← Book details Matan Asokoro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 25

Sashe 4

Matan Asokoro Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Jikin Murtala har bari yake gabaki daya yama rasa maizaiyi gashi babu kowa gidan, dan ka'idan su shine ma'aikatansu basu kwana, da maid, gardener da sauransu duk dasafe suke zuwa suyi aiki sutafi, koma sunanan shibaisan mezaimataba, yana tsaye kanta chan yaga tai wani irin nishi ta bankare ta tashi, saikuma tafara Jan numfashi kaman numfashinta naso yadauke tana kakkama wuyanta, tsugunnawa yayi gaban kujeran cikeda damuwa yana tura hannunshi a aljihu yana ciro wayanshi zai sake dailing number Alhaji yace "Hajiya meke damunki na shiga uku, Hajiya badai mutuwa zakiyiba" ina Hajiya bamatasan wayeke akanta ba, yay dailing number kashe, sau uku yana kira wai akashe daidai lokacin tafado dagakan kujera tana nishin idanunta na kakkapewa shibaimasan meyakeba kawaidai yaganshi ya dauketa ko nauyinta bayaji yafita da ita daga dakin yawuce yabude mota yasata yagyaramata kafafuwa yarufe sanan yashiga gaba danna remote yayi gate yabude yasakai yafice aguje yana tuki yana juyowa yana kallonta yanda yaga tana battling da numfashi yasa kawai yasaki kuka. "Hajiya kiwa Allah karki mutu, kar yan biyu sudawo Marayu wayyo Allahna" kawai shima yahau kuka kaman yaro, wani babban government asibiti dakenan a ASOKORO yakaita yay parking yana kuka sosai yay cikin asibitin yana ganin wani Dr yafito shida nurse kawai fizgo hannun Dr yayi yana kuka sosai, Dr ma tsorata yayi dan yadauka mahaukaci ne yace "Malam lafiya"? Cikin kuka Murtala yace "Hajiyata batada lpy likita zoka taimaka mata dan Allah bata iya numfashi" jin maganan dayayi yasa Dr yabishi Nurse din dasuke tarena binsu har motansu yakaishi yabude Dr naganin yanda takeyi yama nurse alamu data kawo gado dasauri nurse tajuya shikuma Dr yashiga motan trying to help her yabude mata baki yana tambayan Murtala dake kuka har lokacin yace "meya sameta"? Cikin kuka sosai yace "kaman kanta keciwo saita sume saikuma tafara nishi haka" daidai ankawo gadon da za'a daurata, kallon gadon yayi ya kalli yanda Dr da Nurse ke kokarin cirota su sakata agado yace "ina zaku kaita"? Dr da hankalinshi baya kanshi yace "ward mu mata treatment" dasauri yace "likita karufamin asiri kabata magani anan cikin mota kokamata allura kawai mutafi yan gidansu basa kwanciyan asibiti sunada likitansu na gida, yanzu ma babu kowa agidan ne" likitan baimabi takanshi ba dan daga gani kasan illiterate ne, idan yabar matarnan within good 10min heart dinta zai daina aiki tamutu dan as it is ma yanzu heart dinta is very weak, ciki sukaida ita Murtala nabinsu abaya yana gayamusu zasu sashi a matsala, suna shigarda ita emergency room suka rufo kofa hakan yahanashi shiga, zama yayi akasan wajen yana share hawaye na tausayi dakuma fargaban irin fadan dazaisha awajen Hajiya da Alhaji yau yamusu asalin karambani wlh.

Yana zaune wajen wata nurse tabude kofa tafito yana ganinta yatashi da sauri yace "Ya jikin Hajiya"? "Da sauki, yanzu munsamata oxygen and per hour is 15k, yanzu anaso kai deposit din naira dubu hamsin" da sauri ya kalleta yace "eh dubu hamsin" gyadamai kai tayi tace "yes inba hakaba bazamu cigaba da treatment dinta ba, yanzu dai ansamu munyi stabilizing situation din idan kabiya kudine zamu cigaba" shiru yayi kaman wawa saikuma yace "kucigaba to bari naje nadauko kudin agida" Nurse din tace "you have an hour daga yanzu zuwa Magrib" juyawa yayida sauri yafita yaciro wayanshi yana dailing number Alhaji amman har lokacin akashe, rasa yanda zaiyi yayi yawuce yakoma mota yaja motar yakoma chan gidan, bangarensu boysqutars dakinsu yawuce direct, wata katuwar ganamasgo yayi yabude sanan ya shiga cirowa yana ijiyewa kan katifa sanan yaciro watayar leda baka yakoma gefe ya zauna yabude ledan albashinshine dayake cirewa yayi saving duka duka 80k ne yamaida ledan ya kulle sanan yatashi yafito daga dakin dasauri lokacin ana shirin kiran salla komawa asibitin yayi yabiya kudin komi yarike sauran 30 a aljihu sanan yatafi masallaci kafin yadawo yasake samun wuri gaban dakin ya zauna yasake ciro wayanshi yay dailing har lokacin wayanshi akashe abin yabatamai rai amman kuma meruwanshi shidan aikine tashi yayi yawuce masallaci jin ana kiran isha'i yayi yafita waje yaje yasha shayi da indomie sanan yadawo yasake zama awajen shiru babu wanda ya cemai wani abu har bacci yasake kwasheshi yay kwanciyanshi kan yar kujeran yana sharara baccin shi gwanin ban tausayi kana ganinshi kasan yagaji.....
Chapter 4 · 0% Book details