← Book details Matan Asokoro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 25

Sashe 5

Matan Asokoro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kaman an tsikareta tabude idanunta ahankali tanabin inda takeda kallo tabbas tasan nanba gidanta bane, ahankali tajuyarda kanta karin ruwa datagani dakuma oxygen da akai hanging datagani yasa ta lumshe ido dan tagane she's sick but inane nan? Yunkurawa tayida kyar ta tashi tazauna tanadanjin jiri kadan, sanan ta kakkalli gefenta but babu jakanta babu wayanta balle takira wani, sakebin dakin asibitin tayida kallo taga emergency room ita kadaine aciki nothing to talk about wanan wani irin local daki takene, jitayi warin asibiti da dakin keyi na irritating nata yasa cikeda karfin hali irin nata ta yunkura tasauka daga kan gado tana zura takalminta takama karfen da ruwan kejiki dasauri ta lunshe ido, ahankali taja tasaka hannu tabude kofan tafita tana tafiya kaman zata fadi, tabi wajen dakallo babu kowa a wajen kaman ance ta kalli side dinta Murtala tagani ya kudundune jikinshi kan kujeran wajen yana bacci yana sosa hannu daga gani kasan sauro ke cizonshi, tsareshi tayida idanu ranta nabaci mesa zaikawota irin wanan asibitin, wani irin sarawa kanta yayi sabida bacin ran dataji saikuma wani irin mahaukacin jiri yazomata tai baya zata fadi tana kokarin rike karfwn da ruwanta ke sagale shikuma yabugi bango yay lara hakan yasa firgigit Murtala yafarka tareda dagokanshi ganin Hajiya idanunta na juyawa tana kokarin faduwa but tana kokarin hana kanta yasa yawaniyi tsalle yace "Hajiya" tareda tarota tafada kan kirjinshi, ko kawo wani abu baiyiba kawai yadauketa chak dukya rude sanan yaja karfen ruwan yabude dakin yace "mesa kika fito Hajiya aidakin kirani" ahankali tabude idanunta tana kallon fuskanshi yanda damuwa yanuna ko'ina akan fuskan, kirjinshi nabugawa fat fat fat tsoron karta fadi dayaji yasa taji something that is very very strange azuciyanta, she just wish and wish inama Baban Khalid ne haka looking so worried and so concern about her datafi kowace murna aduniyan nan. "Hajiya!" Firgigit tafarka daga tunanin dataje ashema harya zaunar da ita kan gado, cikeda damuwa yace "menene kikeso maiyasa kika fito tsakar daren nan? Jirifa ke mugun damunki? Meke miki ciwo yanzu? Nakira Dr"? Tunda yakemata tambayoyin take kallonshi saida yagama sanan tahade rai tace "ubanme nakeyi awanan kazamin asibitin? Wayakawoni nan?" Shiru yayi yasaukarda kanshi kasa shidaman yasan yayi laifi. "Ina maka magana kamin shiru Murtala!" Tadakamai tsawa dayasa tasake kama kanta dasauri jin kaman zaifita tace "wa....." ganin yadago kanshi ya kalleta yasa tahadiye sauran wash din tai maza ta cire hannun tasake daure fuska zatai magana yace "Hajiya dan Allah kiyihakuri kinji, bakida lafiya baki bukatan hayaniya da fada ko fushi, kinajin sauki zan gayamiki komi kinji Hajiya" ahankali tajinginar da bayanta da bango tanadan yatsine fuska tace "ka kira Alhaji? Meyasameni, mesa kakawoni nan"? Yanda tamai maganan babu wasa yasa yace "kina sauka akan mota kika fita kin fara hawa stairs kawai naganki akasa kina wani irin nishi........." nan yagayamata komi har zuwa yanzu, dan murmushi tayi tace "ayya meeting din must be very serious, jeka kiramin Dr" tai maganan kaman bakomi da sauri yafita daga dakin, daidainan hawayen data rikesu tunda yafara gayamata abinda yafaru yazubo mata sharrrr yanzu inda ace Murtala bai kawota wanan kazamin asibitin ba dahaka zata mutu abanza, Baban Khalid bai kira Dr ba saima kashe wayanshi dayayi irin ko ajikinshi dinan, baimaso adameshi da batun rashin lafiyanta yana aikin office, Baban Khalid Mijine wai ko Makiyi? Ta tambayi kanta! Jin alamun tafiya yasa da sauri ta share hawayenta tass, daidai anbude kofa Dr yashigo Murtala biyedashi yana kallonta yace "Hajiya kuka kikayi"? Wani irin mugun kallo tamai tace "fita daga dakin nan zanga Dr" babu gardama yajuya yafita yarufomusu kofa, Dr yay murmushi yace "why are u treating someone that saved your life today like this"? Murmushi yayi yakaraso gabanta yana gyara karin ruwan yace "I understand he's your driver, but koma a direban ne i must applaud his effort, I am telling u dabadan guy dinan ba we would've lost you by now, at the time daya shigo dake this hospital inda ace kin kara just 5min without seeing a Dr da heart dinki yadaina aiki, haka yashigo dake he was crying sosai" dasauri ta kalli Dr tace "crying"? Murmushi Dr yayi yace "abin yabaki mamaki ko kema, aiko kuka sosai kaman yaro wai dan Allah mutaimaki Hajiyan shi, ya tsareni wai a mota zan miki treatment baki zuwa asibiti da kyar fa yabari muka shigodake that zakiyi fada" for the first time tadansaki murmushi iya lebe, saikuma ta kalli Dr tace "what is wrong with me Dr, maisa nai passout like that"? Kujera Dr yaja yazauna sanan yace "kinada wata damuwa ne, is there anything wrong with you or bothering u"? Wani kallo tamai saikuma ta tabe baki tace "ni babu abinda kedamuna, namaka kala damai damuwa ne kakemin wanan tambayan" shiru Dr yayi yana kallonta, daga this magana datayi yagane yes tanada damuwan but she's the hard and strong type no need to even pressure her bazata fadimai ba hakan yasa yace "some of your results are out, some kuma sai gobe dasafe, kinada hypertension, and heart dinki at this junction is very very weak, bawai kinada ciwon zuciya or anything bane no! Just that heart dinki is weak, dole ki kulada kanki tsantsa dam at any point u can just collapse kimutu, dole kicire ma kanki damuwa, you should put yourself first before anything and anyone, kome kikasani dat will make u happy just be doing it, duk wani abu dake baki damuwa da matsala avoid it, I am sorry idan maganan nan yazo miki like this, I see u are strong u can handle it, and I also believe now that I tell u you will do all u can to keep yourself happy and healthy, so just do that" tunda yafara maganan tai shiru tana sauraronshi harya gama, sanan ya kalleta yace "any question" murmushi tayi kaman ba ita yabama wanan hard details din on her health ba, tace "i want to leave dazaran gari yawaye how much is my bill zan muku transfer" da sauri Dr yace "is not advisable for you to leave kibari mugama miki treatment, and issue of bill kuma your driver yayi taking care of that" da sauri ta kallai saikuma tasauke kanta ta kwanta akan gado tace "once it's morning am leaving, I have my Dr he will take it from here" yanda take maganan zaka gane bawai permission take magana ba, murmushi Dr yayi yasakai yafice yasaba da irin matan nan masuji dakansu ga shegen girman kai da fadin rai shidai Murtala na zaune bakin kofa yaga Dr yafito yawuce hakan yasa yatashi ahankali yabude kofan kaman matsoraci yaleka hada ido sukayi da Hajiya yanda tabishida kallo ba kyaftawa yasa yasauke idanunshi kasa yace "Hajiya dama na leko nagaya miki ina nan bakin kofa idan kina bukatan wani abu kawai kidan bubbuga wanchan drawer inajin karan zan shigo kinji" yanda ta tsareshi da idanu batare datace wani abuba yasa ahankali yajuya yamaida matada kofa yarufe ahankali tasauke ijiyan zuciya itama tarufe idanunta.

Hakanan tasami kantada mikarda hannunta zuwa kan drawer kaman mai tsoron drawer tadan buga kadan kafin tagama janye hannuwanta tadawo dashi jikinta taji anbude kofa da sauri karasowa gabanta yayi yadukar dakanshi kasa cikeda girmamawa yace "Hajiya gani, me kikeso? Nakiramiki likita ne"? Samin kanta tayida bude idanuwanta kadan ta kallai saikuma ta dauke kanta ta kwanta akan gadon taredajan bargo ta juyamai baya sanan ahankali murta chan kasa tace "ga kujera kazauna anan, waje akwai sauro gari na wayewa zamu tafi" "angama Hajiya yanda kikeso haka za'ayi ranki shi dade, Allah karamiki lafiya Hajiya" yay maganan yana daukan kujeran ya matsarda ita baya zuwa chan jikin bango sanan ya zauna, yaso zamanshi awaje atleast yadan mike hakarkari akan kujeran amman wanan dole sai zama yatsine fuska yayi yana gyara zama ya jinginar da kanshi ga bango sanan ahankali ya lumshe ido yana sauke ijiyan zuciya, ko 2min ba'a yiba bacci yay awon gabadashi sai minshari waaaauuuuuu! Juyowa tayida sauri ta kallai jin yanda yake munshari kaman rago, ahankali ta gyara kwanciyanta tana binshi da kallo tundaga kan kafarshi dake cikin silisaf din gida, yanada babban kafa dan diddigenshi ma awaje yake silifas din yamai kadan ga kafarshi fara itama, sai bakin wandon jikinshi na jeans dayay datti sosai, yatsine fuska tayi tabi rigan da kallo itama tai datti gashi kirjinshi very huge ga fadi gakuma cika kaman yana daga karfe, ahankali tasauke idanunta kan wuyanshi fatarshi suli suli gadan gemunshi dabaida wani yawa, saikuma tasauke idanunta akan fuskarshi ahankali tafadi azuciyanta Murtala fa mugun kyakkyawane, kauyanci darashin son gyarane yasa yake hakafa, and he is so innocent, despite the fact bata sakinmai fuska, batamai murmushi kullum cikin fada takemai dudda mugun tsoronta dayakeyi dan yana mugun jin tsoronta samada Alhaji ma dan yana hira da Alhaji sosai, itako bayayi da ita, but despite all of this he saved her life, yamata abinda ko mijinta baitaba mataba, she's so grateful to him dudda bata nunamai ba but har kasan zuciyanta taji dadin abinda yamata and for the first time duk tsanan nan datamai na dan kauye ne bai iya karatu ba duksai taji yakau. Kiran salla dataji anyi yasa tadan gyara kwanciya tace bari atada sallan asuba saita tadashi sutafi gida she needs a very clean and hot shower, lumshe idanunta tayi ahankali tana sauke ijiyan zuciya komida Dr yafadi mata suna kara mata yawo akanta, how will she stay happy now, kodai ta tattara taje gidansu tazauna cikin family tane koda na one month ne, but tana zuwa za'ai sensing something is wrong and Baban Khalid ma zai yardane yabarta taje gida tai one month, sarawa da kanta yayi yasa tahakura da tunanin tasake juyowa tazuba idanunta kan Murtala lokacin ana shirin tada sallan asuba. "Murtala" takirashi ahankali, firgigit yabude idanunshi dake cikeda bacci ya kalleta hada ido sukayi da sauri yatashi tsaye yana sosa kanshi yace "Hajiya gani, akira likita ne? Mekike bukata"? Girgizamai kai tayi softly tace "tafi masallaci kai salla kana dawowa saimu tafi" gyadamata kai yayi yajuya yana tafiya ahankali yafita tabishi da kallo ita karan kanta tasan yagaji.

_Hi Ladies let's deliberate small on this issue. Yanzu if Hajiya start developing something ma Murtala will you all blame her or blame mijinta?_
Chapter 5 · 0% Book details