← Book details Masarautar Mu Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 19

Sashe 18

Masarautar Mu Part 4 Complete Hausa Novel · about 6 min read

ANKARA
Basu bar Ankara ba sai da Saade ta shiga watan haihuwar ta bayan bikin yaye su (convocation) na kammala digiri akan (Pure&Applied Chemistry) inda Saadatu Hashim Askira ta fiddo kwalin ta mai daraja ta farko. In aka duba kuma da idon basira duka nasarar karatun Saade sai ace hobbasar Yarima Sageer ne, miji mai cin tudu ukku a rayuwar Saade; malami kuma masoyi, ta wani fannin Yayan da bata da shi, kuma wanda babu kamar sa a rayuwar ta.
Alkawarin da ya daukar wa Mai Askira ya cika shi, ya rike Saade da dukkan amana, ya rike ta da dukkan kauna da soyayya haka ya zama mijin marainiya.
Ya gama appliedresearches din da ya je yi, yayi nasarar rubuta littafai muhimmai akan fannin sa. Wadanda suka bashi damar zama Farfesa, domin bayan dawowar su Askira da dan lokaci kalilan ya kama aiki da jamiar Maiduguri (UNIMAID) wannan ne dalilin komawar rayuwar su garin su Askira bakidaya, ko ya je Maiduguri baya wuce kwanaki biyu ko uku zai shigo Askira. Har gobe yana nan akan burin sa na kafa privateuniversity a garin Askira kuma yana cigaba da fafatukar hakan.
Saade da ta tashi haihuwa sai ga kyautar Allah ta yaya mata har guda biyu. Wadanda suka ci sunan Ya Gumsu da Fulani Bilkisu. Soyayya ta karshe yan biyu (amaren Askirama) yadda ake kiran su cikin gidan sun gan ta wajen Mai Askira. Dr. Sagir kuwamaida Sahlah da Suhailah ciki ne kawai ba ya yi sabida soyayya.
Ya Gumsu ta dade da samun lafiya kuma tuni ta kama girman ta ta kuma daina adawa da Fulani Bilkisu. Ta yarda da duk abinda Askirama ke fada a kan ta. Sun hada kai sun samarwa Mai Askira madauwamin kwanciyar hankali a shekarun tsufan sa.
Yayin da Sahlah da Suhailah suka zamo masu debe masa kewa don kullum sai ya fita da su fada ya ajiye a hagu da daman sasuna kiriniyar su yana gudanar da alamuran mulkin sa.
Ko kusa babu wanda ya yi mummunan furuci akan haihuwar yaya mata da Saade tayi a masarautar bakidaya, sabida yara ne masu shiga rai, da ko baka yi niyyar daukar su ba sai sun ja hankalin ka ka dauke su. Jinin BAGGARA ne dana BABARBARE ya hadu ya bada wadannan twins masu tsananin kyau da shiga zuci. In har ba UNIMAID zai tafi ba zaka same shi tare da yan biyun sa a cinyar sa ko a gefen sa ko a hannun sa. Prof. Sageer Yusuf Askira.
******

MURFI
Nakuda take tamkar bazata tashi ba, nakuda ce da ko haihuwar yan biyu bata yi mai zafin ta ba. Ta riga ta fidda rai da rayuwa, tana kwance ne a cinyoyin Yarima Sageer ta hada gumi kashirban, gashin kanta ya watsu bisa jikin sa. Idan na taba cutar da kai a tsayin zaman mu ka yafe min Baban Suhailah, ta fanni na baka yi min komai ba sai alheri da soyayya Yaya Yareema. Idan na mutu,kada ka kara aure zan yi ta jiran ka aljannah har ka iso, ka ji? Ka cewa Fulani ta yafe min its not easy being a mother! Na kara daraja ta fiye da baya, na kara son ta fiye da wanda nake mata, na kara ganin kimar ta da martabar ta.. na so in yi tsawon rai in biya mata Hajji Allah bai yi ba..
Sai ga wani uban nishi ya biyo baya, Sageer ya dauka tafiyar kenan! Sabida haka numfashin sa ya soma kokarin barin kirjin saamma sai me? Kafin ya bude ido sai ya ji nurse Aisha na cewa cikin farin ciki.

HERE COMES OUR PRINCE!
Sai kuma baby data taro ya callara kuka wanda ba kwanyar Yarima kadai ya shiga ba har da ta unconscious Saade, kuma kukan ne ya maido ta a hayyacin ta.
Nurse Aisha ta nade jaririn a tawul bayan ta goge masa jiki daman zaitun (olive oil) ta zo ta dora shi a ruwan cikin Saade wadda ke kwance kane-kane a jikin Yarima tana mai kallon komai kamar cikin mafarki.
Yau itace da haihuwar namijin finally. Bayan ta fidda rai, domin kuwa bayan Twins sai da ta kara wasu setin twins din again duka mata, wadanda suka ci suna Rahimah da Hannatu. Sai yau haihuwa ta uku taji ana kiran Prince.
A hankali ta lumshe idon ta da wahala tasa duk suka zurma ciki suka kankance, ta bude su akan kaykkyawan Babyn ta wanda bata ga fuskar kowa a kan fuskar sa ba sai Ahmad autan su Yarima, wato dai daYa Gumsu yake kama. Hakika La taqnadou min rahmatullah. Allah yana jinkirta maka abunda kake so zuwa lokacin da ya ga yafidacewa ya baka, abin so shine ka kasance cikin yin tagociya a adduaarka, wato idan kaza alkhairi ne a gare ni Allah ka bani, idan ba alkhairi bane Allah ka musanya min da mafi alkhairin sa. Not Allah ka bani kaza anyhow.
Yarimah ya dauki babyn yana kallowith affection sannan ya lakuce masa hanci. kai Chiroma shine ka wahalar min da mata ko? Kasa har ta fara bada wasiyyar hana ni aure idan ta zarce? Daidai lokacin da Askirama da Fulani da Ya Gumsu suka shigo fuskar su fal fara don tuni albishir din isowar Chiroma ya je musu.
Nan nurse Aisha take basu labarin wasiyyar Saade ga Fulani da Yareema. Suka ce me zasu yi ba dariya ba. Fulani ta ce yanzu ma bata baci ba a bani kujerar makkah na in je in yi azumi acan ni da takwarata, ban daukar takwarar Ya Gumsu tunda bata zuwa kwana waje na. Askirama yace to kai an ce kada ka kara aure ka jira sai an hade a aljannah, nikuwa da har na shirya maka kwarkwarori uku tunda Saadatu jego zata fara. Yaa Gumsu tace lala-lala Askirama in wasa nea bari, kaima ka haramtawa kan ka naka, a na me shi zaa takura shi a kai Alanguburo? Cewa yayi bai iya jiran matar sa ta gama biki? Kunya ta lullube Saade amma ta ji dadin yadda Ya Gumsu ta dage ta hana a baiwa Yarima concubones, ta san da watakila shikenan ta bar shakar numfashi daidai a duniyar subhanah.yammata hudu rus! Ga Yarima Sageer? Ai karshen ta a barrow zaa kwasheta zuwa asibitin masu dan karamin tabin hankali.
Shima Askirama jin baki ne irin nasa, don ya san ba abinda Yarima ya ki jini irin ace ya kara aure. Da an fadi hakan zai jawo ayar Allah ya ce sai zaku iya adalci, shikuma bai iya adalcin tsakanin Saadatu da wata diya mace, da muguwar rawa gwamma kin tashi. Shiyasa Askirama yake so ya dauki kwarkwarori duk adadin da yake so, amma wani zubin har zuciyar sa yana ganin Yarima ya hada da concubines zai kara fiddo da kimar sarautar sa.
A yanzu dai Yareema Sageer ya ce baya da bukata bai sani ba dai ko can gaba in ya fara tsufa.
Baby ya ci sunan Askirama YUSUF. Ana kiran sa Chiroma. Tsakanin Mai Askira daYa Gumsu ban san wa ya fi son jikokin nan ba. Ya Gumsu kullum ta dubi yaran sai ta kara nadama ta yi dana sanin ja da hukuncin Ubangiji, lalle ne ko rabon wadannan yaya biyar ya isa ya kayar da ita kwanan ta bai kare ba.
A halin yanzu ta fi kowa alfahari da auren Yarima da Saade ta kuma yardada abinda Askirama ke fadi cewa Saadatu diyar Bilkisu,rufin asiri ce, suttura ce ga dan su Yareema Sageer Yusuf Askira.

Masha Allahu laquwwata illa billah.

Nan na kawo karshen littafin MASARAUTARMU 3&4. Kurakuran dake ciki ku tayani rokon Allah ya yafe mini. Abin alfanun da ke ciki Allah ya hada mu a ladan nida ku bakidaya.
Sumayyah Abdulkadir
18/11|2021.

Ina mukualbishirda sabonlittafinamaisuna NA HUCE!Wanda zaizo a matsayingoronsabuwarshekarainsha Allah.

TUNA SUNAN SA;
NAHUCHE (DagaFushina)
Chapter 18 · 0% Book details