna a drawer table dinshi sanan yajawo table din kudine burjik aciki, rappa na dubu dubu yadauko guda uku that's 300k yamika mata yace "take this, use it ki bata kanki dashi, ina jiranki gobe" kallon kudin tayi tana zaro ido daikuma ta kalleshi, babu wasa yace "karba mana Saudat nakine" mika hannu tayi ta karba zata zube tamai godiya yace "banson godiya wuce kitafi" wucewa tayi tafita daga office din rikeda kudi, tana fita ta tsaya taciro handbag dinta tazuba kudin aciki sanan tasauka kasa tafita tana wani irin farinciki wayyo dadi.

Tana fita yakira number Attajiri yace "nayi yanda muka tsara" kwashwwa da dariya Attajiri yayi yace "she is coming back with a yes na me tell u kawai kaman kayi aure kagama, ga wanan gidan, uwarsu da su kansu yaran sun rude, Maman harda kukan murna, nace musu gobe zamuzo tare, sati biyu mukeso asa sunce sun yarda, yanzu kira masu furnitures azuba kaya afalo, kasake komi sabo sabida kar hassana tabaka problem kayan falon dana kitchen duk akai store kazuba sabo komi yazama mallakinka kayanta atattare matasu a store" cikeda farinciki yace "angama abokina" .
*************

Tana zaune a falo itada yar aikinta dake matsa mata kafa akai sallama yar aikin ta tura ta amsa saigata tashigo tace "wai Alhaji yaturosu" shigodasu tasa akayi, gaidata sukayi cikeda respect sanan sukace "Hajiya Alhaji ya aikomu, yace mu kwashe duka kayan falon nan, da kayan kitchen dakuma kayan dakunan sama banda naki mukai chan store, wai za'a zuba komi sababbi ne" shiru tayi kaman mai tunani saikuma tace "okay" tashi tayi takalli yar aikinta tace "zaki iya wucewa gida yanzu Bibalo tunda kinga aiki za'a min" "tom Hajiya" tai maganan tanayin hanyan waje itakuma tawuce sama tashige dakinta tareda maida kofa tarufe, daman dakunan saman bawani kayan kirki bane aciki dudda kowanne da hadaddun gado aciki ga dakunan fadi da girma sosai, tanaji anata kwashe kwashe ana fitarda kaya hakanan taji tana kewan Murtala dayananan dayanzu tasa yafita da ita dan kara ya isheta, haka sukai aikin nan har yamma basu gamaba saidai suka hakura gobe zasu dawo sukarasa, koda ta sauko kasa saitaga gidan kaman banata ba, komawa kawai tayi sama abinta.

Washegari ne suka karasa fitarda komi sanan aka fara wani irin mahaukacin Fendi, ko'ina na gidan harda kitchen din, dansai fentin yabushe tass sanan za'a shigoda sababbin kaya, kawai she's feeling way to lonely inama ace ranan visiting yaranta ne yau dataje school dinsu wlh kota gansu taji dadi, tama rasakan gane gyaran me Baban Khalid yakeyi duddda tasan yanada yawan gyara gida, but tasan at this point dasukai fada bazai gyara gidaba to kodai that's his own way of saying sorry ne, kwanciya tayi kan gado sanan takalli agogo taga 6 but haryanzu Murtala bai dawoba kodai bazai dawo yaubane amman kuma baya ketare dokanta, gashi har masu aiki sun gama sun bude kofofi da windunan falo sun tafi sabida fentin yasha iska, tashi tayi tawuce bayi tadauro alwala tazo tai salla tazauna tana lazimi tai kewan gidansu tanaso taje gidansu taga Babanta, kuka takeji amman tahana kanta tadaure kawai tazauna tai shiru tana wajen aka kira isha'i ta tashi tayi tai shafa'i da wuturi sanan tasake zama tai shiru gabaki daya ranta bayamata dadi.

SHAKUR

EPISODE 6️⃣
Chapter 9 · 0% Book details