← Book details Masarautar Qamar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 24

Sashe 18

Masarautar Qamar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ta daga rigar Hurriya a firgice tace masarautar Heral Inna lillah wa'ina ilahi raji'un ta ambata tana kallon zanen tatoo din Hurriya dake kwance agadon kafadarta ta baya kenan itace yarinyar da kusan shekara biyar dasu ka wuce akazo ana nema don kusan ko wace babbar masarautar dake duniya anje don harda masarautar Qamar akazo tare da alkawarin duk wanda ya samota akwai gagarumar kyautar da za'ayi mashi don dashi da zuri'ar shi hatta tattaba kunnenshi sun gama talauci saboda irin zunzurutun abinda aka alkawarta sannan kuma idan nameji ne zai aureta tare da nadashi sarautar kasar baki daya

Shiru tayi tana hasko Labarin irin masarautar Heral da ake basu irin mulkin da akeyi da irin tarin arziki da daular dake shimfide a cikin kasar don masarautar na daya daga cikin jerin masarautar duniya da ake ji dasu

Shiru tayi tana tunanin duhun da tagani tattare da Hurriya wanda ba'a masarautar Qamar kadai ya kare ba hatta masarautar Heral din idan ta koma zata fuskanci kalubalen da kilan zai iya sanadin rayuwarta don ko masarautar Qamar din Qalubalene da zai iya sanadin rayuwarta ko kuma ya tarwatsa mata duk wani farin ciki na rayuwarta wanda yarinyar ga dukkan alama ta dade ba farin ciki rayuwarta

Inna hanne ta sauke ajiyar zuciya tana kallon kyakyawar fuskarta tana nazarin dalilin da aljanunta sukayi nuna mata bayanin Hurriya yarinyar abar tausayi ce saboda zagaye take da makiya  Amman In Sha Allah zata taimaketa da addu'oi Sosai da azkar masu matukar muhimmanci saboda tasan tsafin da akeyi a masarautar Qamar

Bintu ce ta shigo aguje da ruwan zafi sannan ta ruga aiken da inna hanne tayi mata don amso mata magungunan hausa Bintu bata wani dauki lokaci ba sai gata da magungunan

Kallon Bintu baba hanne tayi tace ta dan fita Bintu batayi musu ba ta basu wuri

Maganin ta hada mata na lamoniya hade da sanyi sannan ta bude bakinta ahankali ta shiga bata don ko motsi batayi rabin maganin na shiga rabi na fita baba hanne kallonta take cike da tausayinta don itadai tunda ta taso rayuwarta A daji kuma babansu magani yake badawa itama har ta gaje shi to bata taba cin karo da makamanciyar lamoniya irin wannan ba
Bayan tagama bata magani ta samu farin tsumma mai kyau sannan ta shiga gasa Hurriya da ruwan zafin

Tana dora hannnunta ajikin Hurriya ta zabura
Haka ta rinkayi da ta taba mata jiki sai ta zabura saida ta taimaka mata sosai wurin ganin gasa jikinta da magungunan gargajiya

Wasba ce zaune à inda Hurriya tazauna jiya tayi wanki tana wasa da karamin icce wanda ke nuni da kamar Hurriya take jira

Kallon hanyar da ta biyo jiya tayi saidai bata ga ko mai kama da ita ba

Bata rai tayi tana turo baki ta tashi ta koma cikin gidansu

Hurriya shiru shiru bata tashi ba saaidai Bintu na zagaye da ita kamar wacce zata gudu don har tayo aikinta ta dawo
Inna hanne ta dade a wurin tana kula da ita kafin ta koma kitchen domin ayyukanta  saida Inna hanne tagama ayyukanta sannan ta dawo inda Hurriya take kwance hannunta rike da kofin shayi cikin hikima ta shiga zuba ma Hurriya ruwan shayin duk da rabi ya shiga rabi ya fito haka abun yake

Bayan tagama bata shayin tayi tagumi tana tunanin ikon Allah tunda take bata taba tunanin ko a rayuwarta zata iya zuwa masarautar Heral ba saboda sai an ketare kasashe shin bama wannan ba itadin wacece ba kowa bace face ma'aikaciya a masarautar Qamar sai kuma Qaddara da ta hadata da long lost princess din Qasar

Saidai Tana Addu'a Allah yabata ikon taimokon yar marainiyar yarinyar nan Allah kada ya sanya san zuciya ya debeta ta tona mata asiri

Su kuma su barira zatayi maganinsu Lallai da ace sun san wacece ita da ko hanya daya basu isa su hada ba

Don duk yan masarautar Qamar tafi karfinsu hatta sarkin idan tagadama tace a sauke shi daga kan mulki to tabbas babu tantama za'a sauke shi don masarautar su tana mulkin masarautoci da yawa a afirca so masarautar Qamar na ciki

Ta dade tana tunanin sannan ta tashi ta fita tana fita saiga Bintu na shigowa dan sauke ajiyar zuciya tayi sannan tace ki kula da ita don Allah.

Abun kamar wasa Amman har yanzu Hurriya bata bude idonta ba har anyi wata daya da sati daya

Su barira suna sane da halin da Hurriya take ciki don har anfara yada jita jita su barira sunyi kisan kai saidai da yake su din suna da power sosai ba wanda ya tarbesu da maganar

Saukin Hurriya daya data samu Inna hanne tayi bake bake ganin taji sauki don lallabata take kamar kwai kowa yana mamakin dalilin don baba hanne bata da irin wannan kirkin da take nuna ma Hurriya don itama ba Ruwanta da kowa

Bintu kam ta zuge ta rame tass kallo daya zakayi mata kasan cewar tana cikin matsinaciyar damuwa .

Imad kam shima ya shiga damuwar rashin ganin mai aikin nan don Hamdan da amrah duk sun gigita su don yanzu a chamber shi suke kwana Neela kam batasan mi zatace ba a al-amarin don tun tana kushe su yanzu ita kanta burinta da fatanta a samo Hurriya

Imad yafi kowa damuwa don kowa kallo yake yasan inda take don yanzu haka suna tare da Ammar ne a balcony Ammar ya kalleshi yace twin Imad kallonshi yayi yana daga mashi kai dafashi Ammar yayi yace nifa na rasa gane mike faruwa wacece wannan yarinyar miye hadinta da Hamdan da Amrah mi yasa suke sonta har haka yaran da basu damu da kowa ba rayuwarsu Amman sun damu da ita fiye da yadda suka damu damu
Shiru Imad yayi yana nazarin maganar saidai baisan yadda zai hada komai ya bashi ma'ana ba don haka ba tare da karayin wani tunanin ba yace Allah yasa lafiya dai

Shiru Ammar yayi sannan yace ka tambayi ma'aikatan ko lafiya? Girgiza kai yayi yace mashi Aa

Shigowar Liya ne ya sanya  Dukansu suka juya suna kallonta cikin jumpsuit din Rimowa wanda sukayi mata kyau sosai zuwa tayi gefen imad ta rike mashi hannu tace na samo labarin maid dinka ka kwantar da hankalin ka

Ammar ne ya zagayo ya rike ma Liya hannu yace lafiya miye ya faru shima rike mashi hannu tayi , murmushi tayi sannan ta gyara zama tace kwantar da hankalin ka tana cikin masarautar Qamar

A hankali ta zayyane masu duk abinda aka gaya mata ance bata lafiya har yanzu batasan inda kanta yake ba tundaga ranar da ta ture Amrah

Shiru sukayi suna kallon yadda takeyi masu bayani har takai karshe ba wanda yace kala Ammar ne yace wani irin ciwo take Liya tace bansaniba Imad baice komai ba ya tashi ya bar masu wurin ba wanda ya damu da tashin da yayi saboda susan halinshi na miskilanci

Hamdan kam ko da yagama jin bayanin da Neela da Liya suka gama mashi sai ya fara sauke ajiyar zuciya kallonshi suka rinkayi da mamaki don abinda basu taba gani bane

Amrah ce ta shigo jikinta sanye da wani crazy jeans sai yar top kunnenta sakale da AirPod Dukansu kallon yar autarsu da damuwa ta bayyana a fuskarta sukayi Hamdan ne ya tashi yaje saitin da take sannan ya zare AirPod din kallon shi tayi ta dage mashi gira guda daya alamun lafiya

Cikin muryar shi mai dadi yace I found her Amrah kallonshi take da alamar bata gane nufinshi ba murmushi yayi mata sannan yace the beautiful young lady bude hakoranta tayi tana kallon hakimi tace like seriously daga mata kai kawai yayi Amrah zuwa tayi ta rungume Hamdan tana mai tsananin murna

Inna Hanne zaune tayi tana kallon Hurriya wadda fuskarta tayi fayau gashin kanta da girarta kwance sai bakinta da yayi pink ta riga ta gama sawa a ranta idan har Hurriya ta cike wata biyu bata samu sauki ba to zataje kauyensu ta taho da yayanta domin ya dubata

Tausayin yarinyar takeji sosai don yarinya mai gata kamarta yaushe ne Zata jira wani maganin gargajiya saidai da yanzu tana asibiti kasar waje Maganar Bintu da taji ya sanya ta dawo daga dogon tunanin da ta shiga ta kalleta sannan tace kindai ci abinci ko? Daga mata kai tayi

Wasba kije innani na kira wani karamin yaro ya gaya mata dauke kanta tayi daga kallonshi hawaye na zuba a idonta yau tasan dukan tsiya zataci bare tun dazu innani take kiranta Amman taki zuwa ta tsaya tana duba hanya ko zataga inda Hurriya zata bullo

Tashi tayi tana kuka tana share majina har tazo dan karamin gidansu dake cikin masarautar Qamar

Aiko tana shigowa innani ta rufeta da duka tana zaginta shegiya daga gidan ubanwa kike yar iska matsiyaciya tsintarciyar mage kin raina mutane ko ta cigaba da dukanta ba tausayi bare tausayawa har saida taga tana Neman daina numfashi ta daina dukanta.

Hurriya a hankali ta fara motsa yatsunta kafin ta bude idanunta Bintu dake zaune ta saki tagumi jin motsin da tayi daga Hurriya ya sanya ta kalleta cikin mamaki taga idon Hurriya bude suna kallonta da wani irin jin dadi da murna Bintu ta nufota girgiza mata kai Hurriya tayi tana mata kallon kada ki sake ki tabani

Daga mata kai Bintu tayi tana ta hamdala Hurriya kuma kallonta kawai take yadda take murna

Shiru Hurriya tayi tana tunanin wadanda suka sanyata jinya inda ace a masarautar Heral ne to babu abinda zai hana su bakunci lahira don abinda suka aikata hukuncinshi kisa ne how dare they messed with Princess wani evil smirk tayi don ita she’s someone that doesn’t take nonsense from anybody whether she’s princess or slave tasan sai tayi maganinsu ita batajira wani ya kwatar mata yanci da kanta da hannunta zata kwatar ma kanta yanci
Chapter 18 · 0% Book details