← Book details Matan Asokoro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 25

Sashe 3

Matan Asokoro Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Jin ranta na tafarfasa yasa tajawo wayanta daga cikin jaka taciro tashiga dial calls dinta saiko ga number Martala Driver tai dailing number shi, yana tsaye bakin titi suna hirada mai rake dake yanka rake saiga wayanshi tashiga ringing dasauri yatura hannunshi cikin wandon yaciro wayan techno yar rakani toilet, musamman yasa akamai Saving number Hajiya da S shikuma Alhaji da A dan yagane idan takira yana ganin kiranta yadaura hannunshi aka amugun rude cikin hausanshi nayan kauye yace "na shiga uku na lalace, Hajiya" dawani irin gudu yajuya ya kalli asibitin hangota tsaye yasa damugun sauri yajuya yasake tura hannu cikin aljihu yaciro wata 500 yamikama mai raken yace "kai bani Hajiya ta tafito, yau nidai nasan na shiga uku" baima jira cewanshi ba ya fizge ledan yawuce, Mai rake yace "ga chanjin ka kabari" titi yashiga da gudunshi yace "nabaka" da gudu ya tsallaka titin ya shiga asibitin duk tana binshida mugun kallo, yana karasowa gabanta ko wata wata baiyiba yawani irin zubewa agabanta yace "Hajiya dan Allah kiyakuri, wlh nasan kinsha gayamin muka fita na tabbatar ina cikin mota idan kinfito, tuba nake Hajiya, Allah yahuci zuciyanki, Allah ya sanyaya kafadunki, tubanake Hajiya" ayanda takejin haushi zata iya shureshi da kafafunta tadai daure cikin fushi tace "my friend will u stand up and open car for me" dasauri yace "eh Hajiya mekikace"? Wani irin runtse ido tayi cikeda takaici tuna bamaya gane turenci, dan dagokai yayi ya kalleta ganin yanda tayi yasa yace "dan girman Allah kiyakuri Hajiya wlh daman rake nasayo miki wlh" yamikamata raken dake leda, bude idanunta tayi tadakamai tsawa. "Murtala katashi kabudemin mota nabar wajen nan!" Abirkice dukya rude yatashi garin hakama yasaki ledan raken suka watse awajen tabishi da mugun kallo dayasa yatashi da sauri yatura hannu a aljihu yaciro hadadden car key sanan yadanna lock tabudu, kafin yabude kofar owner sit yasaukarda kanshi kasa yace "Allah yahuci zuciyan Hajiya, tuba nake matan ranka shi dade, takawanki lpy uwargijiyata, shiga muje" mtswww taja wani wahalallen tsaki tajuya tashiga cikin motar ahankali kanta na mugun sarawa yamaida kofan yarufe, raken daya watse awajen ya kalla har ranshi soyake yatsugunna ya kwashe kayanshi amman tsoron masifan hajiya yake, bude gaban motan yayi ya shiga ya rufe yaja sit belt yasaka saikuma ahankali yaleko bayan sit din ya kalleta kanta na kasa tana kallon wayanta datake latsawa kaman mara gaskiya ahankali yace "Allah huci zuciyan Hajiya" dagokanta tayi tazubamai red eyes dinta dahar lokacin suke nuna alamun kuka, hakuri zai batafa amman ganin yanayin idanunta yasa dasauri yace "Hajiya kuka kikayi? Innalillahi maiya sameki anmiki wani abu a asibitin nanne? Waya batamiki rai eh inje inkoyamai hankali wlh saina barar da mutum na shemar dashi, waye ne Hajiya"? Yanda taga yadamu sosai danya nuna afuskanshi yasa har ranta saitaji dadi, dan yatsine fuska tayi cikedason yamata shiru dakuma tarin gajiya tace "nagaji ne kaini gida kawai nahuta Murtala" da sauri yajuya yatada motar yajada sauri yace "Hajiya sannu, kinga baki saba wanan aiki hakaba, keda kikeda likita dayake zuwa har gida yadubaki maisa kikazo asibiti nan kikabi layi saisa kanki keciwo, sannu Hajiya, Allah huci zuciyanki, yanda kikagajin nan bazanbi hanyar zuwa ASOKORO ba dan akwai go slow, akwai wata short cut hanya dazanbi yanzun nan zakiga munkai ranki shi dade".

Chat me up directly by clicking on this link
https://wa.me/+2347012181461

_This is the only free page of this book, like I said, wanan novel din bakaman normal novel dina bane, I interviewed so many couples, I want to show the world inda akafi samun matsaloli arayuwan auren mu tayau and how to go about it. I trust my fans, u all knows yanayin rubuta, ku gyara zama, wanan littafi shine ga darasi gakuma dadi, lemme say it again please 🔞, anybody less than 18 shouldn't read this book, thank you._

Chat me up directly by clicking on this link https://wa.me/+2347012181461

_This book is 2k, idan kinaso pay into 3107021073 aisha Muhammad first bank and send evidence of payment to my watsapp number 07012181461 sainai adding naki a group din danake posting_

💫 _MATAN ASOKORO_ 💫

✍🏾M SHAKUR

_RANAKUN POSTING *SUNDAYS*, *TUESDAYS,* *FRIDAYS*_

_DAN GIRMAN ALLAH KARKI KARANTA THIS BOOK IN BAKI BIYABA, KUJI TSORON ALLAH_

EPISODE 2️⃣

Ko alamun taji magananshima batayiba saima cigaba da danne dannenta datayi awaya tana chatting a group dinsu na ASOKORO WIVES, gajiya tayi saikawai ta ijiye wayan sabida yanda kanta kewani irin sarawa datarasa maisa, sanan gently ta jinginar da kanta jikin kujera ta lumshe ido. "Hajiya wai lapiyanki kalau"? Bude idanunta tayida sauri jin Murtala yasake mata tambaya ta madubin mota suka hada ido dan gajeren wahalallen tsaki taja tamaida idanunta ta lumshe su ahankali back, maida hankalinshi yayi kan tukin harsu ka shigo ASOKORO District, Usman katsina street suka shiga yay horn agaban wani makeken mansion da tsayawa bayaninshi aikine ganin ba'a bude gate dinba yasa yace "auuuu kullum saina manta abin nan" yay maganan yanadan juyowa ya saci kallon Hajiya yaga tana kaman bacci danhar lokacin idanunta a lumshe yasan inda idanunta biyu datamai bala'i kan kullum saiya mantada remote din da ake bude gate dinsu dashi, remote din dake motar yadauka ya danna gate din yabude sanan yasa kan motan suka shiga cikin gidan gate din yarufe kanshi, kafin ahankali yabude kofa yafito sanan yazagayo ta bangarenta yabude kofa tareda bending kanshi cikeda respect yakira sunanta ahankali danya tadata daga bacci. "Hajiya, Hajiya" dan bude idanunta tayi ahankali tazubasu akanshi awulakance, baidamuba yace "mun iso gida ne daman saisa natadake" yunkurowa tayi tanajin kaman kanta zai fice amman saita daure tafito hakan yasa shima ya matsa yakoma baya, fitowa tayi daga motar ta tsaya da kyau da sauri tasake kulle idanunta jin wani irin jiri take gani hakanan all of a sudden, hakan yasa Murtala daya koma baya yace "Hajiya karkice nacika tambaya amman kaman bakida lpy wlh, duk jikinki ya nuna hakan" bude idanunta tayi tazubamai wani matsiyacin kallo dayasa yaji cikinshi ya murda ahankali yamaida kanshi kasa, daukekai tayi tace "kwasomin jakata da wayata" tai maganan sanan tajuya tafara tafiya gashi daganan parking space zuwa flat dinta dadan tafiya, amman hakan take tafiya ahankali dai dai gudun kartaje tazube dan bamatasan meke damuntaba jitake kaman sauran kiris jikinta yakasa daukanta, akwai staircase haka dazai sadata da kofan shiga flat dinta ahankali take hawa staircase din cikeda karfin hali irin nata da kyar ta iya daga kafanta tahau na karshe batasan meya faruba tadaijita akasa sharaf, sanan kuma taji ihun Murtala sama sama, kara lumshe ido tayi tabude sanan taga Murtalan agabanta ya tsugunna ya haukace yakasa tabata sama sama takeji yana Hajiya, Hajiya, sake lumshe tayi tabude batasan meke going on ba tadaiga waya akan kunnenshi saikuma kawai taji yadauketa, kadan kadan take bude idanunta she could feel and see yanda heart dinshi ke beating, ke racing sosai na fargaban kar wani abu yasameta saikuma dip ta dauke wuta.

Kwantarda ita yayi akan katafaren doguwan kujeran dake falon cikin jerin hadaddun kujerun dake wajen, sanan yatashi da sauri hannunshi har rawa yake ya shiga dailing number Alhaji for the second time yamugun damu dudda yasan Hajiya was never nice to him but still baisan wani abu yasameta.......

Wajen 30 big men ne zaune awani babban conference room, sunci uban suit, wani hadadden magidanci mutum dake zaune kan kujeran CEO ne ke magana yana bayani da turenci, ringing dawayanshi yasakeyi for the forth time yasa yakalli wayan, daukan wayan yayi a hannu yatashi tareda fadin "excuse me" sanan yafita daga conference hall din yakara wayan akunnenshi, kafinma Murtala yay magana yashiga balbaleshi da masifa. "Ka kirani kace tasuma nace ka dauketa ka shiga da ita ciki zan kira Dr, basaika jiraba, saidamuna kake da kira kasan wani irin meeting nakeyi ne? Kaiwani irin wawan bakauyen yarone wai? In nagama I will call d Dr yazo yadubata, kawai yanzu ka tsaya tareda ita, karka barta ita kadai, babu abinda zai sameta ai Hassana is a strong woman she will be fine" ya katse wayan zai maida a aljihu saikuma yaciro yama kashe wayan gabaki daya dan yasan Murtala baida hankali he will keep calling him this meeting is very important anjima idan suka gama zai kira Dr su yasa yaje yadubata, da sauri yawuce yakoma ciki wearing a smile akan face nashi yace "sorry gentlemen let's continue"......
Chapter 3 · 0% Book details