← Book details Masarautar Mu Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 19

Sashe 8

Masarautar Mu Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rapist, at your home Oga!.
Abinda kawai ya gaya wa Sageer ke nan. Ya na so ya shiga ya taimaki Saade yana tsoron ko Ziyad na dauke da makami. Shi kam Uche matsoraci ne na karshe.
Duk da raunin da ta ji masa da fitila bai dame shi ba, ya dafe wajen da fitilar ta huda masa wanda tulin gashin kansa ya rufe shi. Sai jini da ke bulbulowa ta wajen, ya mike da mugun zafin nama ya dauke ta da mari haggu da dama. Saade ta nemi jinta da ganinta na wucin gadi ta rasa. Dr. Ziyad ya yi amfani da wannan damar ya fincike tawul din da ke jikinta
Saade ta sake yunkurawa tana ihu, ya sake sanya kafa ya tadiye ta, Uche yana daga bayan tagar dakin yana ta jera wa Yarima kira, ga shi ba shi da lambar police ko security din makarantar cikin wayar sa, wata zuciyar ta ce ya dauki dutse ya shiga ya kwada wa Dr. Ziyad, wata zuciyar ta hana shi, in ya zo da tsautsayi ya mutu shi ma kashe shi za a yi, a kan matar da ba tasa ba ai ya san shima maigidan nasa yana danawa a gidan Ziyad din, abinda suke yi ne tare yau aka yi masa har cikin dakin auren sa..
Yana wannan sake-saken jikin sa yana bari sai ganin hancin motar Yarima ferrariya yi ya shigo gidan da wani irin mugun gudu, kasa tsayar da motar ya yi sai da ta daki daya dalleliyar motar da ke fake a gefe, sannan ta tsaya cikin kudurar Ubangiji, bayan ya take birkin tsayar da mota.
Da gudu ya fito, jikinsa ba inda ba ya tsuma, hatta jijiyoyin kansa da makwallatonsa sun mimmike. Tsabar rudewa ya rasa ina ya jefa mukullin gidan, ga shi ya kulle ta ta waje. SaiUche yayi masa nuni da kofar kitchen ta baya. A lokacin Uche ya zargi ta kofar kitchen Dr. Ziyad ya shigo.
A guje Yareema Sageer ya danna kai gidansa, don tun daga Kitchen za ka fara jiyo ihun da Saade ke ta kurmawatana ambaton sunan Sageer da neman taimakon Allah.
A falo ya tsaya cikin gigita mara misaltuwa, yana son tantance daga inda ihun Saade ke fitowa. Daga karshe ya gane dakin barcin su ne. Tuni Ziyad ya kai ta kasa, yana ta kicin-kicin cire jallabiyyar jikinsa zai haike mata.. domin ya gama galabaitata da duka karfin kokawar ta ya kare, sai ambaton sunan Allah take hawaye masu zafi na kwaranya, ya yi nasarar cirewar kenan ya ji an ba shi (one blow one die) daga keyarsa.
Da ma ga shi jiki ba jiki ba, siriri ne sai tsayi kamar falwaya, sai da ya tuntsira daga kutufo dayada Dr. Sageer ya yi masa, Yareema ya bi shi ya dinga buga kansa da bango yana naushin hancinsa da bakinsa. Saade ta yi amfani da wannan damar ta ja jiki da rarrafe ta shige toilet dinta ta rufe.
Ta kifa kai jikin jacuzzi tana girza wani irin kuka jikinta yana ta rawa da kakkarwa, wanda sautin sa yake fitowa tun daga karkashin zuciyarta.

Me wannan mutumin ko aljanin zata ce ya zo ya yi mata? Kisa ko me??

O.k tunda ta ganshi ya tube wando ya kuma tsiraitata to raping dinta ya zo yi. Rape, rape, rape dai da ta ke jin labari!!!

Wani mugun tsoro ya shige ta, ta ji ba abin da ta ke so a halin yanzu ban da ta bude ido ta ganta a gaban uwarta.
Ba ta san ya suka kare ba. Ta kasa fitowa daga toilet. Banda tsuma ba abinda jikin ta ke yi ta dunkule a wuri guda a gefen kwamin wanka. Sanyi yana kada ta.
Ta dai ji karar shigowar motar security din Nigerian Turkish Nile University. Gabadaya kuma suka shiga motoci suka tafi har Yareema domin su yi report karkashin hukuma. Har Uche aka tafi, don shi ne zai bada shaidar komai.
Uche ya fada wa kwamishinan yan sanda duk abin da ya sani, cewa yana shigar da cefane ya kai wasu ya koma don ya debo wasu, sai ya tuna wayar sa ya barota a baskwata tana caji ya je don ya dauko, da wannan damar Dr. Ziyad ya yi amfani ya shigo gidan ta kofar kitchen. Ihun Saade da ya jiyo da lekawa da ya yi ta taga ya gansu suna dauki ba dadi.
Kiran Yarima da ya yi da daya makwabcinsu Dr. Wole da ya kira universitysecurity bayan shigowar Yarima.
Lokacin da hukuma ta matsawa Dr. Ziyad kan ya amsa laifinsa kada ya wahalar da hukuma, budar bakin sa sai ya ce shi ma Yarima yana neman mata, komai suke yi ai tare suke yi, don haka bai kamata ya kawo zancen nan ga hukuma ba tunda abin da yake yi wa matan wasu ne shi ma aka yi wa tasa..kuma sharing matan suke yi.

Yarima bai taba jin nadamar aikata zina a tsayin rayuwar sa irin ta yau ba. Lallai Ubangiji ya yi gaskiya, ita zina bashi ce, kuma bibiyar mai ita take yi, in dai ka yi ta a rayuwarka ko ba a yi da dan ka ba zaa yi da matarka ko kanwarka.
Kuka riris Yareema Sageer ke yi akan bencin kwamishinan yan sanda, ya kuma yarda gaskiya Ziyad ya fada. Amma shi tunda yake bai taba neman matar kowa ba sai watsattsun bisa titi, to why matar sa? Amma da gaske ya taba raping yar wani duk da baiwa ce tun a shekarun tashen balagarsa. Amma ai an yi masa hukuncin addini, me ya sa tun bayan nan bai daina ba? Sai ma hakan ya bude shafin rayuwar kaico a gare shi? Sai ya ji koma me Ziyad ya yi masa kamun Allah ne. Ubangiji Subhana yayi gaskiya da yace (in kayi zina da yar wani to hakika zaa yi da yar ka ko kanwar ka ko matar ka.).
Ubangiji Yana kyale mu mu yi ta saba masa, ranar da zai yi mana talala sai ya yi mana ita a kan abin da muka fi so fiye da komai a rayuwarmu.
Yana son Saade, yana kishinta yadda harshe ba zai iya bayyanawa ba. Dr. Ziyad ya keta mata haddi, amma abin nan da Ziyad ya fada sai ya ji ba shi da sauran guts na neman hakki a kansa. In har ya yarda da fadar Ubangiji a kan zina. To ya yarda kawai kamun Allah ne tun a gidan duniya. Wani kamun sai an je lahira.
Ya yi kukansa mai isar sa a gaban Ziyad da kwamishinan yan sanda, sannan ya share hawayen sa ya mike yace a sake shi, ya janye karar sa, amma yana so hukuma tayi masa iyaka da Dr. Ziyad ba shi ba shi har abada! Kuma daga yau ya ajiye aiki a jamiarsu ta Turkawa (Nigerian Turkish Nile University).

Yana tuki a kan hanyarsa ta komawa gida yana hawaye. Hawayen nadamar duk abin da ya aikata a baya. Shi kansa ya san talala ce Allah ya yi masa da soyayyar Saade, soyayyar da ko a labarun hikaya bai taba jin wadda ta yi daidai da wadda yake yi wa Saadatu yar Bilkisu ba. Yau aibunsa ya janyo an shiga gonarsa an keta haddin sa.
Ya shigar da motar maadanarta, sannan cikin sanyin jiki ya kashe ta ya fito, kayan jikinsa duk sun baci da jinin hancin Dr. Ziyad, da sanyin jikin dai ya bude kofar falon don bai san a halin da zai riski Saadatu ba.
Falon yana nan yadda yake tun safe, kofar dakin barcinsu inda abun ya faru har yanzu a bude, ya leka can bai ganta ba sai ya fito zuwa nata dakin.
Tana kwance a kan gadonta tana kallon ceiling hawaye na bi ta gefen idonta. Fuskarta duk ta kumbura ta yi jazur. Ba ta taba shiga tashin hankali a rayuwarta irin yau ba. Ba ta taba ganin abin da ya tsorata ya firgitata tsananin firgitawa irin yau ba da aka yi attempting raping dinta da tsakar rana har dakin aurenta.
Dr. Sageer Yusuf, ya nufi Saadatu da sassarfa, ya dago ta daga kwanciyar da ta yi ya rungume a kirjinsa. Ga mamakin Saade shi ma kukan yake yi. Cikin wata kassararriyar murya tamkar ba tasa ba yake magana.
Saadatu did hedid he succeed???
Ya kasa karasawa sabida tsoron abin da zai fada din.
Ta runtse idonta ta kankame Sageer jikinta yana rawa.
No he didnt.
Wata irin kakkarfar ajiyar zuciya Yareema Sageer ya saki, wadda bai taba yin irinta a tsayin rayuwarsa ba.
Ko an yi ko ba a yi ba, ya ji abin da miji ko uba yake ji in an yi zina da yarsa ko matarsa. A fili ya ke furta, ASTAGFIRULLAH WAATUBU ILAIHI.
Saadatu ta fashe da kuka tana rokon Yareema ya maida ta Askira, ita ta hakura da karatun. Yareema ya ja lallausan duvet ya lullube su, ya kwantar da Saade saman kirjinsa.
Ki kwantar da hankalinki don Allah Saadatu. Aikin ma gabadaya na aje. Alfarma daya nake nema kada ki fadawa Fulani ko Maimartaba wannan kaddarar da ta faru, ni kuma duk abin da ki ke so zan yi miki, I promised.
Saade ta ce, In ban fada ba za ka maida ni Askira gobe?
Ya ce, Insha Allahu za mu koma gabadayan mu, amma sai na mika resignation letter, ki ba ni kwanaki uku.
Chapter 8 · 0% Book details