← Book details Masarautar Qamar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 24

Sashe 8

Masarautar Qamar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hurriya da kanta ta taka sukazo har inda Bintu ta samu wurin kwana Bintu kam dadi ta rinka ji don har ta goge hawayen ta.
Habiba kallo daya tayi ma Hurriya ta washe mata baki tace sannu yanmata Hurriya ko kallon inda take batayi ba bare ta sanya ran zatayi mata magana

Bintu kallon Hurriya tayi tace bari tayo alwala, waje ta fita sannan ta dawo ta gyara hijab dinta ta fara rama sallolinta har tagama Hurriya idonta a rumtse yake don ta jinginar da kanta jikin katifa.

Bintu bayan tagama addu’arta ta kalli Hurriya tace in samo maki abinci Hurriya daga mata kai tayi alamar Eh Kallon habiba Bintu tayi tace ina zan samo mata abinci Habiba tace muje in raka ki kitchen ki amso naku abincin to inji Bintu don haka tabi bayan Habiba suna tafiya akan hanya sai habiba ta dan wuce Bintu itakuma Bintu tana ta tunani tana tafiya.

Habiba juyowa tayi baya sai taga Bintu na tafiya kamar wacce zata fadi dawowa tayi ta rike mata hannu gam tace kina tunaninta ko ?kada ki wani damu zaki samu wadanda suka fita komai a masarautar nan wacce zata kula dake kuma ta soki sai ta farayi mata tafiyar tsutaa acikin hannu tace Ko nima idan kika bani dama zan maye maki gurbinta Sai ta tsunkuli Bintu a waist dinta tana kashe mata ido daya itadai Bintu kallon ta kawai takeyi ba tace uffan ba don batasan inda zancen nata ya dosa ba kallon habiba tayi tace muje ko naga lokaci na tafiya Dariya habiba tayi tace gaskiya kinason wannan yar tawalwalar ki nima inason inga ana kula dani haka shiyasa nike kaunar ki don daga gani kinada kulawa ko kukan da kikayi mata kadai ya isa ya nuna hakan

Gaskiya inasonki nagode kawai Bintu tace sannan tace muyi sauri kada tayi bacci murmushi habiba tayi ta rike mata hannu suka fara tafiya da fan dan sauri sauri itadai Bintu tanajin yadda take mata tafiyar tsutsa da hannu har suka kai babban kitchen din da ake dafa ma bayi da kuyangi da masu aiki abinci ba’a wani hantare su ba saboda sanin sune sabbin ma’aikatan da suka zo don suna bukatar Abinci don habiba tayi masu bayani

Plate biyu aka basu cike da tuwo habiba ta amsa ita kuma Bintu tayi tsaye tana kallo ana miko mata plate din Habiba ta kalleta tace ki amsa mana bata fuska Bintu tayi tace ba shinkafa ne? Kallonta mai bada abinci take da mamaki tace ke yar Gidan maysiyata ki amsa idan ba haka in maida ki kwana da yunwa shegiya har MU zakiyi ma iyayi alhalin agidan ku ba lallai kina samun kalar shi ba Habiba ta mintsinota Bintu ba domin ranta ba haka ta amshin abincin saboda tasan ba lalle cewar taci tuwon ba

Suna zuwa suka ga Hurriya ta kara dukunkune wa don ta kara makurewa wuri daya kamar da alama sanyi takeji Bintu tace Hurriya ki tashi ki ci abinci A hankali ta bude fuskarta tana kallon Bintu da take kuka a hankali tace ya akayi kuma?Share Hawayen ta Bintu tayi tace Hurriya don Allah ki ci abinci kada ki ce bazaki ci ba akwai nisa fa inda muka amso kuma kinga baki lafiya tana sakin baki kamar karamar yarinya Dan tsotsar bakinta Hurriya tayi kamar daman sararta ce ta daga mata kai

Cike da jin dadi Bintu ta miko mata tuwon Habiba dai tana kallon ikon Allah kwano ta samu ta debo ruwa sannan taba Hurriya ta wanke Hannunta ta fara cin abincin a hankali ta dan ci ba laifi tanajin ta koshi ta ture plate din ta kalli Bintu ,da sauri ta kara miko mata kwano ta zuba mata ruwa ta wanke hannunta Habiba cike da kaudi da son ta samu shiga tace Hurriya ga magani kisha na ciwon kaine Da zazzabi Hurriya ko kallon inda Habiba take batayi ba don a hankali ta sanya hannuta cikin hijab aljihun wandonta anan ta fito da magungunan da Kumurci ya bata hannun Habiba har lokacin yana tsaye tana bata magani cikin muryar ta da take da alamun rashin lafiya tace Bintu bani Ruwa.

Da sauri Bintu ta bata ruwa ta shanye maganinta kallon habiba Bintu tayi tace kiyi hakuri tana da wuyar sabo ne Amman tana da kirki zaku saba In Sha Allah .Bari in tafi in samo wurin kwana sai Hurriya ta kwanta tare dake,Habiba murmushi tayi cikin yanga tace yi zamanki ki kula da abarki ba mai takura maku nizaje inda nima za’a kula dani,dadi sosai Bintu taji ta farayi mata godiya don tasan idan har Hurriya ta kwanta Habiba ta kwanta kusa da ita kilan za’a iya tashi aga habiba kwance saboda irin dukan da Hurriya zatayi mata kuma itakanta Bintu bazata taba bari ta kwana kasa ba saboda sanyi.

Habiba ta fita tace matsiyata kuma ashe kunsan harka muje zuwa ta nufi dakin Su Hansa’u Aiko tana shigowa sukazo suka zagayeta sukace mata habiba ya bakin nan nagansu tsalatsala guda habiba tayi tace ayiri to ku kwantar da hankalin ku don ba wata wahala da zamusha wannan karan wurin jawo hankalinsu tace ai yan gidan matsiyatan suma duk sun san harka don wadda na bama makwanci ma baki gansu ba kamar zasu cinye juna nan ta kwashe labari ta basu tass dariya suka rinkayi suka ce gobe zasu zo ta nuna masu yan matan suna fata ma Allah ya sanya akawosu dakin Barira duka tana jinsu Amman batace komai ba don shiru tayi.

Bintu kallon Hurriya tayi da ta fara gyangyadi tace ki kwanta ni zan kwanta kasa daga mata kai Hurriya tayi ta kwanta dukun kune cikin hijab dinta bacci ne mai wahala ya dauketa Bintu kam tagumi ta buga tana kallon Hurriya don ta hango wahalar da zatasha a masarautar nan don Hurriya bata durkusa ma wada sadai da alama waddanin sunyi yawa a masarautar kuma wahala zata sha don ko bata durkusa ma ma’aikata ba ai akwai ubannin gidansu da dole suyi masu biyyaya tana fatar dai Allah yasa kada su sha wahala don ganin Hurriya tana wahala tamkar itace take wahalar bazata iya dauka ba.

Murmushi tayi ganin Hurriya ta tsotsi bakinta sai kuma ta turo bakin tana bata fuska alamar shagwaba magana tayi da wani yaren Bintu da take kallonta taji tana magana tana bata fuska da wani yaren da bata taba ji ba
Don tasan yaren dai gaskiya babu kalar shi a Nigeria
Kallon kyaun hallitar fuskarta takeyi yadda tayi ma fuskarta kamar wata baby magana takeyi cike da shagwaba murmushi Bintu tayi tace naga ranar da Hurriya zata daina daure fuskarta tana shagwaba haka tabb akwai ruwa da kankara ranar.

Bintu bacci ta faraji don Haka ta kalli Hurriya ganin ta dukunkune wuri daya kuma ga space nan da yawa don haka ta raba gefenta ta kwanta nesa sosai da ita don kada cikin bacci Hurriya taji ta a kusa da ita ta tureta

Addu’a tayi sannan ta runtse idonta bacci mai cike da gajiya ya dauketa .

Karfe bakwai Bintu ta tashi har lokacin Hurriya bata tashi daga bacci ba ta makara don haka agurguje ta kama ruwa hade da alwala tazo tayi sallah .Tana gama Sallah taje inda taga sauran yan uwanta karime tayi ma magana tayi banza da ita don haka tayi ma uwale magana tace miye akeyi anan uwale tace zamu tafi ne za’a araba mana aiki bata ida magana ba saiga Uwar bayi tazo Kallonsu tayi tace saifa kun kula kubi a hankali kuskure daya a masarautar nan zai iya zamar mutum babban kalubale a rayuwarta, kowa amsa mata yayi sannan suka bi bayanta tafiya sukayi Mai nisa sannan suka iso katon wuri inda mazan dasuka zo duk sunja layi suma layi sukaja suna kallon kyawu da tsarin masarautar da babu wani Abuna more rayuwa da bai wadace ta ba.

Kwance take a lallausar katifa wani Abu dake gefenta kamar wasan yara ya fara kara bude idonta tayi masu cike da bacci kokarin komawa take Amman karar ta hana ta karar wayarta ta hade da karar abunda yaketa wakar yaran tsoki taja tana maganganu da kuma mamakin wani marar sa’a ne ya tada ta daga bacci Amman bari Taga kowaye tana jawo wayar wani call din na kara shigo mata kallon wayar tayi da wani bacin Rai cikin muryar ta maidadi tace oh my God sannan ta ziro dogayen kafafunta wani Abu ta latsa saiga kuyangi guda Biyu sun shigo suna dukar da kansu kasa sannan cike da mugun girmamawa sukace Allah ya taimake ki Allah ya kara maki Nasara Allah yasa wannan Rana tazamar maki Ranar farin ciki da Albarka Batace masu kala ba sai da tagama Shan kamshinta sannan ta kallesu Dukansu ba wanda baisan ma’anar kallon da tayi masu ba don haka da sauri daya daga cikin kuyangar ta shiga toilet dinta ta hada mata ruwa Daidai yadda tasan tana amfani dashi kullum ta zuba mata flowers masu kamshin dadi ta wanke mata brush ta sanya mata macline Mai kamshi ta fito tana durkusawa tace Allah ya taimaki Batatuma Angama

Dayar da take tsaye wacce har ta dauko pink towel dan dora mata towel din tayi sannan ta zame mata rigar tareda rumtse idonta ta yadda kada a samu matsala taga wata siffa ta jikinta cewa tayi ya isa don Haka ta juya Neela ta ida daura towel dinta ta shiga toilet din saida ta farayin brush tadan shafa wasu abubuwa na skin care sannan ta shiga bahon da aka hada mata ruwan wanka lumshe idonta tayi tadan fara wasa da ruwan saida ta dauki mintina kafin tayi applying showe gel dinta mai sanyi dadi ta wanke jikinta tass sannan ta fito
[12/02, 4:53 PM] Khadyn Sp: Masarautar Qamar

By Khadija (KMU)

Page 13&14
Chapter 8 · 0% Book details