← Book details Matan Asokoro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 25

Sashe 12

Matan Asokoro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Horn yayi agaban dankareren building din gym dinshi mai gadi yazo yabude yana gaidashi, parking motar yayi sanan yazagayo ta bangarenta yabude mata kofa yace "this is my gym, yau Sunday babu kowa, sai anjima, come and take a look". Yanda yake kallonta batada option but tafito ta masa da sauri gefenshi dan baya kunyan yimata wanan kallon kaman zai cinyeta, maida kofan yayi yarufe sanan yashiga gabanta yace "muje" ahankali suke tafiya har zuwa entrance, glass slide door ne daga waje kana iya hango uban equipment din daya cika wajen, gakuma wani katon space nayin aerobics, budewa yayi ya shiga hakan yasa tabishi abaya tanabin gym din da kallo dan yamata kyau sosai sai nuna mata komi yake, juyowa yayi ya kalleta suka hada ido da sauri tadauke kai, murmushi yayi yace "zomuje kiga office dina" girgiza mai kai tayi dasauri dan hakanan taji gabanta yafadi daga ita sai shi awajen nan yakaita office dinshi karya mata wani abu hakan yasa tace "babu wanda yasan nafito daga gida mutafi next time nadawo naga office din" while looking at her face yace "kinyi alkawari ko" gyadamai kai tayi ahankali har lokacin taki kallonshi, ahankali yadan matso gabanta sosai jin alamun mutum yasa tajuyo dasauri, bakintane yafara rawa tace "m...e....me haka"? Murya chan kasa akuma mugun shagwabe harda dan turomata baki yace "to zaki aureni? Kinga anjima Abba zai kiraki kibada final amsa, please tell me tun yanzu zaki aurennn"? Tunda yake maganan fuskanshi take kallo da lips dinshi heart dinta na racing she really feels kaman tai pulling nashi and start kissing him all over is she really this lonely ko kawai sha'awa Murtala yake bata sabida yanda ya iya shiganta yana mata shagwaba kaman wani su Khalid infact kosu Khalid basamata shagwaba haka. "Baaaaby say something zaki will you marry me"? Yay maganan amugun shagwaban ce yana kara matsota sosai kaman xai shige jikinta da batasan lokacin data gyadamai kai tace "y.....yes....I will marry you" wani irin ihu da tsalle daya buga awajen yasa dasauri takai hannunta tashafa bakinta dan wlh batasan lokacin databashi amsa hakaba, tsugunnawa kawai taga yayi agabanta yakamo hannunta zoben zinaren dake hannunta taga yacire sanan yakai hannunshi Aljihu yaciro wata yar akwatin zobe yabude, sirovoski hadadden engagement ring ne kawai yasamata a hannu aiko zoben yazauna cip cip yamata mugun kyau sanan yatashi tsaye yana kallon fuskanta kaman yanda yake kallon nata, ahankali yace "wlh ina mutuwan sonki" lumshe ido tayi ahankali dan bamasai yarantse ba she could see it. "I am the happiest man on earth right now I feel like to hug you, kiss you, back you, dance with you, I feel like doing every damn thing with you right now, wayyo Allah zuciyata can't contain my happiness, I love this woman yoooooooo" yawani yi uban ihu dayasa ta fizge hannunta tadan harareshi tace "mutafi" saramata yayi dasauri yace "yes her majesty" ita tafara fita yabita abaya yana murmushi yanajin dadi, suna kaiwa motan zata bude dasauri yasha gabanta yabude mata, kallon fuskanshi tayi ya dagamata gira daya sanan tashiga tazauna yamaida kofan yarufe yazagaya yashiga yatada motan suka tafi, yanda yake murna suna tuki yasa tama manta da duka damunta she can't believe saurayi kakkyawan gaske ajin farko, masculine well built body guy haka that is doing well yanada rufin asiri da she can swear yanmata na rububin Murtala amman yanace ma tsohuwa bazawara mai manyan yara irinta yanaso and yake farinciki haka sabida ta yarda zata aureshi. Allahu Akbar lallai Allah mai sharema bawa hawayenshi ne, wato idan kai hakuri kowace kalan jarabawa kake ciki rana daya Allah zai sharemaka hawayen ka, haka tadinga tunane tunane tana kallon zoben daya samata a yatsu itace da engagement ring kaman wata yarinya but tanson ring din yama hannunta kyau sosai, ahaka harya kawota gida.

Awaje yay parking sanan yaciro ring dinta daga aljihu yana kallo yace "you should rest for now, dan your owner am now her owner" daukekai tayi tai kaman batajishi ba sanan ya ijiye zoben yabude motan yafito yazagayo yabude mata, fitowa tayi itama, key motan yabata yace "natafi ko karnai latti azo anata jirana bani a gym" karban key tayi yana wani irin kallonta sanan ahankali kaman baiso yatafi yace "bye" dan kallonshi tayi itama sanan tace "bye" wucewa yayi yafara tafiya da sauri sauri samin kanta tayi dakasa shiga gida ta tsaya tana kallonshi yanzu haka zaiyi tafiya har zuwa bakin titi sanan yasami abin hawa yakoma chan gidan gona yadauko motanshi sanan yakoma gym, jingina tayi ajikin gate tana kallonshi she super love him amman bataso ta nunamai ne kawai sabida karya rainata, ahankali tadaga hannunta ta kalli ring din saikuma tasake murmushi ranta fess fess

[11/7, 9:39 PM] +234 814 944 7697: 💫 _MATAN ASOKORO II_💫

✍🏾M SHAKUR

_how about yau nabaku solution to all your skin care issues??? Introducing GLOW & GO NATURALS, suna saida abubuwa na gyara fata, dakuma cire pimples, black head, acne, eczema dasauran su, sunada kayayyaki kaman haka;_

Traditional glow soap
Honey and sugar scrub
Acne face cream
Brightening face cream
Acne face wash
Acne cleanser
Hydrating face toner
Glow sets
Acne sets
Glow oil

You can chat them up directly don sayan kayayyakin su by clicking on this link👇

https://wa.me/+2348144513333
GLOW & GO NATURALS is the best skincare company a Nigeria 💃🏿

EPISODE 8️⃣
Wuraren 10 nadare, tana kishingide akan gadonta, sukuma su Khalid na game da laptop dinta aka turo kofanta aka shigo Mama ce tana sanye da hijabi ta shigo dakin tashigo tace "ashe sunzo sun makale anan ne suna buga game" dan murmushi tayi tace "eh Mama duk sun cikani da hayaniya ma wlh" dariya Mama tayi tace "Baban ki nakiranki yana falonshi" gyadama Mama kai tayi itakuma Mama tazauna tareda su Khalid, yayinda ta tashi tadau hijabi tasaka sanan tabarsu suna hayaniya da Mama tafice daga dakin.

Ahankali tai sallama gaban dakin Baba, izini yabata ta shigo hakan yasa tabude kofa ta shiga ciki, yana zaune kan doguwar kujeranshi sanye da faran jallabiya idanunshi sanye da fararen glass na kara karfin ido hannunshi rikeda jarida yana karantawa, wuri tasamu ta zauna akasa sanan tace "Baba gani" linke jaridan yayi ya ijiye sanan yace "yan biyuna" ahankali tace "na'am Baba" murmushi yadanyi ganin kanta akasa, sanan yay gyaran murya yace "kafin namiki asalin tambayan dazan miki, bari nafara da baki dan labari dakuma shawarwari na rayuwa, mind you kowani decision kika yanke is final ni mahaifinki ne I am just a guardian arayuwanki" sanan yay dan shiru kafin ya nisa yace "zamanin Ma'iki, Annabi Muhammad amincin Allah su tabbata agareshi, matar daya fara aure Nana Khadija ta girmeshi sosai amman ya aureta, sanan idan kikazo wanan lokacin akwai labarai da dama na mutanen dasuka auri wayanda suka girma musu be it macen da girma mijin ko mijin ya girmi matan, Hassana kome zakiyi aduniyan nan inhar bai samaba Allah ba karki sake kiji kunyan mutane kokuma kiji tsoron maganganunsu magana bata kari kinajina kuma duk abinda Allah yanufa da faruwa to babu makawa saiya faru" gyadama Baba kai tayi ahankali, sanan yacigaba yace "arayuwan mu tayau idan kasamu mutum mai sonka, musulmi, mai tsoron Allah, ka aureshi karka jira komi, nasan kinyi tunani kinyi tunani, kinfini sanin waye yaron nan dudda nima nai aike kauyensu an tabbatarmin yaron kirki ne mai zuciyan nema ba malalaci ba, mahaifiyarshi tasha ciwo kafin ta rasu kuma ansanar dani yanda ya kulada ita yay jinyanta dudda yana d'a namiji bai gujeta ba danshi kadai Allah yabata, duka labaran danaji akanshi na arzikine da mutunci bana banza ba, ni idan kinason yaron nan dudda kinaganin matsayinshi ko dukiyanshi baikai nakiba bazan taba hanaki ba, kinga irin yara haka maza ne da Allah kesaka musu son matayensu har karshwn rayuwa kuma su tsaya tsayin daka akan matansu, Allah yaduba yaga kalan wahalan dakika sha arayuwan nan, makirin nan da Allah yatashi tonamai asiri ba baram baram sukazo sukai da shi Baban su Khalid dinba, nan nan falon nan Baban su Khalid yazo agaban kowa yana kuka duk abinda yamiki zigin Attajiri ne kiyafemai shi yana balain son matarshi har yanzu, but what? it was too late dan kin riga kin gama idda da dadewa ma, so idan Murtala yashigo rayuwanki ki dauka hawaye Allah yake shirin share miki ayanzu, and karkimai kallon raini ko wulakanci ganin kinfishi hakan babban kuskure ne amatsayinshi na d'a namiji ki bashi girmanshi ki girmamashi sanan ki daraja shi, yanzu sai tambayar inaso ki fadamin gaskiya karki sake karki kuskura ki cutar da kanki, kinason Murtala ko bakisonshi"?

Kanta nakasa takasa magana. "Hassana!" Baba yakirata da asalin sunanta dayasa ahankali tadago kanta ta kallai kaman yanda yake kallonta yace "kina sonshi"? Kasama Baba karya tayi ta gyada kanta ahankali alamun eh, hakan yasa Baba yace "zaki aureshi"? Nan ma gyadamai kai tayi ahankali alamun eh Baba, hakan yasa Baba yay murmushi yace "tashi kitafi, gobe zan kirashi nakira yayyinki ayi komi agama ayi fixing date banson bikin yadauki lokaci" gyadamai kai tayi sanan ahankali tace "Baba" dasauri yace "na'am" murya chan kasa tace "Baba dan Allah banson hayaniya abikin, afalon ka nakeso adaura auren, niba yarinya bace banson loud daurin aure" Baba yadade yana kallonta sai chan yace "don't be selfish Hassana, though I understand you, but at the same time, don't deprive Murtala wanan dadin da annurin da ango yake cikin tarin jama'an shi wajen daurin aure, karki manta wanan shine aurenshi na farko, tashi kitafi gobe idan yazo zanyi magana dashi" tashi tayi ahankali tawuce tafita daga dakin, koda taje dakinta babu kowa duksun tafi sun kwanta hakan yasa ta kwanta agado ahankali she can't believe tace yes, yanzu dagaske Murtala zata aura, she can't believe it.
Chapter 12 · 0% Book details