← Book details Masarautar Mu Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 19

Sashe 5

Masarautar Mu Part 4 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Har gaban department din su Saade ya shiga da motar, inda babu mai wucewa sai staff only. Yana tsayawa ta bude kofar za ta fice, cike da dokin shiga aji, ta yi kewar karatunta sosai, ta san abubuwa da yawa sun wuce ta, amma ta tabbata Said zai dora mata komai.
Yarima ya rike hannunta tana shirin fita.
Haah! Saadatu har murna ki ke zan tafi in ba ki fili ko?
Ya fada da marainiyar murya, har cikin ransa yake jin rabuwar nan da zai yi da Saade har tsayin kwanaki uku. Kwarai bai yi karya ba tana murna da tafiyar sa ta wani fannin ko don kwarzaba irin tasa, ta san za ta samu hutu da nutsuwa na dan lokaci ta yi karatu sosai na abin da aka wuce ta.
Amma in ta tuna da matarsa zai tafi sai ta ji gara ya zauna ya yi tumurmusar nata da ya tafi wajen mai jan kunnen tasa. Amma ko kashe ta zaa yi ba za ta iya gaya wa Yareema tunaninta ba. Ta san kuma da gaske ne kamar yadda ya ce matarsa ma na da hakki a kansa, ba don ita kadai aka halicce shi ba.
Ba ta ankara ba ta ji hawaye sun zubo mata. A hankali ta ce,
Ni ba murna nake ba, hasali ma I will really miss you.
Cikin jin dadin kalaman ta Yareema ya mika mata hanky dinsa ya ce, To share hawayen, ki bar wayarki a kunne, zuwa asubahi in mun sauka zan kira ki. Me zan sayo miki? Kasar Korea ta Kudu za mu je ni da Sultana.
Ta kasa sabawa da ambaton Sultana da yake yi, don ji ta ke kamar ya fi kowa iya fadar sunan. Wasu hawaye suka sake zubowa, wadanda ba ta san dalilinsu ba. Yareema ya sa hannunsa yana shafe mata hawayen da tafukansa sai a idanun Said da ke fitowa daga lecture hall. Dr. sageer ya gan shi ta karshen idon sa amma ita Saade bata lura da shi ba, da gayya ya kara rungumo Saade yana mata magana cikin kunnen ta.
Zan iya tafiya?
Ta tambaye shi bayan ya gama dauke mata hawayen fuskarta da tafukan hannun sa.
...Only if you give me a farewell kiss (za ki tafi ne only in kin ba ni sumbar bankwana).
Wani irin murmushi ne ya subuce a siraran lebbanta, wanda Said bai taba gani a tare da ita ba. Ji ya yi kafafunsa na neman kasa daukarsa ya juya ya koma cikin aji da mugun sauri. Har yana cin tuntube a bakin kofa saura kadan ya kifa.
Prince ka bar ni in tafi aji, ka ga malam ya shiga. Kuma nan kan hanya ne, mutane suna iya hango mu ko daga lecture hallne.
Kin yi alkawarin in na dawo komai zai canza Saadatu? Za ki daina fushi da ni, za ki dinga gaya min duka bacin ranki? Zamu shimfida sabuwar rayuwa ta amana, soyayya da fahimtar juna?
Da sauri Saade ta gyada kai.
Yareema ya ratsa yatsunshi biyu cikin nata ya matse su sosai sannan ya sake su a hankali. Ta kasa dago ido ta dube shi, domin wata irin soyayyar Sageer da ta ji tana shigarta tana mamayeta a hankali. Ta bude kofar motar ta fice rungume da folder dinta.
Ba ta waiwayo ba sai da ta kai kofar lecture hall dinsu.
Har yanzu yana nan a inda ta bar shi, kanshi kwance bisa sitiyari, bai dauke ido a kanta ba. Ta sakar masa lallausar murmushi, sannan ta juya ta shige aji.
Yau sai ta ji ta kasa zuwa ta zauna kusa da Said yadda suka saba, wanda ya tattara hankalinsa duka ya dora a kanta tana shigowa. Ta dauke kai ta nemi gefen wata kabila mace ta zauna.
Mai miji kamar Yareema Sageer, ji ta yi ta daina son ganin kowanne namiji a duniya sai shi. Tafiyar da ya yi kuma tamkar ya tafi tare da ruhin ta ne. Gabadaya ta rasa kuzarinta da walwalarta.
Malamin Baireshe ne, yana ta bayani a kan applied chemistry, Saadatu ba ta jin muryar kowa sai ta mijinta Yareema Sageer cikin kunnuwanta yana rada mata tausasan kalamansa. Har ya yi awanni biyunsa ya gama ko alifun ba ta rubuta ba.
Said daga inda yake zaune ban da satar kallonta ba abin da yake yi, yana yi yana rubutu, ta yi wani mugun kyau, ta yi fresh da ita. Yana ta mamakin abin da idanunsa suka gane masa yana faruwa cikin motar Dr. Sageer Askira da kanwar tasa Saadatu.
Ba ta taba yin kama da mutanen banza ba, yarinya ce mai tarbiyyar babban gida, amma anya abin da ya gani cikin idanunsu ita da Yayanta Dr. Askira bai yi kama da mashahuriyar soyayya ba? Soyayyar ma irin wadda ba ta taba faruwa sai da physical relationship a tsakani.
Bayan fitar Malamin, Saade dole ta taso ta cimma Said a mazauninsa don ya ba ta notes din da ya wuce ta. Ta yi masa sallama, ta ce,
Said kwana biyu?
Ya daga ido ya dube ta a hankali, sai kuma ya dauke kai. Mamaki ya kama Saade.
Said ba ka gane ni ba ne?
Kawai sai ya tattara takardunsa ya bar gurin.
Saade mamaki ya kashe ta a tsaye, ta bi bayansa yana fita daga theater din.
Said! Said!! Ta daga murya tana kwala masa kira.
Juyowa ya yi ya jefe ta da wani mugun kallo, sannan ya dakata har ta cimmasa. Suka yi kallon-kallo na yan sakanni kafin Saade ta tuna cewa ita yanzu matar aure ce, ta yi saurin kawar da idonta.
What happened Said? Ina magana kamar ba ka san ni ba?
Said ya rasa me zai ce mata, idanunsa sun kada sun yi jazir don kishi. Saade ta soma shaka, don ta tsani wulakanci. Ta kankance ido ta ce,
In dai don notes dinka ne, ka rike abunka kada Allah ya sa ka ba ni, kada ka manta kanwar Dr. Sageer ce ni, zai karba min a hannun kowanne malami.
Said ya yi murmushi mai ciwo, ya ce, Kwarai, na shaida hakan tunda kuwa kina ba shi reward a cikin mota, abin da ya fi notes ma zai karba miki.
Kan Saade ya kulle, ta ce,
Me ka ke nufi?
Ya yi mata wani irin kallo zuciyarsa na zabalbala, ya ce.
Kin ba ni mamaki Saadatu, ina miki kallon yarinyar kirki, mai hankali da tarbiyya, yar manyan mutane, yar babban gida, amma ashe kallon kitse nake wa rogo, duk abin da ya faru cikin motar da ta kawo ki tsakanin ki da wanda ki ka kira Yayanki na gani.
Abin da ban sani ba shi ne, da gaske biological brother dinki ne ku ke aikata wannan assha?
Saade ta kai yatsu ta toshe kunnuwanta ta juya da sauri ta bar wurin. Ba ta san me za ta ce masa ba, tunda ashe duk amincin da ke tsakaninsu ba zai iya shaidarta ba, zai iya yi mata mummunan zargi irin wannan.
Ranta ya yi mugun baci, har ta ji ba ta bukatar fayyace masa gaskiyar ko wane ne Dr. Sageer a gare ta a yanzu. Ya je ya yi ta yi mata kallon yar shan minti a mota, damuwarsa ce. Daga yau ba za ta kuma shiga shirginsa ba.
Ba su gama lectures ba sai yamma lis. Direbanta ya zo ya kai ta gida bisa umarnin Yareema. Ta fito daga motar goye da jakarta irinta yan sakandire (school bag), ta gaya masa gobe karfe takwas zai zo ya shiga da ita.
Uche ta taras ya yo cefane himili guda yana shiga da su kitchen. Ta yi masa sannu, sannan ta ce daga yau ta hutashe shi girkin gidan, aikinsa ya koma share-share da goge-goge kafin ta dawo makaranta ya yi duk abin da zai yi ya gama ya wuce baskwata. Sai kuma cefane da aike da zai dinga yo wa lokaci zuwa lokaci.
A ransa Uche ya ce, Tunda dai ba za ki sa a kore ni ba ai shi ke nan. A fili kuma ya ce, Yes Ma!. Don haka yana gama jera mata komai a firji da store ya bi ta kofar baya ya koma baskwata ya ci gaba da aikin fulawoyin gidan.
Wanka ta yi, sannan tayi sallar magriba ta yi lazimi zuwa isha. Ta kawo sallar isha da shafaI da wutiri, sannan ta roki Allah ya sauki Yareema lafiya, Ya kuma dawo mata da shi lafiya. Ta koma kitchen ta hau aiki, ta gyara komai zuwa yadda ta ke so, ta ke buri tuntuni kitchen din ya kasance (da a ce nata ne).
To shi Allah buwayi ne, gagara misali. Abin da ba ka taba zato ba ko tsammani ya riga ya rubuta shi cikin littafin kaddarorinka.
Noodles kawai ta dafa guda daya ta shige daki, ta ci ta koshi sannan ta yi shirin kwanciya.
Da asubah tana idar da sallah ta janyo wayarta da ta saka a caji ta kunna. Wayar ta cika taf da caji. Tana kunnawa kamar jira yake, sai ga kira daga international number.
Saade na amsawa, tana jin muryar Yareema sai ta saka masa kuka.
Prince yaushe za ka dawo? Jiya da kyar na yi barci, tsoro nake ji.
Hankalinsa gabadaya ya tattara ya mika mata, ya ce, Ki yi hakuri Saadatu, mun sauka lafiya on transit a Amsterdam, yanzu za mu jau jirgin South Korea, insha Allahu jibi i-yanzu muna tare. Mun fara shirin tarbar mai sunan Maimartaba, da ni ki ke so ya yi kama ko da ke?
Ba ta san sanda ta yi murmushi ba, ga hawaye shabe-shabe a idon ta.
Ina gaida Aunty Sultana, ka gaya mata ni ban ce ina son mijinta ba aka aura min, ta daina fushi da ni.
Yareema ya yi ajiyar zuciya, ya ce, In ki ka ce haka ba ki yi min adalci ba Saadatu, dukkanmu mun dade muna son juna, ba mu gane hakan ba ne har sai da Maimartaba ya ankarar da mu. In kuma da gaske ba ki sona din ne Saadatu, to gata ki gaya mata da bakinki.
Ta girgiza kai da sauri kamar yana gabanta, ta ce, Yaya Yareema!!! (In exclamation).
Ya ce, Yes, ki gaya mata da bakinki, sannan ne zan yarda cewa ba kya son nawa.
Murmushi ya subuce mata, ta kawar da zancen da cewa.
Karatu ya wuce ni da yawa, an yi min fintinkau, in ka dawo za ka koya min?
Ya ce, Karatun namu ai kala-kala ne, wanne daga ciki?
Ba ta gane hausarsa ba don haka ta ce, Courses din Applied Chemistry, inorganic, organic and petrochemistry. Tunda kai ka jawo aka wuce ni. Ta fada cikin shagwabar da ba ta san ta yi ba. Dr. Sageer ya yi ajiyar zuciya.
Anya Saadatu za ki bar ni in yi kwanaki biyun nan? Gabadaya kin rikita min lissafi, na kasa zama lafiya cikin nutsuwa tun barowata makarantarku. Ke kawai nake son gani, ke kawai nake son ji a jikina.
Ta kai tafin hannunta ta rufe ido kamar Yareema na ganinta, sannan ta ce, Kada in shiga lokacin Aunty Sultana. Prince sai ka dawo.
Ta yi maza ta kashe wayar ta koma ta jingina bayanta jikin allon gado, ta lumshe idanunta. Ba abin da ta ke son gani a daidai wannan lokacin sai Yareema Sageer.
Chapter 5 · 0% Book details